Limamai da Fastoci Za Su Dara a Bauchi, Gwamna Bala Ya Sanya Su a Sabon Tsari

Limamai da Fastoci Za Su Dara a Bauchi, Gwamna Bala Ya Sanya Su a Sabon Tsari

  • Gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed ta gudanar da taro na majalisar tattalin arziki a ranar, Juma'a 30 ga watan Janairun 2026
  • A yayin taron an cimma matsaya kan fito da tsarin ba da kudaden alawus-alawus ga limamai na fastoci a fadin jihar
  • Hakazalika, gwamnatin ta sanar da adadin ma'aikatan bogin da ta zakulo wadanda ke karba albashi duk wata ba tare da yin aikin fari balle baki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - Majalisar tattalin arzikin Bauchi ta amince da biyan alawus na wata-wata ga limamai da fastoci a fadin jihar.

Gwamna Bala Mohammed ne ya jagoranci taron majalisar tattalin arzikin, wanda manyan masu ruwa da tsaki daga bangarorin kudi da samun kudaden shiga na jihar suka halarta.

Fastoci da limamai za su samu alawus a Bauchi
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce an gudanar da taron ne a ranar Juma'a, 30 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Kotu ta jikawa PDP bangaren Turaki aiki, ta ba jam'iyya umarni

Da yake yi wa manema labarai bayani kan sakamakon taron, shugaban ma’aikatan jihar, Barrista Mohammed Sani Umar, ya bayyana cewa majalisar ta tattauna dalla-dalla kan batutuwan.

Limamai da fastoci za su samu alawus

Ya bayyana cewa gwamnan ya amince da biyan alawus na wata-wata ga limaman masallatan Juma’a daban-daban a fadin jihar, haka kuma ga fastoci na darikun Kirista iri-iri.

A cewarsa, biyan wadannan alawus-alawus ga limamai da fastoci zai kasance ba tare da la’akari da bambanci akida ba.

“Mataki na karshe shi ne a tantance tasirin shirin kan tattalin arziki da na kudi domin aiwatar da wannan manufa yadda ya kamata."

- Barista Mohammed Sani Umar

Ya kuma bayyana cewa majalisar ta tattauna batun fara biyan albashi ga sababbin sarakuna da hakimai da aka nada a fadin jihar, inda ya ce gwamnati ta riga ta tanadi isassun kudade domin tabbatar da dorewar hakan.

An gano ma'aikatan bogi a Bauchi

A nasa bangaren, babban Mai ba gwamna shawara kan tattalin arziki, Alhaji Yahuza Adamu Haruna, ya ce majalisar ta sake duba tsarin biyan albashi na jihar, jaridar Vanguard ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

Jita jita ta kare: Babban alkalin Katsina ya tsage gaskiya kan batun sakin 'yan bindiga 70

Gwamnatin Bauchi za ta ba limamai da fastoci alawus
Taswirar jihar Bauchi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi aiki tare da kamfanin Onyx Investment Advisory Limited, domin ganowa tare da kawar da ma’aikatan bogi daga jerin masu karbar albashi.

Alhaji Yahuza Adamu ya ce wannan aiki ya kai ga gano ma’aikatan bogi fiye da 3,000, lamarin da ya sa jihar ta rarar sama da Naira biliyan 4.16.

Kungiyar CAN ta kare Gwamna Bala

A wani labarin kuma, kun ji cewa Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Bauchi, ta fito ta kare Gwamna Bala Mohammed kan zargin daukar nauyin ta'addanci.

Kungiyar karkashin jagorancin shugabanta, Rabaran Dr. Abraham Damina Dimeus ta bayyana cewa, duba da irin zaman lafiyar da ake morewa a jihar, babu wani abu da ke alakanta Gwamna Bala da daukar nauyin ta’addanci.

CAN ta jaddada cewa mazauna Bauchi sun shaida irin kokarin da gwamnan ke yi wajen magance matsalolin tsaro, inda mutane ke rayuwa cikin zaman lafiya ba tare da bambancin addini ko kabila ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng