Wata Sabuwa: Kotu Ta Jikawa PDP Bangaren Turaki Aiki, Ta Ba da Umarni
- Rikicin shugabanci na PDP ya sanya jam'iyyar ta rabe gida biyu inda ake ta gwabzawa a kotuna daban-daban
- Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Ibadan ta soke babban taron jam'iyyar da aka gudanar a jihar Oyo
- Kotun ta kuma ba da umarni ga shugabannin da aka zaba yayin babban taron na watan Nuwamban shekarar 2026 da ta gabata
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Oyo - Wata babbar kotun tarayya da ke Ibadan, jihar Oyo, ta soke babban taron PDP na kasa da aka gudanar a Ibadan a ranar 15 ga Nuwamba, 2025.
A yayin babban taron, an zabi Kabiru Tanimu Turaki, a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

Source: Instagram
Jaridar Daily Trust ta ce kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Juma'a, 30 ga watan Janairun 2026.
PDP ta gudanar da babban taro
Taron, wanda ya samu halartar wakilai daga jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuna ya kara zurfafa rikicin da ke addabar jam’iyyar adawa.
Wasu ‘ya’yan jam'iyyar da ke adawa da taron sun garzaya kotu domin hana gudanar da shi, amma bangaren da ke goyon bayan Gwamna Seyi Makinde ya kuduri aniyar ci gaba da taron.
Wane hukunci kotun ta yanke?
A hukuncin da alkalin kotun ya yanke, Mai shari’a Uche Agomoh ya hana dukkan wadanda aka zaba a taron na jam’iyyar PDP bayyana kansu a matsayin shugabannin PDP.
Alkalin ya ce an shirya taron na watan Nuwamba ne bisa kin bin umarnin kotu, lamarin da ya bayyana a matsayin raina dokar kotu karara.
Ya jaddada cewa PDP ba za ta iya saba wa umarnin kotu ba, sannan kuma ta dawo kotu tana neman amincewar shari’a kan matakan da ta dauka a kan wadannan umarnin.
Kotu ta fadi kwamitin NWC na PDP
Kotun ta kuma yanke hukunci cewa kwamitin rikon karkashin jagorancin Abdulrahman tare da Sanata Samuel Anyanwu su ne kadai kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) da kotu ta amince da su, har sai an gudanar da sahihin babban taro na kasa.
Bangaren Anyanwu dai na samun goyon bayan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Source: Facebook
PDP ta yi martani
A martanin da PDP ta yi kan hukuncin a shafin X, ta an ce an riga an bai wa lauyoyi umarni su gaggauta daukaka kara, tare da daukar duk wasu matakan shari’a da suka dace domin kare matsayin jam'iyyar a kan lamarin.
Bangaren PDP karkashin jagorancin Kabiru Turaki da aka samar a taron Ibadan ya ce har yanzu yana nan daram a fannin doka, kuma bai girgiza ba, yayin da suke jiran hukuncin karshe daga kotunan daukaka kara.
Saboda haka, sun bukaci ‘ya’yan jam’iyyar da su ci gaba da jajircewa da tsayawa kan akidarsu, suna mai cewa babu wani abin firgici ko tashin hankali.
Tsohon sanatan PDP ya koma APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Simon Mwadkwon, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Sanata Simon Mwadkwon ya lashe zaɓen Sanatan Plateau ta Arewa a shekarar 2023 a karkashin jam’iyyar PDP.
Mwadkwon ya ce ya yanke shawarar sauya shekar ne bayan shawarwari masu zurfi da ya yi da al’ummar mazabarsa.
Asali: Legit.ng


