Sojoji Sun Kai Hari Kasuwa a Yobe bayan Samun Bayanai kan Boko Haram

Sojoji Sun Kai Hari Kasuwa a Yobe bayan Samun Bayanai kan Boko Haram

  • Rundunar Sama ta 'Operation' Hadin Kai ta hallaka wasu ’yan ta’adda bayan harin kasuwar Baimari a Jihar Yobe
  • An kai farmakin ne bisa sahihan bayanan sirri da sa ido na sama da ya biyo sawun maharan har bayan sun watse
  • Sojoji sun ce an aiwatar da aikin cikin ƙwarewa domin rage asarar fararen hula da lalacewar dukiya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Yobe – Dakarun rundunar sojin Najeriya sun yi nasarar kawar da wasu ’yan ta’adda bayan wani harin da aka kai kasuwar Baimari da ke Ƙaramar Hukumar Bursari a Jihar Yobe.

An kai harin ne bayan an samu wasu sahihan bayanan sirri kai-tsaye tare da sa ido ta sama bayan an dade ana bibiyar yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Ma'auratan da suka yi garkuwa da kansu sun karbi fansa N10m

Sojojin Najeriya sun farmaki yan Boko Haram
Daga sojin Najeriya, jirgin sojojin Najeriya Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa majiyoyi sun sun ce an gano wasu da ake zargin yan Boko Haram ne a ranar 29 ga Janairu da 7.00 na dare sun kutsa ksauwar.

Yadda aka gano yan Boko Haram a Yobe

Rahotanni an hango mutanen da aka kyautata zargin yan Boko Haram ne sun kutsa kasuwar Baimari a cikin motoci biyu.

Da shigar kasuwar, sau suka bude wuta a kan bayin Allah. Wannan lamari ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da tsoro.

An kai wa yan Boko Haram hari bayan an jima ana sa ido
Taswirar jihar Yobe, inda aka kashe yan Boko Haram Hoto: Legit
Source: Original

A cewar majiyoyin, maharan sun kashe fararen hula biyu, wato Isah Mohammed, ma’aikacin kamfanin Aminco Global, da Umaru Dahiru, ɗan ƙauyen Baimari.

Bugu da ƙari, sun sace motar Hilux ta kamfani guda, suka ƙona wata motar, sannan suka kwashe kayan abinci da dama daga kasuwar kafin su tsere.

Sojoji sun yi wa Boko Haram martani

Majiyoyin sun bayyana cewa nan take Sashen Rundunar Sama ya ƙaddamar da ayyukan bincike, sa ido da leƙen asiri, inda aka tura jirgin sama domin bin diddigin ’yan ta’addan.

Kara karanta wannan

'Dan bindiga da ya hana Turji, yaransa sakewa ya mutu, an kashe shi wurin sulhu

Majiyoyi sun ce da 11.41 na dare, jirgin ya gano motoci uku, inda suke wasan buya da dakaru a hanya har aka samu daya daga cikin motocin ta tsaya da asubahin ranar 30 ga Janairu.

Bayan tabbatar da kasancewar ’yan ta’adda a wurin, rundunar ta kai farmakin da ya dace da ƙarfe 1.30 na dare.

Rahoton ya nuna cewa ginin da aka kai wa hari ya lalace gaba ɗaya, kuma an hallaka ’yan ta’addan da ke ciki.

Majiyoyin sun ƙara da cewa an sanya dakarun ƙasa da wasu jiragen sama cikin shirin ko-ta-kwana domin tabbatar da tsaron rayuka, bayan an yi amfani da kwarewa wajen kare rayukan fararen fula.

'Yan Boko Haram sun kashe sojoji

A baya, mun wallafa cewa ’yan ta’addan Boko Haram sun kai wani mummunan harin kwanton ɓauna kan dakarun sojojin Najeriya a Jihar Borno, an kashe wasu daga cikinsu.

Rahotanni sun bayyana cewa harin ya auku ne a ranar Litinin, 26 ga watan Janairun 2026, a lokacin da sojoji ke gudanar da sintiri a yankin, inda wasu da dama suka bace.

Majiyoyin tsaro sun ce maharan sun kai farmakin ne kan jerin sojoji fiye da 30 da ke tafiya a ƙasa a wajen garin Damask, wani yanki da ke kusa da iyakar Jamhuriyar Nijar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng