Shaidan EFCC: Yadda Emefiele Ya Hada Takardun Bogi, Ya Ciri $6.23m daga CBN

Shaidan EFCC: Yadda Emefiele Ya Hada Takardun Bogi, Ya Ciri $6.23m daga CBN

  • Shaida na 11 da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ke gabatarwa a kan shari'a da tsohon Gwamnan EFCC ya fito da jawaban boye
  • Ya bayyana yadda aka ce an fitar da Dala miliyan 6.23 daga babban bankin kasa na CBN da takardun bogi a zamanin Emefiele
  • Shaidan ya ce an cire kudin ne a reshen Garki na CBN da ke domin ayyukan masu sa ido kan zabe da harkokin gudanar da zaben

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shaida ta 11 a bangaren EFCC, Bashirudden Muhammed Maishanu, ya bayyana wa Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) kan shari'ar Godswill Emefiele.

A ci gaba da shari'a da ake yi da tsohon Gwamnan bankin kasar nan, shaidan ya ce an cire Dala miliyan 6.23 daga bankin CBN.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano: Binciken Ganduje na nan duk da Abba ya shigo jam'iyyar APC

EFCC ta gabatar da shaida na 11 a gaban kotu
Ofishin hukumar EFCC, Godswill Emefiele Hoto: @cenbank, @OfficialEFCC
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta wallafa Bashirudden Muhammed Maishanu ya ce an yi amfani da takardun bogi a lokacin mulkin tsohon gwamnan bankin, Godwin Emefiele.

An gabatar da shaida a kan Emefiele

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Maishanu, mataimakin darakta a CBN, ya bada shaidarsa gaban Mai shari’a Hamza Muazu.

A yayin da ya ke mayar da magana, ya ce an cire kudin ne a ranar 8 ga Fabrairu, 2023, daga reshen CBN na Garki,.

Bashirudden Muhammed Maishanu ya ce an ciri kudin da sunan cewa za a yi amfani da su wajen daukar nauyin masu sa ido kan zabe da harkokin dabaru.

Lauyan gwamnati kuma Daraktan Gabatar da Kara, Rotimi Oyedepo (SAN), ya tambayi Maishanu kan yadda ya san Emefiele.

Shaidan ya ce ya hadu da Emefiele a 2015 ta hannun wani Eric, wanda ya bayyana a matsayin mataimakin Emefiele a wancan lokaci.

Kara karanta wannan

Gwamnoni, shugabannin jam'iyya sun zauna, an tsayar da lokacin babban taron APC

Yadda shaidan EFCC ya san Emefiele

Ya ce a farkon Janairu 2023, wani Alhaji Ahmed ya tuntube shi, yana ikirarin cewa yana aiki da wata kwamitin musamman a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Bashirudden Muhammed Maishanu ya ce Ahmed ya kuma ce suna shirin karbar wani kudi daga CBN bisa amincewar shugaban kasa.

Maishanu ya ce ya nemi shaidar Ahmed tare da bukatar ya kira Eric domin tabbatar da ikirarin.

Bayan Eric ya tabbatar da saninsa, Ahmed ya ce da zarar an samu amincewar shugaban kasa, za a bi ka’idojin CBN wajen biyan kudin.

Bayan kusan mako guda, Ahmed ya dawo da abin da ya kira amincewar shugaban kasa, inda ya ce za su nemi yardar Emefiele domin fitar da kudin a tsabar kudi.

Ana zargin Emefiele ya cire makudan kudi daga asusun CBN
Tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya, Godswill Emefiele Hoto: @OfficialEFCC
Source: Facebook

Ya kuma bukaci taimakon Maishanu ko ya ba da shawarar wanda zai raka su wajen karbar kudin.

Shaidan ya ce ya ki shiga, amma ya gabatar da wani abokinsa. A ranar 8 ga Fabrairu, 2023, abokin da direbansa suka cire Dala miliyan 6.23 daga reshen Garki.

Kara karanta wannan

Bayan shigar Gwamna Abba APC, sakataren ADC ya ja kunnen jam'iyyar kan zaben 2027

Da ya ke amsa tambayoyin lauyan kare kai, Mathew Burkar (SAN), Maishanu ya ce ya tabbata amincewar bogiya ce.

Ya amince cewa ya karbi wani bangare daga kudin da aka bari, amma ya ce ba nasa ba ne, kuma bai san tun farko cewa harkar bogiya ce ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng