Yadda Musulmi ’Yan Kabilar Igbo Ke Fama da Matsaloli a Yankinsu, an Kawo Mafita

Yadda Musulmi ’Yan Kabilar Igbo Ke Fama da Matsaloli a Yankinsu, an Kawo Mafita

  • Ƙungiyar mata Musulmi ta yi gargaɗi kan barazana da tsangwama da Musulman Igbo ke fuskanta musamman mata masu sanya hijabi
  • Ƙungiyoyin sun ce Musulman Igbo na fuskantar wariya, kalaman ƙiyayya da barazanar tashin hankali saboda haɗuwar ƙabila da addini
  • An kuma bayyana halin ƙuncin da mata Musulmi masu nakasa ke ciki, inda aka buƙaci manufofi da wurare masu sauƙin shiga gare su

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos – Matsalolin da ke addabar mata Musulmi masu nakasa da kuma halin da Musulman Igbo ke ciki a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya sun dauki hankalin jama’a.

Kungiyar mata Musulmi ta yi gargadi game da tsangwama musamman ga mata Musulmi gabanin bikin Ranar Hijabi ta Duniya ta 2026.

Yadda Musulmi ke fusknatar tsangwama a yankin Igbo
Mata Musulmi yayin taro da kare martabarsu a Lagos. Hoto: @fomwan_lagos.
Source: Facebook

FOMWAN ta fusata kan tsangwamar Musulmi

An gudanar da taron manema labaran ne a masallacin Alausa da ke Ikeja, domin tunawa da Ranar Hijabi ta Duniya wadda ake gudanarwa duk shekara a ranar 1 ga Fabrairun 2026, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Solar: Gwamnati ta ware N7bn don samar da wuta ta hasken rana a fadar shugaban kasa

Da take jawabi a madadin Ƙungiyar Ƙasashen Mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN), Hajiya Kudrah Ogunmuyiwa ta nuna damuwa kan tsangwama da raunin da Musulman Igbo ke fuskanta, musamman mata masu sanya hijabi.

Ta ce haɗuwar ƙabila da addini ya jefa mata Musulmi ‘yan Igbo cikin keɓancewa da ware kansu daga al’umma da kuma barazanar tashin hankali.

Hajiya Ogunmuyiwa ta bayyana cewa duk da cewa addinin Musulunci ya dade yana gudana a ƙasar Igbo, Musulman yankin na ci gaba da kasancewa marasa karfi inda suke fuskantar matsi a al’adu da ƙiyayya saboda bayyanar da addininsu a fili.

Ta bayyana wasu kalamai na ƙiyayya da zargin kira ga tashin hankali da wani da aka ambata da suna Mazi Kanayo ya yi, tana mai cewa hakan abin firgici ne kuma barazana ce ga haɗin kan ƙasa.

Ta ƙara da cewa sanya hijabi ba ya rage ƙabilanci ko zama ‘yan ƙasa, tana mai cewa mace Musulma ‘yar Igbo mai hijabi cikakkiyar ‘yar Igbo ce kuma cikakkiyar Musulma.

An gargadi hukumomi kan sakaci da kyamar Musulmi yan kabilar Igbo
Taswirar jihar Lagos da aka gudanar da taron wayar da kai game da tsangwamar Musulmi. Hoto: Legit.
Source: Original

Abin doka ta ce kan yancin addini

Hajiya Ogunmuyiwa ta yi Allah-wadai da kalaman ƙiyayya ta kowanne fanni, tana mai ambaton sashe na 24(1)(c) na Kundin Tsarin Mulkin 1999, wanda ya wajabta girmama mutunci da haƙƙin sauran ‘yan ƙasa.

Kara karanta wannan

Musulmai za su ki yarda da zaben Najeriya sai an sauke shugaban INEC

Ta yi gargaɗin cewa mata Musulmi a Kudu maso Gabas na fuskantar cin mutunci, ƙyamar al’umma, killacewa ta tattalin arziki, tsoratarwa da kuma hana su samun wasu muhimman ayyuka, saboda addininsu.

Ta ce:

“Wannan lamari ba zai taɓa zama abin amincewa ba a ƙasar da ke bin tsarin dimokuraɗiyya.”

FOMWAN ta buƙaci hukumomin tsaro su bincika tare da hukunta duk masu kalaman ƙiyayya da tayar da hankali, ta kuma yi kira ga shugabannin gargajiya da na al’umma a Kudu maso Gabas da su fito fili su yi Allah-wadai da rashin juriya ga addini.

Ƙungiyar ta kuma jawo hankali kan halin da mata Musulmi masu nakasa ke ciki, tana mai cewa matsalolinsu na daga cikin abubuwan da ake nuna wa ƙyama kuma ke bukatar kulawa cikin gaggawa, cewar TheCable.

Masoya sun Musulunta daf da bikin aurensu

A baya, kun ji cewa Aishat Ugochi Obi da angonta Nurudeen (Nicholas) Ikeocha za su yi aure kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a jihar Imo.

Masoyan junan da za su yi auren sunnah kamar yadda suka tabbatar bayan sun musulunta wanda ya zama abin kallo a yankin Kudu mso Gabas.

An gudanar da bikin auren nasu bisa tsarin Musulunci a ranar 10 ga watan Afirilun 2020 a jihar Imo wanda ya dauki hankulan mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.