Tinubu Ya Raba Miliyoyin Kudi ga ’Yan Kasa, Za a Kara Taimakon Mutane Miliyan 16

Tinubu Ya Raba Miliyoyin Kudi ga ’Yan Kasa, Za a Kara Taimakon Mutane Miliyan 16

  • Gwamnatin Tarayya ta ce ta raba tallafin kuɗi ga 'yan Najeriya sama da miliyan 34 domin rage radadin matsin tattalin arziki
  • Ministan Jinƙai, Dr Bernard Doro, ya bayyana cewa ana sa ran kai tallafin zuwa miliyan 50 kafin ƙarshen shekarar 2026
  • An kafa majalisar Jinƙai da Rage Talauci ta Ƙasa domin inganta haɗin gwiwa tsakanin tarayya, jihohi da sauran masu ruwa da tsaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Calabar, Cross River – Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta riga ta bai wa sama da yan Najeriya miliyan 34 ga marasa karfi tallafin kudi a kasar.

Gwamnatin Najeriya ta ce ta yi haka nea ƙoƙarinta na rage matsin tattalin arziki da kuma yaki da talauci a fadin ƙasar nan.

Tinubu ya rabawa miliyoyin yan Najeriya talllafi
Shugaba Bola Tinubu da Ministan jin kai a Najeriya, Dr. Bernard Doro. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Yadda aka shirya tallafa wa 'yan Najeriya

Ministan Jinƙai da Rage Talauci, Dr Bernard Mohammed Doro, ne ya bayyana hakan yayin taron farko na Majalisar Jinƙai da Rage Talauci ta Ƙasa, cewar Punch.

Kara karanta wannan

An zargi Faransa, kasashe 2 da luguden wuta a Nijar, Rasha ta kai dauki

A cewarsa, wannan shiri na tallafi na nuna ƙudirin Gwamnatin Tarayya na fitar da miliyoyin ‘yan Najeriya daga kangin talauci ta hanyar shirye-shiryen jinƙai da aka tsara bisa bayanai, tare da haɗin gwiwa da adalci.

Ministan ya ƙara da cewa gwamnati na da burin kai wa mutane miliyan 50 tallafin kudi kafin ƙarshen shekarar nan, yana mai jaddada cewa kare walwalar jama’a na daga cikin ginshiƙan dabarun rage talauci na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Dr Doro ya ce:

“Gwamnatin Tarayya ta riga ta raba tallafin kuɗi ga sama da yan Najeriya miliyan 34, kuma muna aiki tukuru domin kaiwa miliyan 50 kafin ƙarshen shekara.”

Ya bayyana cewa an kafa Majalisar Jinƙai da Rage Talauci ta Ƙasa ne domin ƙarfafa haɗin kai da ingancin ayyukan jinƙai, yana mai cewa kokari dabam-dabam ba tare da tsari ba ba zai haifar da ci gaba mai ɗorewa ba.

Gwamnatin Tinubu ta bayyana shirin tallafa wa yan Najeriya miliyan 50
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

A nasa jawabin, karamin ministan jinƙai, Dr Tanko Sununu, ya ce sauye-sauyen da ke faruwa a duniya sun sauya yadda ake gudanar da ayyukan jinƙai, lamarin da ya sanya haɗin kai da kirkire-kirkire suka zama wajibi.

Kara karanta wannan

Solar: Gwamnati ta ware N7bn don samar da wuta ta hasken rana a fadar shugaban kasa

Martanin gwamnan Cross River ga gwamnatin Tinubu

Gwamnan Jihar Cross River, Bassey Otu, wanda mataimakinsa Peter Odey ya wakilta, ya yabawa Gwamnatin Tarayya bisa zaɓar Calabar a matsayin wajen gudanar da taron farko.

Gwamnatin Otu ta yi alkawarin ci gaba da ba da goyon baya ga duk wani shiri da ke da nufin rage talauci, musamman ga al’ummomin kan iyaka, cewar Leadership.

Gwamnatin Tinubu za ta ba manoma tallafi

A wani labarin, an ji Gwamnatin tarayya ta ce za ta ɗauki matakan gaggawa domin tallafa wa manoma ganin farashin wasu kayan abinci ya faɗi warwas a kasuwa.

Ministan kuɗi da tattalin arziki, Wale Edun ya ce saukar farashin abinci ya kawo sauƙi ga masu saye, amma yana iya hana manoma ci gaba da noma.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa 2026 za ta mayar da hankali kan tsaron abinci, samar da wutar lantarki, hanyoyi da kariya ga masu karamin karfi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.