Jarumin Nollywood Ya Shiga Hannu a kan Zargin Shirin Juyin Mulki
- An kama wani fitaccen jarumi kuma daraktan Nollywood, Stanley Amandi, bisa zargin hannu a shirin yin juyin mulki a Najeriya
- Rahotanni sun nuna cewa an ɗauke shi aiki a matsayin mai yaɗa farfaganda domin tallata shirin kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
- Rundunar soji ta tabbatar da kammala bincike tare da shirin gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotunan soji da na farar hula
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT Abuja – Jarumi kuma mai shirya fina-finan Nollywood, Stanley Amandi, ya faɗa hannun jami’an tsaro tare da wasu manyan jami’an soji bisa zargin shirya juyin mulki.
Ana zargin Stanley Amadi na da aikin da aka ɗora masa wajen shirin kifar da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a watannin baya.

Kara karanta wannan
An 'gano' wani shiri da masu juyin mulki suka yi domin hana Buhari ba Tinubu mulki

Source: Facebook
A labarin da ya kebanta da Premium Times, Amadi yana cikin wadanda ake zargi da hannunsu a yunkurin hambarar da gwamnatin farar hula a Najeriya.
An ji cewa darektan ya taɓa zama shugaba na reshen Kungiyar Jaruman Najeriya a Jihar Enugu.
Juyin mulki: Yadda aka kama jarumin Nollywood
Rahotannin sun tabbatar da cewa an kama Stanley Amadi a watan Satumba na shekarar 2025. Wannan ne karon farko da aka bayyana rawar da ake zargin ya taka a shirin kifar da gwamnati.
Majiyoyi sun shaida wa jaridar cewa waɗanda ake zargin sun ɗauki Amandi aiki ne domin ya riƙa yaɗa farfaganda, da nufin tallata shirin da ya haɗa da kashe manyan jami’an gwamnati a shekarar 2025.
A matsayinsa na farar hula kuma mai bada umarni a fim, an nemi a yi amfani da shi wajen yada furofagandar da za ta taimaka a kifar da gwamnati.
Rahotanni sun nuna cewa an ware manyan shugabannin ƙasa a matsayin waɗanda za a kai wa hari a shirin juyin mulkin da bai kai ga nasara ba.

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: An fallasa yadda aka shirya kashe Tinubu, Shettima da wasu mutum 2
An so kashe Tinubu a juyin mulkin
Majiyoyin gwamnati da aka sanar da su batun a wancan lokaci sun ce masu shirin sun yi niyyar kashe Shugaba Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima.

Source: Twitter
Sauran wadanda aka so a kashe sun hada da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, da sauran wasu jami’ai.
Ranar Litinin, Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa ta tabbatar da cewa an gano shirin kifar da gwamnatin Tinubu kuma an daƙile shirin.
A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce an kammala bincike kuma an miƙa rahoton ga manyan hukumomi da suka dace bisa ƙa’idojin da ake da su.
Ana binciken wadanda suka shirya juyin mulki
Sanarwar ta ƙara da cewa an yi cikakken bincike inda aka bi duk hanyoyin da doka ta tanada domin tantance dukkanin abubuwan da suka shafi jami’an da abin ya shafa.
Rundunar ta bayyana cewa sakamakon binciken ya nuna akwai wasu jami’an soji da ake zargi da shirin kifar da gwamnati.
Ta kara da jaddada cewa irin wannan hali “ya saɓa wa ɗabi’a, ƙima da ƙa’idodin ƙwarewa da ake buƙata daga sojojin Najeriya.
An kammala bincike a kan juyin mulki
A baya, mun wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa rundunar sojin Najeriya ta mika wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu cikakken rahoto kan shirin juyin mulki.
Binciken ya shafi abin da hukumomin tsaro suka bayyana a matsayin rashin ladabi, karya ka’idojin aiki da kuma aikata abubuwan da suka sabawa dokokin soja.
Majiyoyi daga bangaren tsaro da kuma fadar shugaban kasa sun tabbatar da cewa an kammala rahoton ne bayan tsawon lokaci ana gudanar da bincike a asirce.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
