Daga Sauya Sheƙar Abba, Tinubu Ya Amince da Aikin Naira Tiriliyan 1 a Kano

Daga Sauya Sheƙar Abba, Tinubu Ya Amince da Aikin Naira Tiriliyan 1 a Kano

  • A yammacin Alhamis aka ji Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta amince da gina jirgin ƙasa na N1tr a ƙwaryar birnin jihar Kano
  • Gwamna Abba Yusuf ya ce jirgin zai sauƙaƙa zirga-zirga kuma ya ƙara ci gaban tattalin arzikin jihar a sanadiyyar gwamnatin tarayya
  • Wannan abin arziki ya faru ne kwanaki kadan bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya canja sheka daga NNPP jam'iyya zuwa APC

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta amince da gina jirgin ƙasa na zamani, wanda zai ci kusan N1tr wani muhimmin mataki na sauya tsarin sufuri a birnin Kano.

Wannan shirin zai taimaka wajen inganta harkokin kasuwanci, rage cunkoson ababen hawa, da kuma sauƙaƙa zirga-zirga a duk faɗin birnin.

Kara karanta wannan

Jarumin Nollywood ya shiga hannu a kan zargin shirin juyin mulki

Gwamnatin tarayya za ta gina tashar jirgin ƙasa a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf yana yi wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu jawabi Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Wannan bayani ya fito a cikin wata sanarwa da kakakin gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya a shafinsa na Facebook.

Gwamnan Kano ya magantu kan aiki jirgin ƙasa

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana wannan babban aiki na ci gaban tawagar Kano da ta halarci gasar karatun Alqur’ani ta kasa ta shekarar 2025 da aka gudanar a jihar Borno.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa samar da jirgin ƙasan zai samar da tsarin sufuri na zamani, mai sauri, mai rahusa, kuma mai inganci wanda zai haɗa manyan unguwanni a cikin birnin.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce za a ci moriyar jirgin idan ya iso
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Wannan zai sauƙaƙa wa tafiye-tafiye ga mazauna birnin, ya ƙara tallata kasuwanci, da kuma jawo hannun jari jihar Kano.

Ya bayyana aikin a matsayin wani muhimmin mataki da zai inganta rayuwar jama’a sosai, tare da maida Kano matsayin babban cibiyar sufuri a Arewacin Najeriya.

Amfanin jirgin ga al’ummar Kano - Abba

Kara karanta wannan

Kano: NNPP ta dura a kan masu neman mataimakin Gwamna ya yi murabus

Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa jirgin ƙasan zai samar da tsarin sufuri na zamani, mai sauri, mai rahusa, kuma mai inganci wanda zai haɗa manyan unguwanni a cikin birnin.

Wannan zai sauƙaƙa motsi ga mazauna birnin, ya ƙara tallata kasuwanci, da kuma jawo hannun jari da za su shigo jihar saboda sauƙi rayuwa mazauna yankinsa a Amurka.

Gwamna ya bayyana aikin a matsayin wani muhimmin mataki da zai inganta rayuwar jama’a sosai, tare da maida Kano matsayin babban cibiyar sufuri a Arewacin Najeriya.

Ya bayyana cewa wannan zai kuma kara haɓaka tattalin arzikin jama'a da tabbatar da an samu ingantaccen tsaro a yayin tafiye-tafiye.

Tsagin NNPP ya kare Gwamna Abba

A baya, kun ji cewa tsagin jam’iyyar NNPP ya yi martani kan sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga cikinta zuwa jam’iyyar APC mai mulki a a matakin kasa

A cikin sanarwar da tsagin jam’iyyar ya fitar, an ce Gwamna Abba Kabir Yusuf bai bar NNPP don son ransa ba, illa saboda dama da matsin lamba da mulkin mallaka daga Kwankwaso m

Tsagin ya zargi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da yin wasu abubuwa da suka ƙara jefa jam’iyyar cikin rikici, wanda ya sa gwamnan ya ga dacewar fita daga ciki domin a samu sauki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng