Asiri Ya Tonu: An Fallasa yadda Aka Shirya Kashe Tinubu, Shettima da Wasu Mutum 2
Abuja - Wani gagarumin binciken sirri wanda dakarun sojojin ƙasa da hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) suka gudanar, ya bankaɗo yadda aka shirya yin juyin mulki a Najeriya.
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Binciken ya nuna cewa an shirya yadda za a kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da hallaka shugaban kasa da wasu manyan jami’an siyasar Najeriya.

Source: Twitter
Yadda asirin juyin mulki ya fara tonuwa
Rahoto na musamman da Premium Times ta fitar, ya nuna cewa wannan yunkuri, wanda ya girgiza fadar shugaban ƙasa, ya fara fitowa fili ne a ƙarshen watan Satumban 2025.
Amma rahoton ya nuna cewa yanzu haka an tabbatar da shirin gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotun sojoji.
Asirin wannan shiri ya fara tonuwa ne lokacin da wani jami'in soja dake da masaniya kan shirin ya tuntuɓi tsohon babban hafsan sojin ƙasa, Janar Olufemi Oluyede.

Kara karanta wannan
An 'gano' wani shiri da masu juyin mulki suka yi domin hana Buhari ba Tinubu mulki
Jami'in ya bayyana cewa ya ga ya dace ya tona asirin ne domin tsoron kada a haɗa da shi a matsayin wanda ya san ana shirin cin amanar ƙasa amma ya yi shiru.
A lokaci guda kuma, hukumar DSS ƙarƙashin jagorancin Oluwatosin Ajayi, ta samu wasu bayanan sirrin dake nuna cewa wasu jami'an sojoji na ƙoƙarin ruguza dimokuradiyyar ƙasar.
Bayan samun waɗannan rahotanni daga ɓangarori biyu, shugabannin tsaron suka haɗa gwiwa wajen ƙaddamar da samame na sirri a sassa daban-daban na ƙasar.
A ranar 30 ga Satumba, 2025, yayin da Shugaba Tinubu yake ziyarar aiki a Jihar Imo ba tare da sanin abin da ke faruwa ba, jami'an tsaro suka kama manyan masu shirya juyin mulkin.
Shirin kashe Tinubu, Shettima, Akpabio
Rahoton jaridar ya kuma bayyana cewa masu juyin mulkin ba kawai son ƙwace mulki suke yi ba, har ma da kashe manyan shugabannin ƙasar a lokaci guda.
Wadanda aka yi wa jan maki domin a kashe su sun haɗa da Shugaba Tinubu, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, da kuma shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas.
Masu tada ƙayar bayan sun yi amfani da wasu mutane a cikin fadar shugaban ƙasa waɗanda suke sanya ido kan duk wani motsi na waɗannan shugabannin.
Shirin shi ne a kashe su duka a ranar da dukkaninsu suke cikin ƙasar, sannan a kama manyan hafsoshin tsaro a tsare su domin kafa gwamnatin soja.
Garambawul a rundunar tsaron Najeriya
Bayan da Shugaba Tinubu ya samu labarin wannan danyen shiri, ya soke faretin ranar samun yancin kai na 1 ga Oktoba saboda fargaba, kamar yadda Legit Hausa ta rahoto.
Haka kuma, ya amince da kafa kwamitin bincike na musamman ƙarƙashin Janar Emmanuel Undiandeye. Wannan bincike ya kai ga sake yin garambawul ga shugabannin tsaro, inda aka naɗa Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Tsaron Ƙasa (CDS), yayin da aka kori shugabannin sojin ruwa da na sama.
Wani abin ban mamaki shi ne, dakarun tsaro suna neman tsohon Gwamna Timipre Sylva da wani Janar Adamu mai ritaya, waɗanda ake zargi da ɗaukar nauyin wannan shiri da maƙudan kuɗaɗe.
Ko da yake rundunar soji ta yi ta musanta batun juyin mulkin a farko tare da bayyana shi a matsayin "bincike kan rashin ɗa'a," daga baya ta fito fili ta tabbatar da gaskiyar lamarin.

Kara karanta wannan
Jerin manyan sojoji 16 da hedkwatar tsaro 'ta gano' suna da hannu a shirin kifar da Tinubu

Source: Twitter
Makomar waɗanda ake zargi
A ranar 26 ga Janairu, 2026, rundunar soji ta fitar da sanarwa cewa an kammala bincike mai zurfi wanda ya nuna cewa wasu jami'ai sun yi yunkurin kifar da gwamnati ba bisa ƙa'ida ba.
Sanarwar ta bayyana cewa irin wannan hali ya saɓa wa ɗa'a da ƙimar aikin soja, saboda haka za a gurfanar da dukkan waɗanda ke da sauran bayani a gaban kotun sojadomin su fuskanci shari'a ƙarƙashin dokar soja.
Wannan lamari ya nuna girman ƙalubalen dake fuskantar dimokuradiyyar Najeriya da kuma yadda rashin biyan buƙatun ma'aikata ko jinkirin ƙarin girma zai iya zama hanyar da masu son tada zaune tsaye ke amfani da ita wajen tunzura jami'an tsaro.
Sojoji 16 za su iya fuskantar hukuncin kisa
Tun da fari, mun ruwaito cewa, akalla jami’an soji 16 da ake zargi da yunkurin kifar da gwamnatin Bola Tinubu za su fuskanci hukunci mai tsanani idan kotu ta tabbatar da laifinsu.

Kara karanta wannan
Juyin mulki: Sojoji sun mika rahoto kan jami'ai 16 da ake zargi ga shugaba Tinubu
Rahotanni sun nuna cewa binciken da rundunar soji ta gudanar tun watan Oktoba, 2025 ya tabbatar da samunsu da hannu a yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu.
Biyo bayan lamarin, wasu tsofaffin hafsoshin soji sun ce dokar sojin Najeriya ta tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin yunkurin kifar da gwamnati.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
