Kwankwaso Ya Gana da Tsohon Gwamna bayan Ficewar Abba a NNPP? An Ji Gaskiyar Zance

Kwankwaso Ya Gana da Tsohon Gwamna bayan Ficewar Abba a NNPP? An Ji Gaskiyar Zance

  • An yada wasu rahotanni da ke ikirarin cewa madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi
  • Tsohon gwamnan na jihar Ekiti ya fito ya yi magana kan batun ya yi ganawar sirri da jagoran na jam'iyyar NNPP
  • Kayode Fayemi ya bayyana cewa alakarsa da Kwankwaso ta fara ne tun lokacin da suke rike da mukaman gwamnono a jihohinsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi, ya yi magana kan jita-jitar cewa ya yi ganawar sirri da madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso.

Kayode Fayemi ya karyata rahotannin da ke ikirarin cewa ya yi wata ganawar sirri da tsohon gwamnan na jihar Kano a gidansa da ke Abuja.

Kayode Fayemi ya musanta ganawa da Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Kayode Fayemi
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce Fayemi ya yi watsi da rahotannin ne a wata sanarwa da shugaban sashen yada labaransa, Ahmad Sajoh, ya fitar a ranar Alhamis, 29 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar da Kwankwaso ya yi fata Abba ya shiga maimakon hadewa da Ganduje a APC

Me Fayemi ya ce kan ganawa da Kwankwaso?

Kayode Fayemi wanda shi ne tsohon shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), ya bayyana ikirarin a matsayin karya tare da bukatar jama’a su yi watsi da shi.

A cewar sanarwar, tsohon gwamnan na Ekiti ya hadu da Kwankwaso sau daya ne kacal cikin shekara guda da ta wuce, kuma ba a wata ganawar siyasa ta sirri ba.

“Dr Fayemi ya hadu da Sanata Kwankwaso sau daya ne kawai a cikin shekarar da ta gabata, kuma wannan haduwar ta faru ne a wajen kaddamar da littafin tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya, Mohammed Bello Adoke, SAN, a bainar jama’a."
"A kowane lokaci Dr Fayemi bai taba yin wata ganawar siyasa ta sirri ba, kuma ba ya yin wata irin wannan ganawa da Sanata Kwankwaso, sabanin abin da aka wallafa.”

- Ahmad Sajoh

Meye alakar Fayemi da Kwankwaso?

Tsohon gwamnan ya amince cewa shi da Kwankwaso abokai ne tun lokacin da suke gwamnonin jihohi, amma ya jaddada cewa alakar tasu ta shafi zumunci ne kawai, ba tare da wata alaka ta jam’iyya ba.

Kara karanta wannan

Badaru ya gana da Kwankwaso bayan ficewar Abba daga NNPP? An gano gaskiya

Ya bayyana cewa zumuncin nasu ya ginu ne bisa mutunta juna da kuma burin ganin Najeriya ta ci gaba, ba bisa wata fahimtar siyasa ko hadin gwiwar jam’iyya ba.

Kayode Fayemi ya ce bai gana da Kwankwaso ba
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi Hoto: Kayode Fayemi
Source: Facebook

Fayemi ya kuma yi gargadi kan yunkurin wasu ‘yan siyasa na kokarin alakanta zumuncin kashin kai da siyasa, inda ya nuna cewa da dama daga cikin abokansa da makusantansa ba sa cikin harkokin jam’iyya ko kuma suna cikin jam’iyyu daban-daban.

Sanarwar ta kara da cewa abokan hulɗar Fayemi sun fito ne daga kusan dukkan bangarorin siyasar Najeriya.

Ganduje ya bude kofar sulhu da Kwankwaso

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bude kofar sulhu da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Ganduje ya bayyana cewa ya buɗe zuciya domin daidaita bambance-bambancen siyasa da Kwankwaso, duk da dogon sabanin da ya shiga tsakaninsu a baya.

Tsohon gwamnan na Kano ya ce ya ce a matsayinsu na Musulmi, sulhu da fahimtar juna abu ne da ya dace a ko da yaushe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng