Majalisa Ta Ware Jiha 1 a Arewa da Take So Jami'an Tsaro Su Kai Jerin Hare Hare
- Majalisar wakilai ta bukaci a yi amfani da jiragen yaki wajen fatattakar 'yan bindiga dake addabar kananan hukumomin Akko a jihar Gombe
- Hon Usman Bello Kumo ya koka kan yadda aka kashe mutane shida aka sace mutane 20 a kwanan nan a yankunan Garin Galadima
- Jami'an 'yan sanda sun samu umarnin tura karin dakarun kwantar da tarzoma domin tabbatar da tsaro da kuma dakile hare-haren 'yan bindiga
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Majalisar Wakilai ta ƙasa ta umarci jami'an tsaro da su ƙaddamar da manyan hare-haren haɗin gwiwa a dukkan mabuyar 'yan ta'adda a Gombe.
Majalisar ta ce hare-haren za su hada da amfani da jiragen yaƙi da dakarun ƙasa, domin kakkabe ƴan bindigar da ke addabar al'ummar ƙaramar hukumar Akko dake jihar.

Source: Twitter
Majalisa ta ba da umarnin kai hare-hare Gombe
Wannan mataki ya biyo bayan amincewa da wani kudurin gaggawa da babban mai tsawatarwa na majalisar, Hon. Usman Bello Kumo, ya gabatar in ji rahoton The Guardian.
Jaridar ta rahoto cewa Hon. Usman Kumo ya gabatar da kudurin da ke bukatar amincewar gaggawar ne a ranar Laraba yayin zaman majalisar da Abbas Tajudeen ya jagoranta.
Majalisar ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ba babban jami'in tsaron ƙasa umarnin fara kai farmakin gaggawa domin rusa dukkan sansanonin ƴan bindiga a yankin.
Kisan mutane da sace wasu 20 a Akko
Yayin gabatar da buƙatar tasa, Hon. Kumo ya nuna damuwarsa kan yadda aka kashe mutane shida tare da yin garkuwa da wasu mutane 20 a garuruwan Garin Galadima, Pindiga, Garin Jaji, da Laro a kwanan nan.
Hon. Kumo ya jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyi babban nauyi ne da sashi na 14(2)(b) na kundin tsarin mulki ya ɗora wa gwamnati, kamar yadda rahoton Vanguard ya nuna.
Majalisar ta yi shiru na minti ɗaya domin karrama waɗanda suka rasa rayukansu, sannan ta umarci sufeto janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun, da ya tura ƙarin jami'an MOPOL domin gudanar da sintiri a kai-a-kai.
Neman tallafi ga waɗanda harin ya shafa
Baya ga matakan tsaro, majalisar ta bukaci hukumomin NEMA da NEDC da su kai tallafin kayan abinci da matsuguni ga ɗumbin mazauna yankin da suka rasa gidajensu sakamakon waɗannan hare-hare.
Haka kuma, an umarci kwamitocin majalisar kan harkokin tsaro, sojin ƙasa, sojin sama, da ƴan sanda da su riƙa gabatar da rahoton ayyukan jami'an tsaron mako-mako har sai zaman lafiya ya dawo yankin.
Hon. Kumo ya yi gargaɗin cewa majalisar za ta sanya ido sosai kan yadda jami'an tsaro ke gudanar da wannan aiki, domin tabbatar da cewa an daina asarar rayukan al'ummar Jihar Gombe.
Jami'an tsaro sun gwabza da 'yan bindiga
A wani labari, mun ruwaito cewa, rundunar ‘yan sandan Gombe ta tabbatar da kashe wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, tare da ceto wasu daga cikin mutanen da aka sace.
Lamarin ya faru ne bayan ‘yan ta'addan sun kasa kai farmaki a wasu yankuna sakamakon tsauraran matakan tsaro, sai dai daga bisani suka kai hari a wani kauye.
Rundunar ‘yan sanda ta ce ana cigaba da bincike da farautar sauran ‘yan ta'addan da suka tsere, tare da bukatar jama’a su ci gaba da bayar da bayanai ga hukumomi.
Asali: Legit.ng

