Sanata Ndume Ya Dauko da Zafi, Ya Tona Asirin Wasu Hadimai na Kusa da Shugaba Tinubu

Sanata Ndume Ya Dauko da Zafi, Ya Tona Asirin Wasu Hadimai na Kusa da Shugaba Tinubu

  • Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume ya sake caccakar hadiman shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kan halin da kasa ke ciki
  • Ndume ya bayyana cewa Tinubu ya zagaye kansa da wadanda ba su san siyasa ba, shi yasa bai san halin da 'yan Najeriya ke ciki ba
  • Dan Majalisar dattawan ya yi gargadin cewa matukar Tinubu bai dauki matakin gyara ba, to hakan zai shafi sakamakon zabe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Sanata Ali Ndume, mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya soki wasu daga cikin hadimai na kusa da Shugaba Bola Tinubu.

Sanatan ya yi zargin cewa shugaban kasa yana samun shawarwari marasa kyau daga masu ba shi shawara wadanda ba su fahimci siyasa ko sanin halin da talakawa ke ciki ba.

Kara karanta wannan

Ana batun sauya shekar Abba, za a bayyana asalin wadanda suka ci amanar Kano

Sanata Ali Ndume.
Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar dattawa, Ali Ndume Hoto: Muhammad Ali Ndume
Source: Facebook

Ndume ya fadi haka ne yayin da yake magana a ranar Laraba a cikin wani shiri na gidan talabijin na Arise TV.

Sanata Ndume ya fadi koken 'yan Arewa

Sanata Ndume ya gargadi cewa rashin gamsuwa da salon mulkin Tinubu da ke kara yaduwa yankin Arewa na iya shafar sakamakon zabe mai zuwa idan ba a dauki matakan gaggawa ba.

Ya ce:

“Duk wanda ya gaya maka cewa Arewa ba korafi ko kunci yanzu, to ba gaskiya yake fada maka ba. Wannan koken zai fito fili a kuri’unsu idan ba a gyara ba. Amma babban abin farin cikin shi ne, shugaban kasa na da damar gyara abubuwa.”

Tinubu ya gana da wasu dattawan Arewa

Ndume ya bayyana cewa shugabannin Arewa sun yi kokarin tattaunawa da shugaban kasa domin gyara al'amura, inda ya ce shi kansa ya halarci tarukan da aka yi tsakanin Tinubu da dattawan Arewa.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Yadda Kanal na soja ya tsara kifar da Gwamnatin Bola Tinubu

“A Arewa, dattawa sun dade suna neman ganawa da shugaban kasa. Na kasance daya daga cikin wadanda suka halarci taron farko da na karshe da shugaban kasa ya yi da dattawan Arewa.
"Ya nuna a shirye yake a yi gyara, har ma ya zo da dukkan manyan jami’an gwamnatin tarayya ‘yan Arewa kuma an tattauna sosai. Ya yi alkawarin cewa za a ci gaba da tattaunawa, amma hakan bai faru ba.”

- In ji Sanata Ali Ndume.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana jagorantar taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) Hoto: @DOlusegum
Source: Twitter

Ndume ya dora laifi kan mukarraban Tinubu

Sanata Ndume ya kare shugaba Tinubu, inda ya dora laifin a kan mutanen da ke kewaye da shi, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

"Ka san me nake zargi? Shugaban kasa ba shi ne matsalar ba; mutanen da ke kewaye da shi ne asalin matsalar,” in ji shi.

Sanata Ali Ndume ya ayyana wasu daga cikin hadimin shugaban kasar na yanzu a matsayin wadanda ke rayuwar jin dadi kuma ba su san halin da kasa ke ciki ba.

Ndume ya hango matsala ga APC

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, Ali Ndume, ya yi tsokaci kan yawan sauya shekar da ake yi zuwa jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

An gano abin da Shugaba Tinubu ya taka, ya kusa faduwa a kasar Turkiyya

Sanata Ndume ya yi gargadin cewa jam’iyyar APC mai mulki na iya shiga mummunar matsala saboda yawan sauya shekar gwamnoni da ‘yan majalisa zuwa cikinta.

Dan Majalisardattawan ya yi ikirarin cewa yawancin masu sauya sheka ba sa bada wata gudunmawa bayan shigowa cikin jam’iyyar APC, yana mai cewa hakan matsala ce babba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262