Bayan Shiga APC, Abba zai Kawo Karshen Rikicin Sanusi II da Aminu Ado Bayero

Bayan Shiga APC, Abba zai Kawo Karshen Rikicin Sanusi II da Aminu Ado Bayero

  • Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa rikicin masarautar da ya dade yana jawo ce-ce-ku-ce zai samu mafita ta hanyar fahimtar juna da tattaunawa da hukumomi
  • Kwamishinan yada labarai ya ce an riga an ɗauki matakai masu ƙarfi domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin jihar ba tare da tauye doka ba
  • Haka kuma, gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ce sauya shekar gwamna zuwa jam'iyyar APC mai mulki zai bude sababbin kofofi na ci gaba ga Kano baki daya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano ta bai wa al’ummar jihar tabbacin cewa rikicin masarautar Kano da ya dade yana daukar hankalin jama’a zai zo karshe cikin lumana nan ba da jimawa ba.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Ibrahim Waiya, ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Kano.

Kara karanta wannan

Matashin da ya mallaki bindiga a Kano ya yi wa mahaifiyarsa dukan tsiya

Aminu Ado Bayero, Muhammdu Sanusi II da Abba Kabir Yusuf
Sarki Aminu Ado Bayero, Khalifa Muhammadu Sanusi da gwamna Abba Kabir Yusuf. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa|Masarautar Kano
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa ya ce gwamnatin jihar ta kuduri aniyar magance dukkan batutuwan da suka shafi masarautar ta hanyar mutunta doka, al’ada, da kuma muradun al’ummar Kano baki daya.

Matakan gwamnati kan rikicin masarauta

Daily Nigerian ta wallafa cewa Ibrahim Waiya ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta riga ta shimfida tsare-tsare masu karfi domin tabbatar da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa.

Ya ce gwamnati na ci gaba da tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da shugabannin gargajiya da sauran bangarori, domin tabbatar da cewa batun masarautar bai ci gaba da haifar da tashin hankali ba.

A cewarsa, manufar gwamnatin ita ce ganin an warware rikicin ta yadda ba zai kawo tarnaki ga tafiyar da mulki ko zaman lafiyar al’umma ba.

Karin bayani kan rikicin sarautar Kano

Kwamishinan ya jaddada cewa duk wani mataki da gwamnati ke dauka na karkashin ka’idar bin doka da oda, tare da mutunta cibiyoyin gargajiya da tarihinsu.

Kara karanta wannan

Ana batun sauya shekar Abba, za a bayyana asalin wadanda suka ci amanar Kano

Ya ce gwamnatin ta yi imanin cewa magance rikicin masarautar ta hanya mai kyau zai taimaka wajen karfafa hadin kai da fahimtar juna a tsakanin jama’a.

Batun sauya shekar Abba Kabir

Da yake tsokaci kan sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar APC, Ibrahim Waiya ya bayyana hakan a matsayin wani ci gaba da zai amfani jihar Kano matuka.

Ya ce al’ummar jihar za su ci gaba da samun karin ribar dimokuradiyya, musamman ganin kusantar gwamnatin jiha da ta tarayya.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf yana jawabi ga jama'a. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

A cewarsa, hakan zai jawo karin tallafi, ayyukan raya kasa, da tsare-tsaren ci gaba a bangarori kamar su abubuwan more rayuwa, lafiya, ilimi, da jin dadin jama’a.

Ganduje ya nemi sulhu da Kwankwaso

A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje ya nuna cewa zai iya sulhu da Rabiu Kwankwaso.

Dr. Ganduje ya bayyana cewa shi da Kwankwaso Musulmai ne saboda haka babu wani abu da zai hana su sulhu bayan sabanin siyasa.

Baya ga maganar addini ya hada su, Ganduje ya bayyana cewa shi dan uwa ne da Rabiu Musa Kwankwaso kuma sun yi siyasa tare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng