Yadda Aka Kama Kayan Hada Bama Bamai Masu Yawa Za a Kai wa Ƴan Bindiga a Zamfara
- Rundunar 'yan sandan Zamfara ta kama wani mutum mai shekaru 38 yana dauke da abubuwan fashewa har guda 954 a cikin motarsa
- Akwai zargin cewa mutumin na kan hanyar kai wa 'yan bindiga wadannan abubuwan fashewar ne domin kera bama-bamai a Zamfara
- Yayin da 'yan sanda suka dauki wasu matakai, jami'an sashin kwance bama-bamai na rundunar sun fara binciken kayan da aka kama
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara - Rundunar 'yan sandan Zamfara ta kama wani Mustapha Mohammad, bisa zargin mallakar wasu abubuwa da ake zargin na hada bama bamai ne ba bisa ƙa'ida ba.
Jami'an rundunar na musamman da ke yaƙi da hakar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba ne suka yi wannan kamen, biyo bayan samun sahihan bayanan sirri kan zirga-zirgar wanda ake zargin.

Source: Twitter
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, a cewar rahoton Punch.
An gano kayan hada bama bamai a Zamfara
A cikin sanarwar, DSP Yazid ya ce 'yan sanda sun samu nasarar kama wanda ake zargin tare da kayayyakin yayin da yake tuka wata mota samfurin Toyota Corolla.
Bayan tsayar da motar da Mustapha Mohammad yake ciki, jami'an 'yan sanda sun gudanar da bincike na tsanaki wanda ya kai ga gano abubuwan fashewar guda 954.
Sanarwar ta bayyana cewa:
"A ranar 27 ga Janairu, 2026, da misalin ƙarfe 4:15 na yamma, jami'anmu sun yi nasarar kama Mustapha Mohammad. Binciken motarsa ya bankaɗo abubuwan fashewa guda 954 da aka ɓoye a cikin buhu."
Hukumar 'yan sandan ta bayyana cewa akwai zargin cewa wanda ake zargin ya na hanyar kai waɗannan abubuwan fashewar ne ga 'yan bindiga domin su kera bama-bamai na gida (IEDs).

Kara karanta wannan
Shiri ya baci: 'Yan Boko Haram sun kashe sojoji, sun cafke wani babban soja a Borno
Matakin da 'yan sanda suka ɗauka
A halin yanzu, wanda ake zargin yana hannun jami'an tsaro inda ake gudanar da bincike, kamar yadda rahoton jaridar The Guardian ya nuna wannan.
Su kuma kayayyakin fashewar da aka gano, an miƙa su ga sashen kwance bama-bamai na rundunar (EOD) domin gudanar da binciken ƙwararru da kuma adana su cikin tsaro.
DSP Abubakar ya ƙara da cewa:
"Ana ci gaba da bincike domin gano asalin waɗannan kayayyaki, inda aka nufa da su, da kuma kamo sauran mutanen da ke da hannu a cikin wannan danyen aiki."

Source: Original
Kama abubuwan fashewa a Oyo
Wannan kamen na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da rundunar 'yan sandan Jihar Oyo ta sanar da kama wata babbar mota maƙil da abubuwan fashewa a garin Saki ranar 25 ga Janairu, lamarin da ke nuna ƙaruwar matakan tsaro a faɗin ƙasar.
Rundunar 'yan sandan Zamfara ta tabbatar wa jama'a cewa za ta ci gaba da sanar da su duk wani sabon bayani da aka samu yayin da bincike yake ƙara zurfafa kan lamarin.
An kama abubuwan fashewa a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’an ‘yan sanda a jihar Kano sun kama kayan fashewa da miyagun kwayoyi a samame daban-daban da suka kai cikin birnin Kano.
An gano buhunan abubuwan fashewa da miyagun kwayoyi a Tudun Bojuwa da Sani Mainagge, yayin da jami’an leken asiri suka yi aiki bisa rahotonnin sirri.
Haka kuma, 'yan sanda sun kama wani direban babur da ake zargi da safarar kayan fashe wa daga Jihar Nasarawa zuwa wasu wurare, inda ake ci gaba da bincike sosai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

