Akpabio Ya Saɓa da Kwamitin Majalisa, Ya Kare Tinubu kan Zargin Cushe a Dokokin Haraji

Akpabio Ya Saɓa da Kwamitin Majalisa, Ya Kare Tinubu kan Zargin Cushe a Dokokin Haraji

  • Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi magana a kan zargin majalisar wakilai kan sauya dokar haraji
  • Yana wannan magana ne bayan kwamitin da Majalisar Wakilai ta ce ta tabbatar da cewa an taɓa dokokin harajin
  • Amma a cewar Akpabio, dokokin da aka sanya hannu kuma aka wallafa su ne dai-dai da abin da majalisar tarayya ta yanke

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya yi watsi da zargin cewa an canza sababbin dokokin haraji bayan Majalisar Tarayya ta amince da su.

Ya bayyana cewa dokokin da aka wallafa a jaridar gwamnati kuma Shugaban Ƙasa ya sanya wa hannu sun yi daidai da ƙudurorin da ’yan majalisa suka amince da su a duka bangarorin majalisar.

Kara karanta wannan

Sanata ya sake taso da batun harin Amurka a Najeriya, ya fadi kuskuren Tinubu

Sanata Godswill Akpabio ya ƙaryata zargin cushe a cikin dokokin haraji
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu tare da Sanata Godswill Akpabio Hoto: Reno Omokri
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito Akpabio ya bayyana hakan ne yayin zaman majalisar dattawa, a matsayin martani ga ikirarin da ɗan Majalisar Wakilai, Abdussamad Dakuku, ya yi.

Ɗan majalisar wakilai ta magantu kan dokokin haraji

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Dakuku ya nuna cewa dokokin gyaran haraji da majalisa ta amince da su sun bambanta da abin da aka fitar daga baya zuwa hannun jama’a.

Sai dai Akpabio ya ce wannan zargi ba shi da tushe. Ya jaddada cewa duk wata takarda da ba Majalisar Tarayya ce ta fitar da ita tare da tantancewa ba, ba za a ɗauke ta a matsayin sahihiya ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya mika sababbin kudurorin doka 24 ga majalisa, an ji abin da suka kunsa

Shugaban majalisar dattawan ya ƙara da cewa dokokin sun fito ne bayan dogon nazari a majalisar dattawa da majalisar wakilai, sannan aka sasanta bambance-bambancen da ke tsakanin bangarorin biyu kafin a kammala aikin dokokin.

Ya ce:

“Babu wata lalata wa ko sauya doka ko kaɗan a cikin dokokin da Shugaban Ƙasa ya sanya wa hannu."

Ya bayyana cewa dokoki huɗu da suka shafi haraji sun bi dukkanin matakan dokoki, inda majalisa ta amince da su, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sanya hannu, sannan aka wallafa su a hukumance.

Majalisa za ta raba dokokin haraji ga Sanatoci

Akpabio ya kuma bayyana cewa magatakardar Majalisar Tarayya ta tantance dokokin domin kauce wa ruɗani a tsakanin jama'a.

Za a raba dokokin haraji da Tinubu ya sa wa hannu ga Sanatoci
Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio tare da Mataimakinsa, Barau I Jibrin Hoto: Barau I Jibrin
Source: Facebook

A kalamansa:

“Dokokin huɗu sun kammala, an wallafa su, Shugaban Ƙasa ya sanya hannu, sannan magatakardar Majalisar Tarayya ta tabbatar da su domin a guje wa rikice-rikice."

Ya umarci magatakardar majalisar dattawa da ta raba sahihin kwafin dokokin da Bola Tinubu ya sa wa hannu ga dukkanin Sanatoci.

Kara karanta wannan

Shugaban hukumar alhazai ya hakura da gwamnatin Abba, ya yi murabus

Wadanda ke wurin zaman za su karɓa nan take, yayin da waɗanda ba su halarta ba za a ba su daga baya.

Ya kuma yi gargaɗin cewa kada a fitar da dokokin ta hanyoyin da ba na hukuma ba, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen dakile jita-jita da yaɗa bayanan ƙarya.

An ƙirƙiri batun zabe a Majalisa

A bangare guda kuma, Majalisar dattawa ta jinkirta tattauna rahoton kwamitinta kan harkokin zaɓe.

Shugaban masu rinjaye a majalisar, Opeyemi Bamidele, ya ce an ɗauki matakin ne saboda rashin halartar shugaban kwamitin, Sanata Simon Lalong.

Ya ƙara da cewa duk da an riga an raba rahoton, sanatoci na buƙatar ƙarin lokaci domin yin nazari mai zurfi.

Kara karanta wannan

An gano jiha 1 da Tinubu zai iya amincewa a kirkira a Najeriya

Akpabio ya goyi bayan jinkirin, yana mai cewa majalisar za ta fi son yin aiki a hankali da bin doka da adalci, maimakon gaggawa.

Ya ce:

“Ba mu buƙatar gaggauta rahoton; bin ƙa’ida da adalci ne za su jagoranci matakin majalisar.”

Majalisa: "An yi cushe a dokokin haraji"

A baya, mun wallafa cewa bangaren marasa rinjaye na Majalisar Wakilai ya tabbatar da cewa an yi sauye-sauye a dokokin harajin Najeriya da suka fara aiki a shekarar 2026.

’Yan majalisar sun ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa an yi cushe ko gyare-gyare ne bayan sun gama aikinsu, sannan Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya sa hannu.

Wannan bayani ya fito ne daga rahoton wucin gadi na kwamitin bincike na musamman da bangaren marasa rinjaye na Majalisar Wakilai ya kafa domin bincikar zargin sauya dokokin harajin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng