Sanata Ya Sake Taso da Batun Harin Amurka a Najeriya, Ya Fadi Kuskuren Tinubu
- Sanatan da ke wakiltar Bauchi ta Tsakiya a majalisar dattawa, Abdul Ningi, ya soki harin da Amurka ta kawo a Najeriya
- Abdul Ningi ya bayyana cewa harin ya keta 'yancin Najeriya kuma ya sabawa yarjejeniyar majalisar dinkin duniya
- 'Dan majalisar ya koka kan yadda Mai girma Bola Tinubu ya bar majalisar tarayya cikin duhu kan hare-haren da Amurka ta kawo
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Sanatan Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi, ya soki hare-haren sama da Amurka ta kai tare da haɗin gwiwar sojojin Najeriya kan kungiyoyin ta’addanci a wasu sassan ƙasar, ciki har da Jihar Sokoto.
Ningi, wanda mamba ne a jam’iyyar PDP ya bayyana hare-haren a matsayin keta ’yancin ikon Najeriya da kuma saba wa yarjejeniyar majalisar dinkin duniya.

Source: Facebook
Jaridar Premium Times ta ce Sanata Abdul Ningi ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 28 ga watan Janairun 2026 a zauren majalisar dattawa

Kara karanta wannan
Jerin manyan sojoji 16 da hedkwatar tsaro 'ta gano' suna da hannu a shirin kifar da Tinubu
Sanatan ya ce irin waɗannan ayyukan na sojoji ya kamata a gudanar da su ne bayan samun amincewar majalisar tarayya tare da haɗin gwiwa da hukumomin tsaron cikin gida.
Me Sanata Abdul Ningi ya ce kan Tinubu?
Sanatan ya yi zargin cewa shugaban kasa ya gaza sanar da ’yan majalisa kafin da kuma bayan aiwatar da harin, lamarin da ya ce ya tauye nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora musu.
“Wani lokaci a watan Disamba, Amurka ta hannun rundunar sojojinta ta shiga yankin Najeriya, wanda hakan babban keta kundin tsarin mulki ne, kuma har ila yau babban saba wa yarjejeniyar majalisar dinkin duniya."
- Abdul Ningi
Abdul Ningi ya amince cewa duk da shugaban kasa a matsayinsa na babban kwamandan rundunonin sojoji na da ikon neman taimakon sojojin kasashen waje, amma dole ne a yi hakan tare da goyon bayan majalisar tarayya.
“Abin da shugaban kasa zai iya yi shi ne ya gayyaci irin waɗannan rundunoni su shigo Najeriya su yi aiki tare da jami’an tsaron cikin gida tare da ba su umarnin da suka dace."
"Amma idan muka bar wannan lamari ba tare da majalisa ta yi magana ba, gwamnati za ta ce an sanar da su ne kawai, alhali dole ne majalisa ta yi magana duk da kyakkyawar niyyar sojojin Amurka."
- Abdul Ningi
Ningi ya koka kan rashin masaniya a harin Amurka
Sanatan ya jaddada cewa majalisar tarayya na da muhimmin nauyi da alhaki a harkokin mulki, kuma bai kamata a ɗauke ta a matsayin abin da ke biye wa ɓangaren zartarwa kawai ba.
Abdul Ningi ya kuma koka da cewa tun bayan dawowar majalisar tarayya daga hutun Kirsimeti da sabuwar shekara, ba a yi wa ’yan majalisa wani bayani kan lamarin ba.
Sanata Ningi ya yi gargadi
Ya gargadi cewa gaza tabbatar da sa ido na majalisa kan ayyukan gwamnati na iya jefa ’yan majalisa cikin barazanar tsangwama daga waje, yana mai cewa dole ne bangaren zartarwa ya rika sanar da shugabannin majalisar tarayya kan muhimman batutuwan tsaro.

Source: Twitter
Da yake mayar da martani, shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce ya yi niyyar yi wa ’yan majalisa bayani ne da aka koma zaman majalisa a ranar Talata, amma rasuwar Sanata Godiya Akwashiki ta kawo cikas ga shirin.

Kara karanta wannan
Wata 6 bayan shiga ADC, tsohon Sanata a Sokoto ya dawo PDP, ya jingina zargi ga Tambuwal
Tashar Channels tv ta ce Akpabio ya kara da cewa za a tattauna batun a zaman sirri, yana mai jaddada cewa an aiwatar da harin ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaron Najeriya.
An gayawa Tinubu illar sauya Shettima
A wani labarin kuma, kun ji cewa Kungiyar 'APC Youth Parliament North East' ta nuna damuwa kan batun sauya Kashim Shettima a zaben 2027.
Kungiyar ta ce masu kiran a sauya Shettima daman suna gaba da gwamnatin Bola Tinubu tun farko sai yanzu Allah ya tona musu asiri suka bayyana mummunan manufarsu.
Hakazalika matasan sun bayyana cewa masu kiran sauya mataimakin shugaban kasar suna fada ne da Mai girma Bola Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
