NNPCL Ya Bi Sahun Matatar Dangote, Ya Kara Farashin Litar Man Fetur
- Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya fara sayar da litar fetur a kan sabon farashi jim kadan bayan matatar Dangote ta kara kudi
- Karin da kamfanin NNPCL ya yi tuni ya shafi jihar Legas da babban birnin tarayya Abuja, inda tuni aka fara sayar da man a sabon farashi
- Sabon karin da NNPCL ya yi na zuwa a daidai lokacin da matatar Dangote ta kara farashin kowace litar mai zuwa N799 a jiya
A’isha Ahmad, edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku, musamman kan al’amuran da suka shafi mata da yara, siyasa da harkokin tattalin arziki.
Jihar Lagos — Kamfanin Man Fetur na Kasa, NNPCL ya sake daidaita farashin sayar da man fetur a gidajen mai da ya mallaka.
A yanzu, ana sayar da kowace lita a kan N835 a Legas da kuma N839 a Abuja, jim kadan bayan matatar Dangote ta kara farashin mai.

Source: Getty Images
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa wannan sabon mataki ya kara tayar da muhawara a tsakanin jama’a, musamman a wannan lokaci da ake fama da tsadar rayuwa a sassa da dama na kasar nan.
Bincike ya nuna cewa NNPCL ya fara aiwatar da sabon farashin a dukkannin gidajen man ta da ke manyan biranen biyu.
Sabon farashin ya nuna karin N50 idan aka kwatanta da tsohon farashin N785 a Legas, yayin da aka samu karin N20 daga N815 zuwa N839 a Abuja.
Masu saye sun bayyana damuwa kan yadda karin farashin ke shafar sufuri, abinci da sauran bukatun yau da kullum.
Karin farashin NNPCL ya biyo bayan Dangote
Wannan sabon karin farashi na NNPCL ya zo ne kasa da awanni 24 bayan matatar Dangote ta sanar da karin farashin man fetur a matakin zuwa N799 kan kowace lita.
Babban Darakta a matatar, David Bird, ya bayyana cewa matatar na ci gaba da samar da kusan lita miliyan 50 na man fetur a kullum domin biyan bukatar kasuwar cikin gida.
Ya kara da cewa jigilar mai da rabon sa zuwa sassa daban-daban na kasar nan na gudana cikin sauki, ba tare da samun tsaiko ba.

Source: Facebook
Bird ya kuma jaddada cewa sassaucin tsarin aiki na matatar na ba ta damar tace nau’o’in danyen mai da kayan ciyarwa na tsaka-tsaki iri-iri.
A cewarsa, wannan tsari yana tabbatar da ci gaba da samar da man fetur ko da a lokutan da ake gudanar da gyare-gyaren tsari da aka tanada.
Bayan sanarwar, matatar ta ce gidajen man hadin gwiwa da ita, ciki har da MRS, za su rika sayar da fetur a kan N839 kan kowace lita, daga tsohon farashin N739.
A bangare guda, hukumar kula da harkokin man fetur ta NMDPRA ta bayyana kwarin gwiwar cewa karuwar gasa a bangaren rarraba man fetur za ta taimaka wajen rage farashi a nan gaba.
Kamfanin NNPCL ta fusata gwamnoni
A baya, kun ji cewa sabuwar takaddama ta kunno kai tsakanin Kamfanin Man Fetur na Kasa, NNPCL da kuma kamfanin da ke yi wa Gwamnoni aiki, Periscope Consulting.
Gwamnonin jihohi sun dauki kamfanin aiki domin binciken wasu kudi da ake zargin ba a tura su zuwa asusun Tarayya ba, lamarin da ya dagula alakar da ke tsakaninsu.
Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) na zargin cewa NNPCL bai tura kimanin Dala biliyan 42.37 na kudaden da aka samu daga harkokin mai zuwa asusun Tarayya ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


