Jirgin Soja Ya Yi Ruwan Wuta kan Jama'a bisa Kuskure a Neja, an Rasa Rayuka
- Akalla manoma biyu sun mutu yayin da wasu da dama ciki har da yara suka jikkata sakamakon wani hari ta sama da aka ce kuskure ne a Jihar Neja
- Mazauna yankin sun ce jirgin saman leƙen asiri ya yi shawagi na wasu mintuna kafin ya buɗe wuta kan gidaje ba tare da wani gargadi ba
- Bayan aukuwar wannan abu wanda ba shi ne na farko ba, mutane da dama suka tsere daga gidajensu zuwa kauyen Bangi da sauran wuraren da ke kusa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Neja – Akalla manoma biyu ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama ciki har da yara suka jikkata, sakamakon wani hari ta sama a ƙauyen Kurgi da ke ƙaramar hukumar Mariga a Jihar Neja.
Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, bayan da wani jirgin saman leƙen asiri na soji ya yi ta shawagi a saman al’ummar na tsawon lokaci.

Source: Original
Daily Trust ta wallafa cewa har yanzu rundunar sojin saman Najeriya da sauran hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da harin.
Yadda jirgin soji ya saki wuta a Neja
Mazauna ƙauyen Kurgi sun shaida wa manema labarai cewa jirgin ya yi shawagi a sararin samaniya na wasu mintuna kafin daga bisani ya buɗe wuta.
Wata majiya ta ce harbin ya faɗa ne kai tsaye kan gidajen mutane, inda wasu suka samu raunuka a cikin gidajensu ba tare da sun fita waje ba.
Wani mazaunin yankin, Suleiman Sanusi, ya ce lamarin ya zo musu da mamaki matuƙa, domin ba su yi wani abu da zai jawo irin wannan hari ba.
Mutane sun gudu bayan sakin wutar
Aminiya ta wallafa cewa Suleiman Sanusi ya bayyana cewa harin ya ƙara tsoratar da jama’a, inda da dama suka fara barin gidajensu domin tsira da rayukansu.
A cewarsa, wasu daga cikin mutanen sun tsere zuwa garin Bangi, yayin da wasu suka nemi mafaka a ƙauyuka da garuruwa makwabta.
Kira ga hukumomi bayan harin
Mazauna yankin sun yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta bincike kan abin da ya faru domin gano hakikanin dalilin harin.
Sun kuma buƙaci a tallafa wa waɗanda suka jikkata ta hanyar ba su kulawar lafiya cikin gaggawa, tare da taimakon iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

Source: Twitter
A ‘yan shekarun nan, an samu rahotannin hare-haren sama da aka ce kuskure ne a wasu jihohin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
A watan Disamba, 2024, BBC ta rahoto cewa wani hari ta sama ya kashe mutane 10 a Jihar Sokoto, inda gwamnatin jihar ta bayyana cewa an yi kuskuren kai harin kan fararen hula bayan Kaduna da Zamfara.
An kama mai hada makamai a Nasarawa
A wani labarin, mun kawo muku cewa Dakarun sojojin Najeriya sun kai farmaki wani gida da aka samu bayanai cewa ana kera makamai.
Dakarun Najeriya sun tabbatar da cewa sun kama mutum daya yana kokarin guduwa ta kan bishiya yayin da wasu abokansa suka tsere.
Bayan dogon bincike a gidan, jami'an tsaro sun gano bindigogin gida, makudan kudi, wayar hannu da wasu kayayyakin da ake hada makamai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


