Najeriya da Turkiyya Sun Cimma Yarjejeniya a kan Tsaro

Najeriya da Turkiyya Sun Cimma Yarjejeniya a kan Tsaro

  • Najeriya ta yi nasarar cimma sababbin yarjejeniyoyin tsaro da Türkiye domin da ake sa ran zai taimaka wajen yaki da ta'addanci
  • Shugabannin kasashen biyu sun kulla yarjejeniyoyi tara a Ankara, babban birnin kasar bayan an gana a kan ciyar da kasashen gaba
  • An cimma matsaya kan horar da sojoji, musayar bayanan sirri da yaki da ta’addanci da ya addabi kasar nan ta fuskoki da dama

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Ankara, Turkiye – Najeriya ta kulla sababbin yarjejeniyoyin tsaro da kasar Türkiye domin kara karfin yaki da matsalolin rashin tsaro da ke addabar kasar nan.

Wannan na zuwa a lokacin da kasar nan ke fama da matsalolin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane da hare-haren ta'addanci.

Kara karanta wannan

Hadimin Shugaban kasa: Abin da ya kai Bola Tinubu Turkiyya daga dawo wa Najeriya

Najeriya ta kulla yarjejeniya da Turkiyya
Shugabannin Najeriya Bola Tinubu, takwaransa na Turkiyya, Raccep Tayyip Erdogan da mukarrabansu bayan sa hannu a kan yarjejeniyoyi 9 Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa an rattaba hannu kan yarjejeniyoyi tara tsakanin kasashen biyu a ranar Talata, a gaban Shugaban Türkiye, Recep Tayyip Erdoğan, da Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.

Najeriya da Turkiyya sun kulla yarjejeniya

Aminiya ta wallafa cewa sanya hannu kan yarjejeniyoyin ne bayan ganawar sirri da kuma taron manyan jami’an kasashen biyu da aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa da ke Ankara, babban birnin Türkiye.

Kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da fahimtar juna a fannoni da dama, daga ciki har da manufofin ‘yan kasashen waje.

Sauran sun hada da kafafen yada labarai da sadarwa, manyan makarantu, hadin gwiwar soji da kuma hulda tsakanin makarantu na diflomasiyya.

Haka kuma, an amince da wata sanarwa ta hadin gwiwa da ta kafa Kwamitin Tattalin Arziki da Cinikayya na Hadin Gwiwa (JETCO).

Shugaba Erdoğan ya jaddada kudirin Türkiye na taimakawa Najeriya wajen yaki da ta’addanci.

Kara karanta wannan

Jerin manyan sojoji 16 da hedkwatar tsaro 'ta gano' suna da hannu a shirin kifar da Tinubu

Ya kara da cewa kasarsa ta duba hanyoyin kara hadin gwiwa a horar da sojoji da kuma musayar bayanan sirri yayin tattaunawa da Shugaba Tinubu.

Bola Tinubu na ziyarar aiki a Turkiyya

Tinubu na ziyarar aiki a Türkiye daga ranar 26 zuwa 28 ga Janairu, 2026 inda ake sa ran kasashen biyu za su kulla karin yarjejeniyoyi.

Haka kuma suna ganawa da shugabannin kasuwanci da masana’antar tsaro domin zurfafa dangantakar dabaru.

Daya daga cikin muhimman yarjejeniyoyin ita ce Yarjejeniyar Horon Soji da Bayanai (2026), wadda aka ayyana a hukumance a matsayin 'Protocol on Military Cooperation.'

Turkiyya za ta taimaka wa Najeriya ta fuskar tsaro
Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Wannan yarjejeniya na bai wa kwararrun Türkiye damar horar da rundunonin musamman na Najeriya tare da raba bayanan tauraron dan adam domin yaki da kungiyoyin ta’addanci irin su Boko Haram.

Yarjejeniyar ta mayar da hankali kan muhimman fannoni uku: musayar bayanan sirri kai tsaye tsakanin hukumar leken asirin Najeriya (NIA) da ta Türkiye (MİT).

Sai kuma horar da sojoji kan yaki da ‘yan tawaye da yaki a birane, da kuma kafa dunkulalliyar hadin gwiwa wajen yaki da ta’addanci a yankin Sahel da Tafkin Chadi.

Kara karanta wannan

Juyin mulki a Najeriya: Ana zargin sojojin da aka kama na cikin mawuyacin hali

Shugaba Erdoğan ya ce Türkiye na tare da ‘yan Najeriya wajen yaki da ‘yan bindiga da ta’addanci, yana mai jaddada kudirin cimma cinikayyar kasashen biyu da ta kai $5bn.

Abin da ya kai Tinubu Turkiyya - Bwala

A wani labarin, kun ji cewa hadimin Shugaban Najeriya, Daniel Bwala ya yi karin haske a kan dalilan da suka kai Shugaba Bola Ahmed Tinubu zuwa kasar Turkiyya.

Ya yi karin bayanin ne a lokacin da Shugaban kasa ya sake ficewa daga kasar nan jim kadan bayan ya dawo Najeriya daga Dubai, inda ya ce ba yawo kawai Tinubu ya tafi ba.

Daniel Bwala ya jaddada cewa na farko dai, gayyatar Shugaban Turkiyya ta yi a matsayinsa na tsohon Shugaban ECOWAS da kuma martabar Najeriya a idon duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng