Amana: Kusa a ADC Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Jonathan Ya Kore Shi daga Kujerar Minista

Amana: Kusa a ADC Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Jonathan Ya Kore Shi daga Kujerar Minista

  • Tsohon ministan matasa da wasanni a mulkin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fadi dalilin rasa kujerarsa bayan kamfe
  • Bolaji Abdullahi ya ce Jonathan ya cire shi daga mukamin minista saboda ya ki sukar Bukola Saraki a yakin neman zabe
  • Ya bayyana hakan ne a Abuja yayin kaddamar da littafinsa, inda ya ce an matsa masa lamba ya soki kan Saraki bayan ya koma APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Sakataren yada labarai na kasa na ADC, Bolaji Abdullahi ya fadi dalilin cire shi daga mukamin minista.

Bolaji Abdullahi ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sallame shi daga mukamin minista saboda Bukola Saraki.

Bolaji Abdullahi ya fadi dalilin rasa kujerar minista a mulkin Jonathan
Sakataren yada labaran ADC, Bolaji Abdullahi. Hoto: Bolaji Abdullahi.
Source: Twitter

Tsohon minista ya kaddamar da sabon littafi

Tsohon ministan ya bayyana hakan ne a Abuja, yayin gabatar da littafinsa mai suna 'The Loyalist: A Memoir of Service and Sacrifice', cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Ganduje ya zagi tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadi Buhari? An samu bayanai

Ya ce an cire shi ne saboda ya ki zagin tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, yayin yakin neman zabe a jihar Kwara.

Ya taba rike mukamin ministan bunkasa matasa, sannan daga bisani ministan wasanni a karkashin gwamnatin Jonathan kafin a kore shi a 2014.

Lokacin da Bukola Saraki ke gwamnan Kwara, Abdullahi ya kasance mataimaki na musamman kan sadarwa da kuma mai ba da shawara kan manufofi.

Daga baya Saraki ya nada shi kwamishinan ilimi a jihar Kwara kafin ya shiga gwamnatin tarayya a matsayin minista.

Ya ce ya ki shiga rikicin da ya barke tsakanin Saraki da Shugaba Jonathan bayan Saraki ya fice daga PDP zuwa APC.

Bolaji Abdullahi ya tuna yadda suka rabu da Jonathan
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan. Hoto: Goodluck Jonathan.
Source: Twitter

Yadda Jonathan ya so Bolaji ya zagi Saraki

A cewarsa, lokacin da Jonathan ya ziyarci Kwara a watan Maris 2014, ana sa ran zai jagoranci kamfen din PDP a jihar.

Bolaji Abdullahi ya ce dukkan masu jawabi sun hau mimbari suna sukar Saraki, kuma ana tsammanin shi ma zai bi sahu.

Ya ce duk da kasancewarsa minista daga Kwara, ya ki hawa mimbari domin sukar Saraki saboda bai ga dalilin hakan ba.

Kara karanta wannan

Jerin manyan sojoji 16 da hedkwatar tsaro 'ta gano' suna da hannu a shirin kifar da Tinubu

Wasu gwamnoni sun nemi a kore shi, suna zargin shi da zama dan leken asirin APC a cikin gwamnatin Jonathan.

Ya ce gwamnan Cross River a wancan lokaci, Liyel Imoke, ya roki shugaban kasa kada a kore shi saboda gasar cin kofin duniya.

Duk da haka, Abdullahi ya ce ya san makomarsa ta riga ta tabbata, har ya shaida wa matarsa cewa zai rasa aikinsa, cewar Punch.

Ya ce bayan kamfen din, yana London ne a wani aiki na hukuma lokacin da ya fara samun sakonnin cewa an kore shi.

Abdullahi ya jaddada cewa ba zai taba sukar kan Saraki ba, kamar yadda ba zai farmaki Jonathan idan Saraki ya bukata ba.

'Abin da ya sa Buhari ya ban minista' - Lai

Kun ji cewa Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa aminci da biyayya ne suka sanya Muhammadu Buhari ya nada shi minista har tsawon shekaru kusan takwas.

Tsohon ministan ya kaddamar da littafinsa na musamman domin girmama ranar haihuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Littafin ya bankado sirrin yadda Buhari ya kira Lai Mohammed ta waya domin sanya shi a kwamitin sauyin gwamnati a shekarar 2015.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.