Tinubu Ya Mika Sababbin Kudurorin Doka 24 ga Majalisa, An Ji abin da Suka Kunsa

Tinubu Ya Mika Sababbin Kudurorin Doka 24 ga Majalisa, An Ji abin da Suka Kunsa

  • Shugaba Bola Tinubu ya tura wa majalisa daftarin dokoki 24 domin rage yawan mambobin hukumomin lafiya da inganta ayyuka
  • Dokokin sun hada da garambawul ga asibitocin tarayya da wasu hukumomi da suka hada da NAFDAC da majalisar ungozoma
  • Shugaba Tinubu ya kuma gabatar da sabuwar dokar lafiya yayin da ya nemi majalisa ta yi gaggawar amince wa da kudurorin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya tura wa Majalisar Dattawa jerin wasu muhimman daftarin dokoki 24 da suka shafi fannin lafiya domin nazari da kuma tabbatar da su.

Wannan buƙata tana ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta yayin zaman majalisar na ranar Laraba.

Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da sababbin kudurorin lafiya 24 ga majalisar dattawa
Shugaba Bola Tinubu ya na jawabi gaban majalisar dokoki ta kasa a Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa waɗannan kudurori sun biyo bayan bincike na tsanaki da babban lauyan gwamnati da kuma ministan lafiya suka gudanar, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Lokuta 3 da aka ga Shugaba Tinubu ya yi tuntube ya fadi a wajen taro

Manufar sauya dokokin fannin lafiyar

Babban dalilin gabatar da waɗannan kudurorin dokokin shi ne rage yawan mambobin hukumomin lafiya waɗanda suka yi yawa da kuma rage kashe kuɗaɗe ba gaira-ba-dalili.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa matakin zai taimaka wajen inganta yadda asibitoci da hukumomin lafiya suke gudanar da ayyukansu da kuma bayar da sabis ga jama'a.

Ya nuna cewa sauye-sauyen za su shafi manyan asibitocin koyarwa na ƙasa, asibitoci na musamman, da kuma hukumomin da ke lura da kwararrun ma'aikatan lafiya.

Hukumomin da garambawul ɗin zai shafa

Wasu daga cikin hukumomin da waɗannan sababbin dokoki za su shafa sun haɗa da Asibitin Mata da Yara na Ƙasa da kuma dukkan manyan asibitocin tarayya (FMCs).

Haka kuma, Premium Times ta rahoto cewa garambawul ɗin ya shafi:

  • Hukumar kula da asibitocin ƙasusuwa (OHMB).
  • Cibiyoyin kula da idanu da kuma kunne na ƙasa (NEECC).
  • Majalisar ungozoma da ma'aikatan jinya ta Najeriya (NMC).
  • Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC).
  • Hukumar adana jini ta ƙasa (NBSA).

Kara karanta wannan

An gano jiha 1 da Tinubu zai iya amincewa a kirkira a Najeriya

Tinubu ya ce yana fatan majalisar dattawa za ta gaggauta amincewa da sababbin kudurorin.
Shugaba Bola Tinubu a Majalisar tarayya a Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Sababbin daftarin dokoki na musamman

Baya ga gyaran tsofaffin dokoki, Shugaba Tinubu ya kuma gabatar da wasu sababbin daftarin dokoki guda biyu na shekarar 2025 domin ci gaban fannin.

Waɗannan sun haɗa da dokar rajistar jami'an adana bayanai da lafiyar zamani ta yanar gizo (Digital Health Bill) da kuma dokar kafa kwalejin tarayya ta magungunan gargajiya.

Bayan karanta wasiƙar, Sanata Akpabio ya tura dukkan kudurorin 24 zuwa kwamitin majalisar kan harkokin kasuwanci domin gudanar da sauran ayyukan majalisa a kansu.

Shugaban ƙasar ya nuna kwarin gwiwa cewa majalisar za ta duba waɗannan dokoki cikin hanzari domin amfanin al'ummar Najeriya da kuma ƙarfafa tsarin lafiya.

Tinubu zai kashe kudi a fannin lafiya

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 na Naira tiriliyan 58.18 a zaman haɗin gwiwa na Majalisar Ƙasa.

A fannin lafiya, Tinubu ya ware N2.48tr, kusan 6% na kasafin, da nufin kara yawan ababen more rayuwar lafiya, faɗaɗa samun kulawa a manyan asibitoci, da rage yawan cututtuka a ƙasar.

Tinubu ya kuma bayyana wata yarjejeniya da Amurka, wacce ta samar da fiye da Dala miliyan 500 a matsayin tallafin kuɗi don ayyukan lafiya na musamman a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com