Ministan Buhari Ya Sha Alwashin Kafa Shari’ar Musulunci idan Ya Zama Gwamna
- Tsohon ministan sadarwa a mulkin Muhammadu Buhari ya yi magana game da kafa shari'ar Musulunci idan ya zama gwamna
- Adebayo Shittu ya ce zai kafa dokar Shari’a a Oyo idan jama’a suka buƙaci hakan bayan ya zama gwamna a 2027
- Kalaman Shittu sun sake tayar da ce-ce-ku-ce kan shirin kafa kotunan Shari’a a jihohin Kudu maso Yamma, musamman bayan rikicin Oyo a 2024
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibaban, Oyo - Tsohon Ministan Sadarwa a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, Adebayo Shittu, ya fadi abin da zai yi idan ya zama gwamna a Oyo.
Shittu ya ce idan aka zaɓe shi gwamnan jihar, zai aiwatar da dokar Shari’a matuƙar jama’ar jihar suka buƙaci hakan.

Source: Twitter
Tsohon minista ya magantu kan shari'ar Musulunci
Shittu ya bayyana haka ne yayin wata hira a shirin “Naija Unfiltered”, wani shahararren shiri da kamfanin Symfoni ya shirya wanda TheCable ta bibiya.
A yayin hirar, mai gabatar da shirin ya nemi Shittu ya yi tsokaci kan yunkurin wasu masu ruwa da tsaki na kafa dokar Shari’a a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.
Da yake martani, Shittu ya tambaye shi yadda kafa dokar Shari’a a Kudu maso Yamma zai cutar da shi a matsayinsa na Kirista.
Shittu ya ce:
“Ina tambayarka, ta yaya dokar Shari’a, idan aka kafa ta, za ta shafe ka a matsayin Kirista? Ta yaya za ta cutar da kai?”

Source: Facebook
Tsohon minista ya kare shari'ar Musulunci
Sai dai mai hira da shi ya ce a wasu jihohin Arewa, ‘yan Hisbah suna take haƙƙin bil’adama a yayin aiwatar da dokar Shari’ar Musulunci.
Da yake martani, Shittu ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi ‘yancin addini, yana mai zargin masu adawa da Shari’a da rashin haƙuri da addini.
Ya ce:
“Kundin tsarin mulki ya tabbatar da ‘yancin addini. Abin da kuke yi rashin haƙuri ne da addini. Kuna da tsananin rashin jurewa a addini.”
Da aka tambaye shi ko zai kafa dokar Shari’a idan ya zama gwamnan Oyo a 2027, Shittu ya ce zai yi hakan ne idan jama’a suka buƙata, cewar PM News.
A cewarsa:
“Idan jama’a suka nema. Har ma kundin tsarin mulki ya ce duk lokacin da aka buƙaci Shari’a, ya kamata a kafa ta. Tsarin mulki ya ba da damar hakan. Ba na gudu daga gwagwarmaya.”
Shittu ya ƙara da cewa mutane da dama suna adawa da Shari’a ne saboda rashin haƙuri, yana mai jaddada cewa ba za a tilasta wa Kirista bin dokar Shari’a ba a kowace al’umma da aka aiwatar da ita.
'Jahilci ya yi yawa': Shittu ga masu sukar shari'a
A baya, kun ji cewa tsohon ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ya soki masu adawa da kafa kwamitin shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma.
A cewarsa, kwamitocin sun dade suna gudanar da shari’o’in addini a wasu jihohi ba tare da haddasa wata matsala ba.
Ya kara da cewa Musulmi suna da ’yancin gudanar da harkokinsu bisa doka ta shari'a, don haka gwamnati ba ta da ikon hana su yin hakan.
Asali: Legit.ng

