An Gano Abin da Shugaba Tinubu Ya Taka, Ya Kusa Faduwa a Kasar Turkiyya
- Fadar shugaban kasa ta yi bayanin abin da ya faru da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron maraba da aka shirya masa a Turkiyya
- Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce Tinubu ya ci tuntube ne da wani karfe, amma bai ji rauni ba
- Ya tabbatar da cewa Tinubu na cikin koshin lafiya kuma ya ci gaba da ayyukan da aka tsara masa a ziyarar aikin da ya fara a kasar Turkiyya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Fadar Shugaban Kasa ta tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya gamu da wani dan tsautsayi a ziyarar aiki da ya kai kasar Turkiyya.
Fadar ta ce Tinubu ya dan rasa daidaito na dan lokaci a ranar Talata bayan ya taka wani karfe a lokacin ziyarar aiki da yake gudanarwa a birnin Ankara, Turkiyya.

Source: Twitter
Sai dai fadar shugaban kasar ta jaddada cewa shugaban yana nan cikin koshin lafiya kuma yana ci gaba da taron da aka tsara, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Ainihin abin da ya faru da Bola Tinubu
Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Mista Bayo Onanuga, ne ya fito ya bayyana abin da ya faru, inda ya ce shugaban ya taka wani abu ne ba tare da ya yi tsammani ba, wanda ya sa ya dan yi taga-taga kamar zai fadi.
Onanuga ya ce:
“Shugaban kasa ya taka wani karfe ne, wanda hakan ya sa ya dan rasa daidaito. Wannan ba wani babban abu ba ne, sai dai wadanda ke son yin amfani da lamarin domin su yi suka.”
“Tuntube ne kawai ya yi, kuma muna kara gode wa Allah ba faduwa ya yi ba.”
Sakon fadar shugaban kasa ga 'yan Najeriya
Fadar Shugaban Kasar ta bukaci jama’a da su yi watsi da duk wani yunkuri na rura wutar labarin ko sanya tsoro, inda ta sake jaddada cewa Tinubu yana nan daram kuma yana gudanar da ayyukan da aka tsara yadda ya kamata.
A gefe guda, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan yada labarai, Mista Sunday Dare, ya bayyana a shafinsa na X cewa tuni Tinubu ya ci gaba da ayyukan gabansa.
Tinubu ya shiga ganawa da Erdogan
Ya ce shugaban ya wuce kai tsaye daga wurin faretin maraba da bako zuwa taron ganawa da aka tsara da Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, da sauran manyan jami’an kasar.
Fadar shugaban kasar ta bayyana cewa tattaunawar na da nufin karfafa dangantakar diflomasiyya da fadada hadin gwiwa a fannoni kamar tsaro da kare kai, kasuwanci da zuba jari, makamashi da ci gaban tattalin arziki.
A cewar fadar shugaban kasa, yadda ziyarar ke tafiya lami-lafiya ya nuna irin karfin alakar da ke tsakanin Najeriya da Turkiyya da kuma sabon yunkurin diflomasiyya na Shugaba Tinubu.

Source: Twitter
Dalilan da suka kai Tinubu kasar Turkiyya
A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta bayyana dalilan da suka kai Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu zuwa Turkiyya a makon nan.
Hadimin Shugaba Tinubu, Daniel Bwala ya bayyana cewa gwamnatin Turkiyya ce ta gayyaci Shugaban Najeriyan bisa wasu dalilai da za su kara inganta alakar kasashen biyu.
Ya kara da cewa ci gaban da Najeriya ke samu a bangarorin tattalin arziki, tsaro da siyasa ya kara wa ziyarar armashi, domin duniya na kallon kasar da ido na daban fiye da da.
Asali: Legit.ng

