Ta'addanci: Kotu Ta Yi Hukunci da Nnamdi ke Neman Ɗauke Shi a Gidan Yarin Sokoto

Ta'addanci: Kotu Ta Yi Hukunci da Nnamdi ke Neman Ɗauke Shi a Gidan Yarin Sokoto

  • Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi hukunci game da korafin da shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya shigar bayan daure shi a Sokoto
  • Kanu na neman a dauke shi daga gidan gyaran hali na Sokoto da aka kai shi bayan yanke masa hukuncin daurin rai da rai a karshen 2025
  • Ya ce tsare shi a Sokoto zai hana shi daukaka kara yadda ya dace, saboda nisan wurin da kuma rashin samun damar haduwa da masu taimaka masa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wata Kotun Tarayya da ke Abuja ta raba gardama bayan korafin shugaban IPOB, Nnamdi Kanu ya shigar a gabanta.

Kotun a ranar Talata 27 ga watan Janairun 2026 ta yi watsi da bukatar da Nnamdi Kanu ya shigar domin a sauya masa wurin zama daga gidan yarin Sokoto.

Kara karanta wannan

Jerin manyan sojoji 16 da hedkwatar tsaro 'ta gano' suna da hannu a shirin kifar da Tinubu

Kotu ta yi fatali da buƙatar Kanu game gidan yarin Sokoto
Shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu. Hoto: Emmanuel Kanu.
Source: Twitter

Mai shari’a James Omotosho, wanda ya yanke hukuncin, ya bayyana cewa bukatar da Kanu ya gabatar ba ta dace da ka’idojin doka ba, cewar Vanguard.

Bukatar da Nnamdi Kanu ya nema a kotu

A cikin bukatar da ya rattaba hannu da kansa, Kanu ya ce tsare shi a Sokoto zai hana shi damar daukaka kara yadda ya dace.

Ya bayyana cewa gidan yarin Sokoto yana da nisan fiye da kilomita 700 daga Abuja, inda kotun daukaka kara take.

Kanu ya ce ba shi da lauya a halin yanzu, kuma yana son daukaka kara da kansa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Ya kara da cewa shirya takardun daukaka kara na bukatar ganawa kai tsaye da ma’aikatan kotu a Abuja.

Kanu ya ce ‘yan uwansa, abokansa da masu ba shi shawara a fannin shari’a duk suna zaune ne a Abuja.

Kara karanta wannan

Dogara: Kiristan da aka ce zai maye Shettima a 2027 ya fito ya yi magana

Musabbabin neman dauke Kanu daga Sokoto

A cewarsa, ci gaba da tsare shi a Sokoto zai tauye masa hakkin daukaka kara kamar yadda sashe na 36 na kundin tsarin mulki ya tanada.

Ya bukaci kotu da ta umarci gwamnatin tarayya ko Hukumar Gyaran Hali ta kasa da su gaggauta mayar da shi kusa da Abuja.

A madadin haka, Kanu ya roki kotu da a kai shi gidajen yari na Suleja ko Keffi domin ya samu saukin daukaka kara.

An kori bukatar dauke Nnamdi Kanu daga Sokoto
Taswirar jihar Sokoto da aka kulle Nnamdi Kanu a gidan yari. Hoto: Legit.
Source: Original

Lauyan Kanu ya janye korafin da yake yi

Sai dai a zaman kotu na ranar Talata, Lauyan Kanu, Demdoo Asan ya sanar da janyewa daga shari’ar saboda sabanin da ba za a iya sasantawa ba.

Lauyan ya ce duk kokarinsa na ganin wani daga ‘yan uwan Kanu ya rantse a takarda ya ci tura, cewar Punch.

Ya kuma zargi Kanu da kokarin gaya masa yadda zai tafiyar da shari’ar, abin da ya ce bai dace ba.

Kara karanta wannan

Badakalar fansho: Abdulrasheed Maina ya shaki iskar 'yanci bayan shekaru 8 a garkame

“Asalin aikina a matsayina na jami’in kotu ba ya ba ni damar bin umarnin wanda ake karewa."

- In ji Asan.

An musanta sake zama kan shari'ar Kanu

An ji cewa rahotanni na yawo a kafafen sadarwa cewa Babbar Kotun Tarayya za ta sake duba hukuncin da aka yanke wa Nnamdi Kanu a Abuja.

Sai dai an yi bincike mai zurfi game da jita-jitar da ake yadawa cewa za a sake duba kan hukuncin da aka yankewa shugaban IPOB.

Hakan ya biyo bayan Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukunci bayan tuhumar Nnamdi Kanu da ta'addanci a Abuja a shekarar bara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.