Shugaba Tinubu Ya Yi Tuntube a Turkiyya, Ya Fadi Kasa yayin Ziyara a Kasar
- Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi tuntube ya fadi a birnin Ankara na kasar Turkiyya yayin wata ziyarar aiki
- Lamarin ya faru ne yayin da Tinubu ke tafiya tare da Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, bayan an yi masa liyafar tarba
- Majiyoyi suka ce Shugaba Tinubu ya fadi ne na dan lokaci, kuma nan take ya tashi lamarin da ya jawo maganganu a kafofin sadarwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ankara, Turkey - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi tuntube ya fadi a birnin Ankara, babban birnin kasar Turkiyya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne yayin da Shugaba Tinubu ke tafiya tare da takwaransa na Turkiyya, Shugaba Recep Tayyip Erdogan.

Source: Twitter
Daily Trust ta ce faduwar shugaban ta kasance na dan lokaci kadan, inda aka tabbatar da cewa ya ci gaba da gudanar da abin da ya kai shi daga baya.
Tinubu ya taba faduwa yayin taro a Abuja
Wannan ba shi ne karon farko ba da Shugaba Tinubu ke faduwa a yayin taro tun bayan hawansa kan karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fadi kasa yayin da yake kokarin hawa mota a yayin bikin ranar dimokuraɗiyya da aka yi a 2024.
Bola Tinubu ya fadi ne yayin da ake faretin murnar ranar dimokuraɗiyya a dandalin Eagle Square a birnin tarayya Abuja a ranar 12 ga watan Yunin 2024.
Fadar shugaban kasa ta yi bayani kan lamarin inda ta ce ba abin tashin hankali ba ne tunda shugaba kasar ya cigaba da tafiya da gudanar da taron kamar yadda aka saba.

Source: Facebook
Faduwar Tinubu a Turkiyya yayin taro
Kafin faruwar lamarin, an ce Shugaba Tinubu ya duba faretin sojoji a matsayin wani bangare na gagarumar liyafar tarba da aka shirya masa a kasar Turkiyya.
Fadar shugaban kasa ta yi magana bayan faruwar lamarin inda ta ce Tinubu ya ci gaba gudanar da abin da ya kai shi Turkiyya.
Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga rubutun hadimin Bola Tinubu kan yada labarai, Bayo Onanuga da ya wallafa a shafin X.
Onanuga ya ce bayan shugaban ya dan yi tangal-tangal na wani lokaci, ya ci gaba da ganawar diflomasiyya da kuma taron manema labarai kai tsaye bayan haka.
Onanuga ya rubuta cewa:
“Shugaban ƙasa ya ɗan yi tangal-tangal na ɗan lokaci kaɗan, amma ya ci gaba da ganawar diflomasiyya da Shugaba Recep Tayyip Erdoğan.
"Ana gudanar da taron manema labarai kai tsaye nan take bayan ganawar.”
Abin da ya kai Bola Tinubu Turkiyya
A wani labarin, Fadar Shugaban kasa ta bayyana dalilan da suka kai Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu zuwa Turkiyya a makon nan.
Hadimin Tinubu, Daniel Bwala ya bayyana cewa gwamnatin Turkiyya ce ta gayyaci Shugaban Najeriyan bisa wasu dalilai.
Ana sa ran cimma yarjejeniyoyi a fannoni da dama da suka hada da tsaro da tattalin arziki a yayin tattaunawar da suke yi a kasar.
Asali: Legit.ng

