Hadimin Shugaban Kasa: Abin da Ya Kai Bola Tinubu Turkiyya daga Dawo wa Najeriya

Hadimin Shugaban Kasa: Abin da Ya Kai Bola Tinubu Turkiyya daga Dawo wa Najeriya

  • Fadar Shugaban kasa ta bayyana dalilan da suka kai Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu zuwa Turkiyya a makon nan
  • Hadimin Tinubu, Daniel Bwala ya bayyana cewa gwamnatin Turkiyya ce ta gayyaci Shugaban Najeriyan bisa wasu dalilai
  • Ana sa ran cimma yarjejeniyoyi a fannoni da dama da suka hada da tsaro da tattalin arziki a yayin tattaunawar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Daniel Bwala, mai bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara ta musamman kan harkokin sadarwar manufofi, ya magana kan ziyarar Shugaban kasa zuwa Turkiyya.

Bwala ya yi wannan bayani ne yayin ganawarsa da manema labarai a birnin Ankara, babban birnin Turkiyya, inda ya ce wannan ziyara ta zo ne bisa gayyatar gwamnatin Turkiyya.

Kara karanta wannan

Shugaban hukumar alhazai ya hakura da gwamnatin Abba, ya yi murabus

Tinubu ya ziyarci Turkiyya domin tattauna muhimman batutuwa
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Ajuri Ngelale
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta wallafa cewa, kiran da aka yi wa Shugaba Tinubu ya samo asali ne daga matsayin da yake da shi a matsayin tsohon shugaban kungiyar ECOWAS.

Dalilin da ya kai Bola Tinubu Turkiyya

Daily Post ta wallafa cewa Bwala ya kara da cewa an yi wa Tinubu kiran domin girmamawa da mutuncin Najeriya a nahiyar Afrika.

Ya kara da cewa:

“Ba wata tafiya ce kawai ba. Gwamnatin Turkiyya ce ta gayyace mu, kuma kowa ya san shugaban Najeriya mutum ne mai tasiri a Afrika."

Ya kara da cewa ci gaban da Najeriya ke samu a bangarorin tattalin arziki, tsaro da siyasa ya kara wa ziyarar armashi, domin duniya na kallon kasar da ido na daban fiye da da.

Hadimin Shugaban kasa ya ce za a tattauna maganganu kan tsaro
Daniel Bwala da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bwala Daniels
Source: Twitter

Bwala ya ce zuwan Shugaban kasa a wannan lokaci na nuna cewa Najeriya na kokarin bude sabbin hanyoyin hadin gwiwa da kasashen da ke da karfi a duniya.

Kara karanta wannan

Dogara: Kiristan da aka ce zai maye Shettima a 2027 ya fito ya yi magana

Bwala ya bayyana cewa daga ranar da za a fara shirye-shiryen ganawa, bangarorin biyu za su tattauna muhimman fannoni kamar tsaro, tsaron kasa da kuma tattalin arziki.

Ya ce ministocin da ke kula da wadannan sassa sun raka shugaban domin saukaka tattaunawa da cimma matsaya mai amfani ga bangarorin biyu.

Najeriya da Turkiya za su tattauna tsaro

A cewarsa, Turkiyya na da kwarewa sosai a harkar tsaro da kera makamai, wanda hakan ya yi daidai da bukatun Najeriya.

Ya ce:

“A tarihi, Turkiyya ta yi fice a bangaren tsaro, kuma tana da karfin kera muhimman makamai da muke bukata."

Bwala ya kuma tunatar da irin dangantakar da kasashen biyu ke da ita tsawon shekaru, inda ‘yan kasuwa da gwamnati daga Turkiyya suka zuba jari a Najeriya.

Haka kuma ‘yan Najeriya da gwamnatin kasar sun bayar da gudunmawa ga ci gaban Turkiyya ta fannoni daban-daban.

Shugaba Bola Tinubu ya bar Najeriya

A baya, mun wallafa cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bar birnin tarayya Abuja domin zuwa ziyara ta musamman a ƙasar Turkiyya domin amsa gayyata.

Kara karanta wannan

Arewa: Matasan APC sun cire tsoro, sun fadawa Tinubu illar sauya Shettima a 2027

Jirgin Shugaban kasar ya tashi daga sashen shugaban ƙasa na filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin ƙarfe 2.05 na rana a ranar Litinin, 26 ga watan Janairun 2026.

Daga cikin manyan jami’an da suka yi wa shugaban ƙasa rakiya zuwa filin jirgin saman akwai Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma da Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng