Juyin Mulki a Najeriya: Ana Zargin Sojojin da aka Kama na cikin Mawuyacin Hali

Juyin Mulki a Najeriya: Ana Zargin Sojojin da aka Kama na cikin Mawuyacin Hali

  • Wata kungiya ta nemi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamnatin Tarayya su sake duba tsare sojojin da aka kama tun Oktoba, 2025, bisa tabarbarewar lafiyarsu
  • Rundunar sojin Najeriya ta ce an kama jami’an ne bisa karya ka’idoji da rashin da’a, yayin da rade-radi suka alakanta lamarin da zargin yunkurin juyin mulki a kasar
  • Kungiyar ta bukaci a ba su kulawar lafiya, a ba su damar tuntubar iyalansu, ko kuma a gurfanar da su gaban kotu idan akwai tuhumar da ake yu game da kama su

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Nasarawa – Wata kungiyar masu rajin kare dimokuradiyya mai suna Concerned Pro-Democratic Activists of Nigeria ta bayyana damuwa kan halin da wasu jami’an soji da aka tsare ke ciki.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Sojoji sun mika rahoto kan jami'ai 16 da ake zargi ga shugaba Tinubu

Kungiyar ta bayyana cewa lafiyar sojojin na kara tabarbarewa sakamakon tsawaita tsare su ba tare da isasshen kulawar lafiya ba.

Hafsun tsaron Najeriya Janar Oluyede Olufemi
Babban hafsun tsaron Najeriya a ofis. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa kungiyar ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamnatin Tarayya da su sake duba batun tsare jami’an sojin da aka kama tun watan Oktoba, 2025.

Shugaban kungiyar, Yusuf Musa Dauda, ya bayyana wannan matsaya ne yayin da yake ganawa da manema labarai a Lafia, inda ya ce an hana iyalan jami’an damar ganinsu ko tuntubarsu tun bayan kama su.

Bayani kan kama jami’an sojojin

A ranar 4, Oktoba, 2025, tsohon daraktan yada labaran rundunar soji, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya sanar da kama jami’an soji 16 bisa zargin karya dokokin aiki da aikata rashin da’a.

Sai dai bayan makonni, wasu rahotanni daga cikin sojoji sun alakanta kamun da zargin yunkurin juyin mulki, suna nuni da soke faretin ranar ‘yancin kai da aka yi a ranar 1, Oktoba, 2025.

Duk da haka, rundunar soji da gwamnati sun musanta wannan rade-radi, suna jaddada cewa babu shirin kifar da gwamnati da aka gano.

Kara karanta wannan

Badakalar fansho: Abdulrasheed Maina ya shaki iskar 'yanci bayan shekaru 8 a garkame

Damuwa kan sojojin da aka tsare

Dauda ya ce wasu daga cikin jami’an da aka tsare tun Oktoban 2025 na fama da rashin lafiya mai tsanani, ba tare da samun kulawar likitoci yadda ya kamata ba.

A bayanin da ya yi, ya ce hana iyalansu damar ganinsu ko jin halin da suke ciki ya kara tayar musu da hankali da fargaba sosai.

Kungiyar ta soki tsare jami’an na tsawon lokaci ba tare da gurfanar da su gaban kotu ba, tana cewa hakan bai dace da tafarkin dimokuradiyya ba.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na rattaba hannu kan takarda. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Ta jaddada cewa duk da kin amincewa da duk wani yunkuri na kifar da gwamnati ta haramtacciyar hanya, adalci da bin doka su ne ginshikin zaman lafiya.

Kungiyar ta ce idan babu shari’a a kansu, a sake su, amma idan akwai tuhuma, a gurfanar da su gaban kotu domin a bi hanyoyin doka.

Yayin da kungiyar ta yi kira ga shugaban kasa, jaridar Daily Trust ta wallafa rahoton cewa dakarun Najeriya sun ba Bola Tinubu rahoto kan zargin juyin mulki.

Kara karanta wannan

Tinubu ya soke tura tsohon gwamnan Kebbi jakada zuwa Turkiyya sa'o'i da nada shi

Tinubu ya fasa tura jakada Turkiyya

A wani labarin, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta sanar da soke tura tsohon gwamnan Kebbi, Usman Dakingari zuwa Turkiyya.

A karon farko, shugaban kasa ya amince da Dakingari zuwa kasar Turkiyya a matsayin jakada, amma jim kadan aka sanar da soke hakan.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya tabbatar da soke tura shi kasar, sai dai bai fadi dalilin daukar matakin ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng