Juyin Mulki: Sojoji Sun Mika Rahoto kan Jami'ai 16 da ake Zargi ga Shugaba Tinubu

Juyin Mulki: Sojoji Sun Mika Rahoto kan Jami'ai 16 da ake Zargi ga Shugaba Tinubu

  • Rahoton binciken sojoji kan jami’ai 16 da ake tsare da su ya isa gaban Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Binciken DIA ya gano laifuffuka, kuma ana jiran amincewar Shugaban kasa domin ɗaukar matakan da suka dace
  • Majiyoyi sun ce an tabbatar wa Shugaban kasa cewa yunkurin juyin mulki da aka yi zargin wasu sojoji sun kudiri aniya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Sojoji sun mika wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu rahoton binciken da suka gudanar kan zargin wasu sojojin kasar nan da yunkurin kifar da gwamnatinsa.

An yi bincike a kan abin da aka kira rashin ladabi da karya dokokin aiki da ake zargin wasu jami’ai 16 da ake tsare da su sun aikata.

Kara karanta wannan

Daga barin kurkuku, AbdulRasheed Maina ya fara tone tone kan Abubakar Malami

Sojoji sun yi binciken zargin shirya juyin mulki a Najeriya
Babban hafsan tsaron kasa Janar Olufemi Oluyede, Shugaban Kasa Bola Tinubu Hoto: HQ Nigerian Army/Bayo Onanuga
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wasu majiyoyi masu tushe daga bangaren tsaro da fadar shugaban kasa sun tabbatar da cewa an mika rahoton ne bayan tsawon lokaci ana aikinsa.

An kammmala bincike kan zargin juyin mulki

Wani rahoto da Sahara Reporters ta wallafa a watan Oktoban 2025 ya yi ikirarin cewa an kama jami’an, daga mukamin Kyaftin zuwa Birgediya Janar, bisa zargin shirin kifar da gwamnatin Shugaba Tinubu.

A wancan lokaci, Hedikwatar Tsaro da Fadar Shugaban Kasa sun musanta batun juyin mulki, duk da rahotannin da suka danganta lamarin da soke bikin zagayowar ranar ‘yancin kai ta 1 ga Oktoba.

Majiyoyin sun bayyana cewa sama da watanni biyu aka kwashe ana tsaurara tambayoyi da bincike mai zurfi a kan zargin, wanda hukumar leken asiri ta kasa (DIA) ta gudanar.

Rahoton sojoji ya tabbatar da shirin juyin mulki a Najeriya
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima suna addu'a Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Twitter

Wata majiya da ke da masaniya kan binciken ta shaida cewa an kammala aikin kuma an mika rahoton ga shugaban kasa, wanda shi ne Babban Kwamandan Rundunar Soji.

Kara karanta wannan

Badakalar fansho: Abdulrasheed Maina ya shaki iskar 'yanci bayan shekaru 8 a garkame

Ta ce matakin da shugaban kasa zai ɗauka ne zai ba da damar ci gaba da daukar matakai na gaba.

A cewar majiyar, jami’an da aka bincika an same su da laifi, kuma za a hukunta su daidai da ka’idojin soja da zarar shugaban kasa ya amince.

Ana dakon Tinubu kan rahoton juyin mulki

Majiyar ta ƙara da cewa har yanzu ba ta san ko za a gurfanar da su a gaban kotun soja ba, amma tabbas za su fuskanci hukunci bisa tsari na doka.

Haka kuma, wata majiya daga Fadar Shugaban Kasa ta tabbatar da cewa an yi wa shugaban kasa cikakken bayani, inda aka tabbatar da shirin juyin mulkin.

An ce Birgediya Janar ɗin da ke cikinsu an kama shi ne saboda sanin shirin amma bai kai rahoto ba.

An kuma ruwaito cewa ana binciken tsohon gwamna daga Kudancin ƙasar nan kan zargin daukar nauyin shirin.

Juyin mulki: Shawarar Tinubu ga sojoji

A baya, mun wallafa cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga rundunonin sojin Najeriya da su ci gaba da kasancewa masu tsayin daka kan ladabi, biyayya.

Kara karanta wannan

Abubakar Malami ya yi magana game da makamai da DSS ta gano a 'gidansa' na Kebbi

Shugaban ya ce rawar da sojoji ke takawa ta wuce tsaron iyakoki kawai, har da kare haɗin kan al’umma a ƙasa mai kabilu da addinai masu yawa, saboda haka akwai bukatar su tsaya a kan aiki.

Shugaba Bola Tinubu ya isar da wannan saƙo ne ta bakin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, a yayin bikin tunawa da sojoji na shekarar 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng