‘Zan ci Gaba da Kaunarsa’: Minista Ta Tuna Kaunar da Ke tsakaninta da Abdulsamad BUA
- Ministar harkokin fasaha, al’adu da tattalin arzikin kirkire-kirkire, Hannatu Musawa ta yi magana kan tsohon tsohon mijinta, Abdul Samad Rabiu
- Hannatu Musawa ta ce Abdulsamad Rabiu zai ci gaba da kasancewa “wani muhimmin bangare na zuciyarta” duk da rabuwar aurensu
- Ministar ta bayyana cewa ba ta da nadama kan auren da ta yi da shugaban BUA , tana mai cewa dangantakarsu ta koma ta yan uwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Hannatu Musawa, ministar harkokin fasaha, al’adu da tattalin arzikin kirkire-kirkire, ta magantu game da tsohon mijinta, Abdul Samad Rabiu.
Hannatu Musawa ta ce shugaban kamfanin BUA, zai ci gaba da kasancewa a zuciyarta har abada saboda alakarsu.

Source: Twitter
Minista ba ta yi nadamar auren BUA ba
Ta bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin MIC on Podcast wanda ɗan jarida Seun Okinbaloye ke gabatarwa da Imran Muhammad ya wallafa a X, wanda Legit Hausa ta bibiya.
Musawa ta ce ba ta da wata nadama kan auren da ta yi da Rabiu da kuma rabuwar aurensu daga bisani.
Ministar ta jaddada cewa tana alfahari da kanta da kuma zabin rayuwar da ta yi, tana mai cewa dangantakarta da attajirin ɗan asalin Kano ta wuce ta aure zuwa ta yan uwa.
A cewarta:
“Abdul Samad dan uwana ne. Iyalanmu sun hade wuri guda. Mun san juna sama da shekaru 30. Mu yan uwa ne kawai. Muna yawan barkwanci da juna saboda mu yan uwa ne.”
Ta kara da cewa Rabiu ya zama kamar uba, ɗan uwa, aboki kuma mai kareta, tana mai cewa hakan ba ita kaɗai ba ce ke ganin Rabiu haka, mutane da dama na ganin sa a matsayin mai taimako.
Da aka tambayeta game da aurensu na baya, Musawa ta ce har yanzu akwai soyayya da girmamawa a tsakaninsu, duk da cewa ba su ƙara zama miji da mata ba.
“Shi tsohon mijina ne, amma har yanzu dan uwa ne. Mun fito daga al’adar da idan aka hada ku, ko bayan rabuwar aure, kuna cikin rayuwar juna."
- In ji Hannatu Musawa

Source: Facebook
Minista ta tuna lamarin Allah a rayuwarta
Hannatu Musawa ta kuma bayyana cewa komai yana hannun Allah, inda ta ce wataƙila da ta ci gaba da zama matar Rabiu, da ba za ta kai matsayin da take kai a yau ba.
A ƙarshe, Musawa ta ce har yanzu tana cike da kauna a zuciyarta ga attajirin ɗan kasuwar, tana mai cewa:
“Samad zai ci gaba da kasancewa a zuciyata. Ba shakka yana daga cikin manya a rayuwata. Zan ci gaba da kaunarsa har tsawon rayuwata.”
Minista ta yi gargadi kan sauya Shettima
Mun ba ku labarin cewa ministar harkokin fasaha, al’adu da tattalin arzikin kirkire-kirkire, Hannatu Musawa ta gargadi APC kan sauya tikitin Tinubu–Shettima kafin 2027.
Hannatu Musawa ta ce sauyin zai iya jawo asarar kuri’u a Arewacin Najeriya kuma akwai barazanar cewa ba za a kai labari ba.
Ta bayyana cewa siyasar Arewa tana da tsari da tunani na musamman, kuma dole a nazarce shi da kyau kafin yanke hukunci.
Asali: Legit.ng

