Shiri Ya Baci: Amarya Ta Hallaka Mijinta har Lahira a Jigawa

Shiri Ya Baci: Amarya Ta Hallaka Mijinta har Lahira a Jigawa

  • Ana zargin wata sabuwar amarya da yin sanadiyyar rasuwar mijinta har lahira bayan ta dafa masa abinci ta ba shi ya ci
  • Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta cafke amaryar bisa zargin raba mijinta da lahira bayan da aka tabbatar da rasuwarsa
  • Amaryar ta amsa ta aika an sayo mata wani sinadari da ta sanya a abincin mijin, wanda ta ce dama iyayenta ne suka aura mata shi dole

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Jigawa - Rundunar ’yan sandan jihar Jigawa ta kama wata sabuwar amarya a kauyen Gauza da ke karamar hukumar Jahun.

Rundunar 'yan sandan ta cafke amaryar ne bisa zargin sanyawa mijinta guba a abinci wanda hakan ya yi sanadiyyar rasuwarsa.

Amarya ta sanyawa mijinta guba a Jigawa
Taswirar jihar Jigawa, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta ce rahoton da jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Shiisu Lawan Adam Anipr, ya fitar ya ce lamarin ya faru ne ranar Alhamis, 23 ga Janairu, 2026, da misalin karfe 5:00 na yamma.

Kara karanta wannan

Daga barin kurkuku, AbdulRasheed Maina ya fara tone tone kan Abubakar Malami

Amarya ta sa guba a abincin mijinta

Ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa marigayin ya ci abincin da matarsa ta dafa masa a gidansu, kafin daga bisani ya kamu da matsananciyar rashin lafiya ba zato ba tsammani.

Nan take aka garzaya da shi zuwa wani asibiti da ke kusa domin yi masa magani, amma aka tabbatar da mutuwarsa yayin da ake kokarin ceto ransa.

Biyo bayan faruwar lamarin, jami’an bincike daga ofishin ’yan sanda na shiyyar Jahun suka fara gudanar da bincike, wanda ya kai ga cafke matar a matsayin babbar wadda ake zargi.

Me amarya ta ce kan zargin kashe mijinta?

A yayin tambayarta, wadda ake zargin ta amsa cewa ta zuba maganin bera a cikin abincin mijinta.

Haka kuma, ta amince cewa ita ce ta aika wani dan uwanta ya je sayen gubar da aka yi amfani da ita.

Rahoton jaridar The Punch ya nuna cewa wadda ake zargin ta shaida wa masu bincike cewa iyayenta ne suka tilasta mata auren, lamarin da ta ce ya yi tasiri a kan abin da ta aikata.

Kara karanta wannan

Badakalar fansho: Abdulrasheed Maina ya shaki iskar 'yanci bayan shekaru 8 a garkame

'Yan sanda sun dukufa aiki

Kwamishinan ’yan sandan jihar ya bayar da umarnin mika lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) da ke Dutse domin gudanar da cikakken bincike.

'Yan sanda sun cafke amarya a Jigawa kan zargin kashe mijinta
Jami'an 'yan sandan Najeriya a cikin motar aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Bayan kammala binciken, za a gurfanar da wadda ake zargi a gaban kotu.

A halin da ake ciki, rundunar ’yan sandan ta yi kira ga al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka da oda, su kuma rika neman hanyoyin shari’a wajen warware matsalolin iyali da na aure.

Rundunar ta gargadi jama’a da kada su dauki doka a hannunsu, tana mai jaddada cewa irin hakan na yawan haifar da dana sani daga baya.

Amarya ta yi garkuwa da kanta

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata Amarya ƴar shekara 29 ta ƙirƙiri labarin sace kanta don karɓar kuɗin fansa da za ta biya bashin Naira miliyan 3.6.

Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta cafke amaryar mai suna, Merit Eleh, tare da wasu da ake zargin sun taimaka mata wajen shirya rashin gaskiyar.

Bayan cafke waɗanda ake zargi, ɗaya daga cikinsu ya amsa cewa ba a yi garkuwa da matar ba, illa dai sun haɗa baki ne da ita don karɓar kuɗin fansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng