Wata 10 da Rasuwar Malam Idris, Maganar Rabon Gado Ta Dawo, an Gargadi Mutane
- Iyalan marigayi Sheikh Abdulaziz Dutsen Tanshi sun sake gargadin mutanen da suka sayi filaye daga hannun shehin malamin a Bauchi
- Sun ce an riga an raba dukiyoyin marigayin ga magada, sai gonar da ke hanyar Bauchi–Gombe da har yanzu ake jiran masu filaye su fito
- Iyalan sun jaddada cewa wannan ita ce sanarwa ta ƙarshe, inda suka ce duk wanda bai zo da takardu ba kafin karshen watan Janairu zai rasa filinsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Iyalan marigayi Sheikh Abdulaziz Dutsen Tanshi sun sake gargadin mutane da suka sayi filaye daga hannun shehin malamin.
An tabbatar da cewa yau kimanin watanni 10 kenan da rasuwar malamin wanda tuni aka riga aka raba gadonsa.

Source: Twitter
Yaushe aka raba gadon dukiyar Dutsen Tanshi?
Wannan sanarwa ta fito ne daga shafin da ke yada karatuttukan malamin (Dutsen Tanshi Majlis Bauchi) da aka wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan
Badakalar fansho: Abdulrasheed Maina ya shaki iskar 'yanci bayan shekaru 8 a garkame
Sanarwar ta shawarci al'ummar Musulmi da suka sayi filaye a wurin marigayin su gaggauta bayyana kansu domin cire musu hakkinsu.
An tabbatar da cewa na raba gado ga iyalan marigayi Dutsen Tanshi tun watanni biyu da suka wuce bayan rasuwarsa.
Sai dai duk da haka akwai bangaren filayensa da ke hanyar Gombe da ba a kai ga kammala tantancewa ba saboda hakkin jama'a a ciki.
Sanarwar ta ce:
"Yau kimanin wata 10 kenan da rasuwar Sheikh Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, wata biyu kenan da aka raba gadon dukiyarsa ga magadansa.
"Abin da ya rage ba a raba ba ita ce gonarsa da ke daura da 'MobileBarrack' da ke hanyar Bauchi zuwa Gombe.
"Dalili kuwa shi ne saboda a samu fitar wa wadanda suka sayi filaye a wurin marigayin kuma kodai ba a fitar masu ba ko kuma sun manta wuraren."

Source: Facebook
Dutsen Tanshi: Wa'adin da aka ba mutane
An bukaci wadanda ke da hakki a wurin su yi gaggawar bayyana da takardu domin cire musu hakkinsu duk da cewa an yi ta sanar da hakan a baya.
Sanarwar ta ce mutane da dama sun amsa kiran da aka yi ta yi a baya amma duk da haka akwai wadanda ake zargin ba su zo ba.
"Wannan ita ce sanarwa ta karshe ga duk wanda bai samu zuwa ba ya hanzarta ya zo da takardu domin samun hakkinsa.
"Wannan sanarwar za ta daina aiki zuwa ranar 31 ga watan Janairun 2026, da zarar wannan ranar ta shige za a rabawa magada gonar."
- Cewar sanarwar
Abubuwan da Dutsen Tanshi ya gina a rayuwa
An ji cewa malamin addini Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya rasu a daren Alhamis, 3 ga Afrilun 2025, lamarin da ya girgiza al’umma da dama.
Dutsen Tanshi Majlis Bauchi, shafin da ke kula da karatuttukan marigayin ya sanar da cewa za a gundanar da jana’izarsa a safiyar washe garin Juma'a.
Wannan rahoto na dauke da muhimman abubuwa 7 da marigayi Idris Abdullaziz Dutsen Tanshi ya gina rayuwarsa a kan su, ciki har da riko da tauhidi.
Asali: Legit.ng
