Bidiyon Kwankwaso, Gawuna yayin Ziyara ga Haruna Bashir da Aka Hallaka Iyalinsa
- Manyan 'yan siyasa ciki har da Nasiru Gawuna da jagoran Kwankwasiyya sun ziyarci gidan Malam Haruna Bashir a Kano
- Yan siyasar sun kai ziyarar domin jajantawa mutumin game da iftila'in da ya faru da shi na kisan gilla da aka yi wa iyalinsa a jihar
- Rundunar ’yan sanda ta kama waɗanda ake zargi da aikata kisan, ciki har da Umar Auwal, ɗan uwan matar da aka kashe
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Ana ci gaba da tururuwa zuwa gidan Maam Haruna Bashir domin taya shi jaje kan iftala'in da ya faru da shi a makon jiya na hallaka iyalinsa.
Tsohon dan takarar gwamnan Kano karkashin APC, Nasiru Gawuna da Jagoran Kwankwasiyya sun ziyarci gidan Malam Haruna Bashir.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani faifan bidiyoyi mabambanta da Freedom Radio ta wallafa a Facebook a yau Juma'a 23 ga watan Janairun 2026.
Yadda aka hallaka mata, yaranta 6
Haruna Bashir dai shi ne wanda wasu matasa suka shiga gidansa da tsakar rana suka yi wa iyalansa kisan gilla wanda ya jawo martani daga sassan kasa baki daya.
Yayin harin, an hallaka matarsa da yaranta guda shida a wani irin mummunan yanayi da ya daga hankulan al'umma jihar da kasa baki daya.
Tuni rundunar yan sanda ta yi nasarar cafke wadanda ake zargi da aikata laifin ciki har da dan uwan matar da ake kira Umar Auwal.
Umar ya tabbatar da cewa shi ya aikata laifin yayin tuhumarsa da yan sanda suka yi bayan nasarar kama shi da aka yi.
Har yanzu dai ana ci gaba da bincike yayin da rundunar ke kwantar wa al'umma hankali da gargadinsu kan yada jita-jita.

Source: Facebook
Ziyarar jagora Kwankwaso gidan Haruna Bashir
A cikin bidiyon, Jagoran siyasar Kwankwasiyya ma ba a bar shi a baya ba domin ya ziyarci unguwar da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan
Binciken makamai: Malami na tsaka mai wuya a hannun hukumar DSS, ya fito ya yi magana
An gano dandazon jama'a na tafe yayin da Kwankwaso ya shigo unguwar yayin da ake ci gaba da yi masa kirari na siyasa duba da gudunmawarsa a jihar.
Gawuna ya ziyarci gidan Malam Haruna Bashir
A bidiyon da Hassan Gawuna Ibrahim ya wallafa, an gano Nasiru Gawuna ya dura a gidan tare da yin jaje da ta'aziyya da Malam Bashir da aka hallaka masa mata da yara shida.
Gawuna ya nuna jimaminsa matuka da kuma yin addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasa ransu da kuma ba shi hakurin juriya.
Abba Kabir ya ziyarci gidan Haruna Bashir
A baya, kun ji cewa Gwaman Abba Kabir na jihar Kano ya kai ziyara gidan Malam Haruna Bashir domin yi masa ta'aziyya kan abin da ya faru.
Gwamna Abba ya yi alkawarin biya wa Haruna Bashir, mutumin da aka kaahe matarsa da yaransa kudin aikin Hajji da Umrah domin samun natsuwa.
Abba ya bayyana haka ne a lokacin da ya je ta'aziyya ga mutumin bisa wannan jarabawa da ya tsinci kansa a ciki a unguwar Dorayi.
Asali: Legit.ng
