Malami Ya Dauko da Girma, Ya Hango Masu Daukar Nauyin Ta'addanci a Kusa da Shugaba Tinubu

Malami Ya Dauko da Girma, Ya Hango Masu Daukar Nauyin Ta'addanci a Kusa da Shugaba Tinubu

  • Primate Elijah Ayodele ya yi zargin cewa akwai masu hannu a daukar nauyin ta'addanci a cikin jami'an gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Fitaccen malamin cocin ya gargadi gwamnatin tarayya cewa ya kamata ta tashi tsaye domin kawo karshen duk wata barazana ta tsaro
  • Ayodele, wanda ya shahara wajen hasashen abin da zai faru, ya bayyana ‘yan ta’adda a matsayin makiyan kasa masu taurin kai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja, Nigeria - Babban limamin cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya zargi wasu manyan jami'ai a gwamnatin tarayya da hannu a daukar nauyin ta'addanci.

Ayodele ya yi zargin cewa mutanen da suke daukar nauyin ta’addanci a Najeriya suna cikin manyan jami’an soja da kuma masu fada a ji a gwamnati, har ma da wadanda ke kusa da Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Daga barin kurkuku, AbdulRasheed Maina ya fara tone tone kan Abubakar Malami

PPrimate Ayodele.
Babban limamim coci a Najeriya, Promate Elijah Ayodele yana wa'azi Hoto: Primate Elijah Ayodele
Source: Twitter

Malamin coci ya gargadi gwamnatin Tinubu

Malamin addinin ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Osho Oluwatosin, ya sanya wa hannu, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.

Primate Ayodele ya gargadi gwamnati cewa rashin tsaro na iya zama babban barazana ga mulkin yanzu idan ba a dauki kwakkwaran mataki ba.

Ya bayyana cewa yaki da ta’addanci na bukatar hadin kan kowa, inda ya jaddada cewa matsalar rashin tsaro za ta ci gaba da yaduwa sai dai idan gwamnatin tarayya ta hada karfi da mazauna yankuna baki daya.

Wadanda malamin ke zargi a gwamnati

A cewarsa, wadanda ke marawa ‘yan ta’adda baya ba baki ba ne; manyan mutane ne da ke aiki a cikin tsarin gudanarwa a gwamnati.

"Akwai mutanen da ke ba su kudi a cikin sojoji da kuma kusa da madafun iko. Wasu daga cikinsu suna cikin masu yanke shawara tare da Shugaban Kasa, suna nan a ko’ina.

Kara karanta wannan

Bello Turji ya firgita a cikin daji, yana gudun neman tsira zuwa wurare

Primate Ayodele ya bukaci gwamnati da ta tashi tsaye wajen magance rashin tsaro, yana mai gargadin cewa gazawa wajen yin hakan zai iya cutar da kasar da kuma makomar siyasar Shugaba Tinubu.

"Dole ne gwamnati ta nuna da gaske take a wannan yakin. Kowa dole ne ya shiga ciki, tun daga matakin kasa har zuwa matakin tarayya.
"Idan wannan gwamnatin ta gaza, to saboda rashin tsaro ne, kamar yadda na yi gargadi a baya. Kada a raina wannan lamarin," in ji shi.
Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Ayodele ya yabawa sojojin Najeriya

Yayin da yake yaba wa sojojin Najeriya kan kokarinsu, malamin ya bayyana ‘yan ta’adda a matsayin makiya kasa masu taurin kai, inda ya yi zargin cewa suna kulla makircin kai hare-hare don gurgunta gwamnatin.

"Sojojin Najeriya suna yi kokari, amma wadannan 'yan ta'addan suna da taurin kai kuma sun kuduri niyyar ganin bayan gwamnati. Suna son tsananta hare-hare, ciki har da kai hari kan Kiristoci, domin bata sunan wannan gwamnatin," in ji shi.

Malamin coci ya ba Tinubu mafita

A wani rahoton, kun ji cewa Primate Elijah Babatunde Ayodele ya sanar da Mai girma Bola Tinubu abin da zai kawo karshen matsalar wadda aka dade ana fama da ita.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya bada umarni game da kisan matar aure da yaranta 6 a Kano

Malamin cocin ya gargadi Tinubu cewa matsalar tsaro a Najeriya ba za ta kare ba, muddin gwamnati ba ta ɗauki matakin kama masu karfafawa da ɗaukar nauyin ta’addanci ba.

Ya ce duk wani ƙoƙari da ake yi yanzu wajen magance rashin tsaro ba zai haifar da da mai ido ba, idan har ba a gano tare da gurfanar da masu ɗaukar nauyin ta’addanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262