Hamza Al Mustapha Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Manyan Najeriya ke Zarginsa da Kashe Kudirat

Hamza Al Mustapha Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Manyan Najeriya ke Zarginsa da Kashe Kudirat

  • Manjo Hamza Al-Mustapha, tsohon dogarin Shugaban kasa ya bayyana dalilan da ya sa aka rika zarginsa da kashe Kudirat Abiola
  • Ya bayyana haka ne bayan kotu ta wanke shi daga dukkanin zargin da aka yi masa na hannu a kitsa kisan a shariar shekaru 30
  • Al-Mustapha ya ce tsayuwarsa wajen kare tsohon Shugaban kasa Sani Abacha ta janyo masa bakin jini a ciki da wajen Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon dogarin shugaban kasa, Manjo Hamza Al-Mustapha, ya bayyana cewa mutane da dama sun saka shi a gaba saboda ya yi tsayin daka wajen hana kashe tsohon Shugaban Kasa, marigayi Sani Abacha.

Ya bayyana hakan ne bayan Kotun Koli ta Najeriya ta wanke shi daga zargin cewa shi ne ya kashe Kudirat Abiola, bayan kusan shekaru 30 ana jan shari’a a kotuna daban-daban.

Kara karanta wannan

Daga barin kurkuku, AbdulRasheed Maina ya fara tone tone kan Abubakar Malami

Hamza Al-Mustapha ya bayyana dalilin makala masa zargin kisan Kudirat Abiola
Tsohon dogarin Shugaban kasa, Hamza Al-Mustapha, Marigayi Janar Sani Abacha Hoto: Hamza Al-Mustapha
Source: Facebook

A wata hira da ya yi da DCL Hausa, Hamza Al-Mustapha ya gode wa Allah SWT bisa yadda Ya wanke shi daga zargin da aka dade ana masa.

Hamza Al-Mustapha ya gode wa Allah SWT

Manjo Hamza Al-Mustapha ya bayyana hukuncin kotun a matsayin nasara ga gaskiya da adalci, yana mai cewa hukuncin ya tabbatar da gaskiyarsa.

Manjo Al-Mustapha mai ritaya ya ce, duk da irin radadin da ya ce ya sha a tsawon shekarun da aka tsare shi, ya yafe wa mutanen da suka zalunce shi.

Hamza Al-Mustapha ya bayyana cewa a tsawon shekarun da ya kwashe a tsare, ya hadu da mutane iri-iri, musamman wadanda suka azabtar da shi, ‘yan uwansa da makusantansa.

Ya ce:

“Godiya ga Allah da Ya bar mu da ranmu har muka ga haka, da kuma idon wadansu wadanda suka kitsa hakan. To mun gode wa Allah. Su Allah Ya shirye su su daina. Allah Kuma Ya zaunar da kasar mu lafiya.”

Kara karanta wannan

Badakalar fansho: Abdulrasheed Maina ya shaki iskar 'yanci bayan shekaru 8 a garkame

Wadanda za a zarga da kisan Kudirat

Hamza Al-Mustapha ya kara da cewa a cikin shekaru 15 da aka tsare shi, an azabtar da shi ta hanyoyi daban-daban, ciki har da kona shi da wuta da duka.

Hamza Al-Mustapha ya yafe wa mutanen da suka azabtar da shi
Tsohon dogarin Shugaban kasa, Hamza Al-Mustapha Hoto: Hamza Al-Mustapha
Source: Facebook

Ya ce an kuma tsare kaninsa sau da dama ba tare da dalili ba, tare da azabtar da wasu daga cikin makusantansa.

Hamza Al-Mustapha ya kara da cewa makusantan gwamnati ne ya kamata a mayar da hankali a kansu wajen binciken kisan Kudirat Abiola a wancan lokaci.

A kalamansa:

“Ni a gwamnatance, ina tare da Shugaban kasa ne. Akwai ‘yan sanda, akwai ‘yan sandan ciki, akwai masu bincike, su za a zarga.”

Ya kara da cewa:

“Ni dai na san bakin ciki da ake da ni shi ne na hana su su buge marigayi shugaban kasa. Wannan shi ne magana tsantsa a fili. Mutane da yawa sun tsane ni, mu kuma babu yadda za a yi mu dauki amanar da aka ba mu mu ci wannan amanar daga inda muke, sai dai idan ba mu da rai.”

Kara karanta wannan

Martanin Hamza Al Mustapha bayan hukuncin kotu kan zargin kisan Kudirat Abiola

Kotun koli ta wanke Hamza Al-Mustapha

A baya, mun wallafa cewa Kotun Koli ta Najeriya ta yi watsi da bukatar da aka nemi sake gurfanar da tsohon babban dogarin shugaban kasa, Manjo Hamza Al-Mustapha.

Kotun ta ki amincewa da bukatar sake dawo da Hamza Al-Mustapha gaban kuliya domin ci gaba da shari’ar da ake tuhumarsa da hannu a kisan Kudirat Abiola.

Kotun Koli ta yanke wannan hukunci ne bayan nazarin karar da aka shigar, inda ta tabbatar da cewa babu dalilin doka da zai sa a sake bude shari’ar da aka riga aka yanke hukunci a kanta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng