Martanin Hamza Al Mustapha bayan Hukuncin Kotu kan Zargin Kisan Kudirat Abiola
- Tsohon dogarin Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya, ya ce ya yi farin ciki bayan kotun koli ta wanke shi
- Al-Mustapha ya ce an yi yunkurin kashe shi lokuta da dama a cikin shekaru 15 da ya kwashe a tsare saboda zarge-zarge
- Ya ce ba zai nemi diyya ba duk da azabar da ya sha, tsohon sojan ya yi kira ga ’yan Najeriya su hada kai su gina kasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon dogarin marigayi shugaban kasa, Sani Abacha ya yi magana bayan kotun koli ta wanke shi kan zargin kisan Kudirat Abiola.
Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya bayyana farin cikinsa game da hukuncin kotu inda ya ce bai rike kowa a zuciya ba.

Source: Facebook
Hamza Al-Mustapha ya tuna bala'in da ya shiga
Hakan na cikin wata hira da aka yi da shi wanda jaridar yanar gizo ta DCL Hausa ta wallafa a shafin Facebook a yau Juma'a 23 ga watan Janairun 2026.
Yayin hirar, Al-Mustapha ya tuna azabar da ya sha tsawon shekaru ba tare da kama shi da laifin komai ba.
Ya ce:
"Ni dai na san bakin cikin da suke da ni shi ne na hana su buge marigayi shugaban kasa, wannan shi ne magana, mutane da yawa sun tsani shi, mu kuma ba za mu bari a ci amana ba.
"Na fada maka, fushi da ake yi da mu daga manyan Najeriya da kasashen waje shi ne mun tsaya ka da a kawar da gwamnati, na yi bakin jini a idon mutane sosai.
"An yi shirin a kashe ni har sau 18 a cikin shekaru 15 da suka rike ni, Allah ne ya sa za mu kawo yanzu da rai."

Source: Facebook
Jerin kalubalen da Al-Mustapha ya fuskanta
Al-Mustapha ya kuma bayyana irin sharrukan da aka yi ta masa da kage duk domin a samu hanyar da za a ga bayansa.

Kara karanta wannan
Kotun kolin Najeriya ta kunyata wadanda suka nemi a dawo da shari'ar Hamza Al Mustapha
Tsohon sojan ya ce an taba rufe cikin karkashin kasa ban da kona leda da wuta da aka rika yi a jikinsa, kan laifuffukan da yake cewa bai aikata ba.
Ya kuma yi magana game da neman diyya bayan azabar da aka yi masa inda tsohon dogarin ya ce babu abin da zai nema na diyya.
"Ai da ba wannan laifi ba ne ake tuhuma ta, an ce dukiyoyin Gaddafi ne, an ce dukiyoyin marigayi shugaban kasa aka dawo aka ce juyin mulki na ke shiryawa.
"Ni ba na neman diyya, abin da ya sa suka tsorata suke ta azabtar da ni, ni ina duba abu daga wurin Ubangiji ne, Allah muka saka a gaba."
- Hamza Al-Mustapha
Hamza Al-Mustapha ya ce tun farko ba shi da laifi a zarginsa da ake yi bayan tambayar dalilin rashin halartar zaman kotun koli da ta wanke shi.
Ya shawarci yan Najeriya ba tare da bambancin addini ko kabianci ba a hadu a gina Najeriya domin inganta yan kasar.
Al-Mustapha ya gano kuskure a hadakar ADC
A baya, kun ji cewa tsohon dogarin Sani Abacha, Hamza Al-Mustapha, ya ce ba zai shiga hadakar siyasa ba saboda rashin gaskiya da ruɗani.

Kara karanta wannan
Binciken makamai: Malami na tsaka mai wuya a hannun hukumar DSS, ya fito ya yi magana
Ya ce wasu daga cikin 'yan hadakar suna yaudarar juna, suna kokarin kawar da abokan tafiyarsu domin su zama jagorori su kaɗai.
Al-Mustapha ya zargi wasu daga cikin shugabannin hadakar da kasancewa cikin masu mulkin baya da suka jefa Najeriya cikin kunci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
