An Wallafa Bidiyon Kurkukun da Boko Haram ke Daure Mutane a Daji

An Wallafa Bidiyon Kurkukun da Boko Haram ke Daure Mutane a Daji

  • Dakarun Operation Hadin Kai sun gano tare da rushe wuraren tsare fursunoni da Boko Haram ke amfani da su a yankin Timbuktu Triangle na Jihar Borno
  • An gano wuraren ne a sansanin ‘yan ta’adda na Guraba yayin da sojoji ke ci gaba da kai hare-haren tsabtace yankin daga masu tayar da kayar baya
  • Rahotanni sun nuna cewa wannan nasara ta ƙara karya farfagandar ‘yan ta’adda tare da nuna ƙarfafa ikon dakarun Najeriya a yankin Arewa maso Gabas

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno – Dakarun Operation Hadin Kai sun samu gagarumar nasara bayan sun rushe wuraren tsare fursunoni har guda uku da kungiyar Boko Haram ke amfani da su a yankin da ake kira Timbuktu Triangle a Jihar Borno.

Kara karanta wannan

Sojoji sun shiga har dajin Sambisa sun yi wa 'Yan Boko Haram jina jina

Wannan nasarar ta zo ne yayin da sojojin ke ci gaba da kutsawa cikin yankin da aka dade ana dauka a matsayin mafakar ‘yan ta’adda.

Kurkukun da Boko Haram a cikin daji
Sojoji na rusa kurkukun da Boko Haram ta yi a daji. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa an gano wadannan wuraren tsare fursunonin ne a sansanin Guraba, yayin da ake gudanar da ayyukan tsabtace yankin domin kawar da barazanar Boko Haram.

An gano kurkukun 'yan Boko Haram

Majiyar ta bayyana cewa kowanne daga cikin wuraren tsare fursunonin da aka gano na dauke da dakuna uku dabam-dabam, alamar yadda ‘yan ta’addan ke tsare mutane da dama a lokaci guda.

An ce rushe wuraren ya nuna irin zaluncin da Boko Haram ke aikatawa a yankunan da suke mamaye, tare da fallasa yadda suke amfani da fursunoni wajen cimma manufarsu.

Sojojin sun kuma lalata kayan aiki da wasu muhimman abubuwan more rayuwa da ke taimaka wa ‘yan ta’addan gudanar da ayyukansu a sansanin Guraba.

Sojoji sun fatattaki Boko Haram a daji

Majiyar ta ce dakarun sun samu gagarumin ci gaba bayan sun tsabtace tare da mamaye muhimman wurare da dama a Timbuktu Triangle.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kutsa babban sansanin Boko Haram, sun bankado kabarin 'yan ta'adda

Daga cikin wuraren da sojojin suka samu ikon mallaka har da Tergejeri, Chiralia da kuma yankunan Ajigin da Abirma, inda ‘yan ta’adda ke yawan fakewa a baya.

Sojojin Najeriya a bakin fama
Yadda sojoji ke kutsawa daji a yaki da 'yan ta'adda. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

A yayin wadannan hare-hare, dakarun sun yi artabu da ‘yan ta’addan da ke kokarin tserewa, inda aka yi amfani da makamai wajen hallaka wasu daga cikinsu.

Za a cigaba da yakar Boko Haram

Majiyar ta kara da cewa dakarun na ci gaba da matsa lamba kan ‘yan ta’addan da ke gudu, ba tare da basu damar sake shirya kai hare-hare ba.

Sojojin Operation Hadin Kai sun jaddada kudirinsu na kare fararen hula, rushe cibiyoyin ‘yan ta’adda da kuma dawo da dorewar zaman lafiya da tsaro a yankin Arewa maso Gabas.

Sojoji sun farmaki dajin Sambisa

A wani labarin, mun kawo muku cewa sojojin Najeriya sun kai gagarumin hari yankunan da 'yan Boko Haram ke buya a dajin Sambisa.

Farmakin ya jawo nasarar kashe wasu daga cikin mayakan Boko Haram ciki har da dan ta'addan da ake kira 'Ba Sulhu' da mai suna Ubaida.

Dakarun Najeriya sun kwato bindigogi, babura da wasu kayayyakin sadarwa da Boko Haram ke amfani da su wajen kai hare-hare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng