Sojoji Sun Shiga har Dajin Sambisa Sun Yi wa 'Yan Boko Haram Jina Jina
- Rundunar Operation Hadin Kai ta samu babbar nasara bayan dakile shirin kwanton bauna da ‘yan Boko Haram/ISWAP suka yi a Sambisa da Mandara
- A yayin artabun, sojoji sun kashe ‘yan ta’adda da dama tare da kwato makamai, babura da kayan sadarwa da ke taimaka musu wajen kai hare-hare
- Bayan nasarar da ta samu, rundunar sojin Najeriya ta ce za ta ci gaba da matsa lamba a fadin Arewa maso Gabas domin kawo karshen ‘yan ta’adda baki daya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Rundunar hadin gwiwa ta sojin Najeriya a Arewa maso Gabas karkashin Operation HADIN KAI ta sanar da samun gagarumar nasara kan ‘yan Boko Haram da ISWAP a dajin Sambisa da tsaunukan Mandara.
Harin ya gudana ne a ranar 22, Janairu, 2026, a karkashin Operation Desert Sanity V, inda ‘yan ta’addan suka yi yunkurin kwanton bauna ga dakarun soji.

Source: Facebook
A labarin da rundunar soji ta wallafa a X, sojoji sun mayar da martani mai karfi kan Boko Haram cikin gaggawa, lamarin da ya tarwatsa shirin ‘yan ta’addan tare da janyo musu asara mai yawa.
Sojoji sun kai farmaki Sambisa
Bayanan rundunar sun nuna cewa ‘yan Boko Haram da ISWAP sun shirya kai hari ta amfani da bama-baman da ake dasawa a kan hanya tare da harba bindigogi masu nauyi.
Sojojin runduna ta 1 na Operation Hadin Kai sun mayar da martani cikin kwarewa, inda suka yi amfani da makamai wajen murkushe 'yan ta'addan.
A sakamakon haka, an kashe ‘yan ta’adda 10, ciki har da manyan kwamandoji biyu da aka bayyana sunayensu a matsayin Basulhu da Ubaida.
Kayayyakin Boko Haram da aka gano
Bayan dakile harin, sojoji sun ci gaba da bibiyar ‘yan ta’addan da suka tsere, lamarin da ya ba su damar kwato tarin makamai da kayan aiki.
Daga cikin kayan da aka kwato akwai bindigogi kirar AK-47 guda uku, wata samfurin bindiga guda daya, babura guda biyar da gurneti biyu.
Haka kuma an kwato na’urorin sadarwa, majigi, harsasai, kayan hada bama-bamai da sauran kayayyakin da ke taimaka wa ‘yan ta’adda wajen gudanar da ayyukansu.
Artabun sojoji a yankin Malkube
A wani bangaren hare-hare, sojojin runduna ta1 karkashin Operation Hadin Kai sun sake cin karo da ‘yan ta’adda a yankin Malkube.
A wannan artabu, an kashe ‘yan ta’adda biyu tare da kwato karin bindigogi kirar AK-47, harsasai da kayan sadarwa, ba tare da sojoji sun rasa ko daya daga cikinsu ba.

Source: Facebook
An kara dakile shirin Boko Haram
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa wani bangaren sojoji daga runduna ta 1 ya yi artabu da ‘yan Boko Haram/ISWAP da ke kokarin kutsowa daga kasar Kamaru ta yankin Galakura zuwa Najeriya.
Sojojin sun tilasta musu ja da baya cikin rudani, tare da kwato kayayyaki da abubuwan hawa da suka bari, daga cikin kayan da aka samu akwai babura guda biyu da wasu kayayyaki..
An gano kabarin Boko Haram a Borno
A wani labarin, mun kawo muku cewa dakarun Najeriya sun kusta cikin dajin Timbuktu Triangle da ake cewa shi ne babban sansanin Boko Haram.
Yayin da suka shiga wajen, sojoji sun fafata da mayakan Boko Haram, inda aka kashe da dama wasu kuma suka ruga da gudu.
A binciken da sojoji suka yi a dajin, dakarun Najeriya sun gano wani babban kabarin da aka birne 'yan Boko Haram da aka kashe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


