Tonon Silili: Tsohon Gwamna Ya ‘Tona’ Abin da Tinubu Ya Ce ga Makinde Balo Balo
- Tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana abin da aka tattauna tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Seyi Makinde
- Fayose ya ce Tinubu ya fada masa balo-balo ba zai goyi bayansa a siyasa ba a zaben shekarar 2027 da ke tafe ba
- Ya ce Tinubu ya jaddada cewa Makinde ya ci gaba da zama a PDP, yana mai cewa babu wata dama ko yarjejeniya gare shi a APC
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana wasu bayanai game da abin da ya faru a ganawar Bola Tinubu da Seyi Makinde.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a Fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Source: UGC
'Abin da Tinubu ya ce ga Makinde'

Kara karanta wannan
Lissafi zai iya canzawa, Tinubu ya shiga ganawa da gwamnan PDP a fadar shugaban kasa
Fayose ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, 22 ga watan Janairun 2026.
Ya ce ganawar ta kunshi tattaunawa mai zurfi kan siyasa, biyayya ga jam’iyya da kuma babban zaben shekarar 2027.
A cewarsa, Shugaba Tinubu ya bayyana wa Gwamna Makinde cewa a shirye yake ya saurare shi kan batutuwan mulki da suka shafi jihar Oyo kawai, amma ba zai shiga tattaunawar siyasa ta sirri da ke sabawa kalaman da Makinde ke yi a bainar jama’a ba.
Fayose ya ce shugaban ya gargadi Makinde kan zarginsa na cewa Tinubu na shirin kafa jam’iyya daya tilo a kasar, sannan daga baya ya nemi sasanci a bayan fage.
Ya ce Shugaban kasa ya bayyana cewa:
“Ba zai yiwu mutum ya fadi wani abu a fili, sannan ya zo a sirrance yana fadin wani abu dabam ba.”

Source: Facebook
Meye Tinubu ya fadawa Makinde kan 2027?
Dangane da zaben 2027, Fayose ya ce Tinubu ya bayyana wa Makinde karara cewa kada ya sa ran samun wani goyon bayan siyasa daga gare shi, domin a matsayinsa na jagoran jam’iyyar APC, wajibi ne ya mara wa jam’iyyarsa baya.

Kara karanta wannan
Kaduna: Gwamna ya sha alwashi, zai ceto mutum sama da 170 da 'yan ta'adda suka sace
A cewarsa, Shugaban kasar ya kuma ce Gwamna Makinde ya ci gaba da zama cikin kwanciyar hankali a jam’iyyar PDP, yana mai cewa babu wata yarjejeniya ta siyasa da za ta hada shi da APC.
Har ila yau, Fayose ya ce Shugaba Tinubu ya sake jaddada cikakken goyon bayansa ga Ministan Abuja, Nyesom Wike, inda ya bayyana shi a matsayin amintaccen aboki wanda biyayyarsa ba za a yi watsi da ita ba.
Ya ce Tinubu ya shaida wa Seyi Makinde cewa duk wani rikici da ke tsakaninsa da Wike batu ne na kansu ko na jam’iyya, kuma bai kamata a saka ofishin Shugaban kasa cikin lamarin ba.
Makinde ya yi magana bayan ganawa da Tinubu
An ji cewa Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya sanya labule da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Alhamis, 22 ga watan Janairun 2026.
Seyi Makinde ya amsa tambayoyi daga wajen manema labarai kan yiwuwar sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki.
Gwamnan na daga cikin sauran gwamnonin da suka rage a jam'iyya mai adawa inda ya ce yana nan a PDP ba zai yi rawa ba.
Asali: Legit.ng