Yadda Taimakon Amurka Ya Sanya Sojojin Najeriya Rage Karfin 'Yan Boko Haram

Yadda Taimakon Amurka Ya Sanya Sojojin Najeriya Rage Karfin 'Yan Boko Haram

  • Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Abdulsalam ya yi magana kan taimakon da suke samu daga Amurka
  • Manjo Janar Abdulsalam Abubakar ya ce suna amfani da hadin gwjwar da aka yi da Amurka wajen murkushe 'yan ta'addan Boko Haram
  • Kwamandan ya bayyana cewa suna ci gaba da kai hare-hare ta sama da kasa don kawo karshen 'yan Boko Haram cikin kankanin lokaci

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Abdulsalami Abubakar, ya yi magana kan yaki da 'yan ta'addan Boko Haram.

Kwamandan ya ce rundunar sojojin Najeriya na amfani da sabon haɗin gwiwar da ta kulla da Amurka domin karfafa yakin da ake yi da Boko Haram da kungiyoyin da suka balle daga cikinta.

Sojojin Najeriya na ci gaba da ragargazar 'yan Boko Haram
Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Jaridar The Nation ta ce Manjo Janar Abubakar ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar da manema labarai na bangaren tsaro suka kai masa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Kara karanta wannan

Bello Turji ya firgita a cikin daji, yana gudun neman tsira zuwa wurare

Amurka na taimakon sojojin Najeriya

Kwamandan ya ce gwamnatin Amurka na ba sojojin Najeriya muhimman bayanan sirri da ke taimaka musu wajen hallaka ’yan ta’adda da yawa.

“Muhimmin abin da nake so na jaddada shi ne yadda muke amfana da haɗin gwiwarmu da Amurka."
"Bisa ingantattun bayanan sirri masu matuƙar muhimmanci ne muke aiki domin ganin mun kawo ƙarshen wannan yaƙi cikin gajeren lokaci."
“Muna samun bayanan sirri masu muhimmanci, wanda ya kara karfafa ayyukanmu. Kun gani a kafafen watsa labarai cewa an kashe ’yan ta’adda 40."
"Wannan ya faru ne sakamakon hare-haren sama da na kasa da ake ci gaba da yi a dazuzzuka, musamman a Dajin Sambisa da duk faɗin yankin Timbuktu Triangle.”

- Manjo Janar Abdulsalam Abubakar

Sojoji na ragargazar 'yan Boko Haram

Manjo Janar Abubakar ya ce sun samu umarnin gudanar da manyan hare-hare masu karfi, inda ya bayyana cewa ta wannan hanya rundunar ta hallaka manyan shugabannin Boko Haram guda 54, ciki har da Abu Fatima, wanda aka sa tukwici na Naira miliyan 100 a kansa.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi magana kan sace masu ibada a Kaduna, ya fadi kuskuren gwamnati

“Muna aiwatar da abin da muke kira hare-haren kawar da shugabannin ’yan ta’adda."
“Ma’ana, muna kai farmaki ne kan tsarin jagoranci na abokan gaba. Idan ka lalata shugabanci, tsarin gaba ɗaya zai rushe. Hakan na raunana ikon yanke shawara na ’yan ta’adda a hankali."
“Shi ya sa bayanan sirri ke da matuƙar muhimmanci.”

- Manjo Janar Abdulsalam Abubakar

Kwamandan OPHK ya gana da manema labarai
Wasu daga cikin mahalarta taro da kwamandan rundunar Operation Hadin Kai Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

'Yan Boko Haram na mika wuya

Rahoton TVC News ya ce kwamandan ya kuma bayyana cewa a shekarar 2025 kaɗai, mutane fiye da 16,000 da ake zargin ’yan Boko Haram ne, tare da iyalansu, sun miƙa wuya sakamakon matsin lamba mai karfi da sojoji suka dinga musu.

Ya ce wannan ci gaba ba wai kawai ya taimaka wajen inganta zaman lafiya a Arewa maso Gabas ba, har ma ya kara bunkasa harkokin tattalin arziki da zamantakewar jama’a.

Bam ya tarwata motocin sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun fuskanci harin daga wajen 'yan ta'addan Boko Haram a Borno.

Kara karanta wannan

An bada umarnin kama tsohon hadimin gwamna da mutum 4 kan zargin alaka Bello Turji

Wani dan kunar bakin wake ya tuka mota dauke da bama-bamai ya buge motocin sojoji, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji biyar tare da jikkata wasu da dama.

Rahotanni sun nuna cewa sojojin na kan hanyarsu ta dawowa daga wani aikin kakkabe sansanonin ’yan ta’adda lokacin da lamarin ya auku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng