Kisan Gilla: Lauya Ya ci Gyaran Masu Neman a Yanke wa Su Umar Hukuncin Kisa
- Wani lauya a Kano ya ce kiran a gaggauta kashe masu laifin kisan uwa da ’ya’yanta shida ya saɓa wa dokokin Najeriya
- Ya bayyana cewa dole ne kotu ta same wanda ake zargi da laifi, tare da kammala dukkan matakan ɗaukaka ƙara, kafin hukuncin kisa
- Lauyan ya gargadi jama’a kan ɗaukar doka a hannu, yana mai cewa dole ne a bar shari’a ta bi ƙa’ida duk da tsananin laifi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wani lauya a jihar Kano, Mubarak Abubakar, ya yi magana game da mutane da ke neman a yanke wa wadanda ake zargi ya kashe iyali guda hukuncin kisa.
Lauyan ya bayyana cewa kiran da wasu jama’a ke yi na a hanzarta kashe wadanda ake zargi da hallaka Fatima da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi-Chiranci, ya saɓa wa doka.

Source: Facebook
Kisan gilla: Lauya ya gargadi mutane a Kano
Lauyan ya jaddada cewa bisa ƙa’ida, ba za a iya aiwatar da hukuncin kisa ga kowa ba, sai bayan kotu mai ikon shari’a ta same shi da laifi bayan cikakken bincike da sauraron shari’a, cewar Aminiya.
Ya ce doka ta tanadi matakai masu tsauri kafin hukuncin kisa, inda dole ne wanda ake zargi ya samu damar kare kansa a kotu, tare da amfani da dukkan hanyoyin ɗaukaka ƙara da kundin tsarin mulki ya tanada.
A cewarsa, ko bayan kotu ta yanke hukunci, doka ta bai wa wanda aka same shi da laifi damar kai ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara, sannan daga bisani zuwa Kotun Ƙoli.
“Har sai an kammala dukkan waɗannan matakai na shari’a, ba bisa doka ba ne a aiwatar da hukuncin kisa."

Source: Facebook
'Sharadin yanke hukunci kan laifuffuka' - Lauya
Lauyan ya ƙara da cewa, sai bayan Kotun Ƙoli ta yanke hukunci na ƙarshe, kuma babu sauran damar ƙara ne kawai doka ke ba da izinin aiwatar da hukuncin kisa.
Ya yi nuni da cewa duk da tsananin zafin laifin kisan gilla, dole ne a bar doka ta yi aikinta, domin kauce wa ɗaukar doka a hannu duba da yadda al'umma suka fusata.
Ya kuma yi gargaɗi cewa irin kiran da ake yi na iya haddasa tashin hankali a cikin al’umma, yana mai jaddada cewa adalci na gaskiya ba ya samuwa sai an bi hanyar doka.
Masanin shari'ar ya yi kokarin nuna yadda doka ta ke aiki ne ba bada kariya ga wadanda ake zargi ba.
Alkawuran da Abba ya yi wa Haruna Bashir
Mun ba ku labarin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi alkawarin biya wa Haruna Bashir, mutumin da aka kashe matarsa da yaransa kudin aikin Hajji da Umrah.
Abba Kabir ya bayyana haka ne a lokacin da ya je ta'aziyya ga mutumin bisa wannan jarabawa da ya tsinci kansa a ciki a unguwar Dorayi da kuma dauka masa alkawura.
Gwamnan ya kuma dauki nauyin auren da Haruna zai yi, tare da ba shi kyautar sabon gida a wata unguwa ta daban a jihar Kano domin samun kwanciyar hankali.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


