Kotun Kolin Najeriya Ta Kunyata Wadanda Suka Nemi a Dawo da Shari'ar Hamza Al Mustapha

Kotun Kolin Najeriya Ta Kunyata Wadanda Suka Nemi a Dawo da Shari'ar Hamza Al Mustapha

  • Gwamnatin jihar Legas ta gaza daukaka kara kan shari'ar tsohon dogarin shugaban kasa, Manjo Hamza Al-Mustapha
  • Kotun koli ta yi watsi da karar da ke gabanta na neman dawo da shari'ar Al-Mustapha kan kisan Kudirat Abiola
  • Al-Mustapha ya sha fama da wannan shari'a ta zargin kisan Kudirat, laifin da ya musanta a gaban kotu kafin daga bisani ya samu 'yanci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Bayan shekaru tara da shigar da ita, kotun koli ta yi fatali da karar da aka nemi sake gurfanar da tsohon babban dogarin shugaban kasa, Manjo Hamza Al-Mustapha (mai ritaya).

Kotun ta ki aminta da sake dawo da Al-Mustapha gaban kuliya domin ci gaba da shari'ar da ake tuhumarsa da kisan Kudirat Abiola.

Manjo Hamza Al-Mustapha.
Tsohon dogarin shugaban kasa, Manjo Hamza Al-Mustapha Hoto: Hamza Al-Mustapha
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Manjo Hamza Al-Mustapha ya yi aiki ne a matsayin babban dogarin tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Marigayi Janar Sani Abacha.

Kara karanta wannan

Tikitin ADC: Baba Ahmed ya samo mafita ga Peter Obi kan fafatawa da su Atiku, Amaechi

Zargin da ake wa Hamza Al-Mustapha

Rahotanni sun nuna cewa an kashe Kudirat, matar marigayi Moshood Abiola, ne a ranar 4 ga watan Yunin 1996 a birnin Legas.

An tuhumi Al-Mustapha da Lateef Shofolahan, wanda mataimaki ne ga Kudirat, da hannu a kisan na ta.

Bayan haka, gwamnatin jihar Legas ta gurfanar da su a gaban kotu kan tuhume-tuhume guda biyu da suka shafi hadin baki wajen kisan kai, da kuma kisan Kudirat din kanta.

Yadda aka wanke Manjo Al-Mustapha

A ranar 30 ga watan Janairun 2012, Mojisola Dada, alkalin babbar kotun tarayya da ke Legas, ta yanke wa Manjo Al-Mustapha da Shofolahan hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samunsu da laifin kisan kai.

Sai dai, Al-Mustapha da Shofolahan sun daukaka kara kan hukuncin a kotun daukaka kara reshen Legas, inda a nan ne aka wanke su daga zargin a ranar 12 ga watan Yulin 2013.

A ranar 12 ga watan Janairun 2017, wani kwamitin alkalai guda biyar na kotun koli karkashin jagorancin Walter Onnoghen, ya ba gwamnatin Legas karin lokaci domin shigar da karar, duk da lokacin yin hakan ya wuce.

Kara karanta wannan

Binciken makamai: Malami na tsaka mai wuya a hannun hukumar DSS, ya fito ya yi magana

Gwamnatin Legas ta gaza komawa kotu

To sai dai kuma, a zaman kotu na yau Alhamis, Paul Daudu, lauyan Al-Mustapha, ya shaida wa kotun cewa har yanzu jihar Legas ba ta dauki wani mataki na aiwatar da umarnin da aka ba ta tun a shekarar 2017 ba.

Don haka, ya bukaci kotun da ta dauka cewa mai daukaka karar ya yi watsi da shari’ar, kuma a yi fatali da ita baki daya, cewar rahoton Guardian.

Bayan wani bincike da kwamitin alkalai biyar na kotun koli karkashin Uwani Abba-Aji ya gudanar, an gano cewa an isar da takardar sanarwar zaman kotun ga jihar Legas yadda ya kamata, amma duk da haka ba su turo lauya ya wakilce su ba.

Kotun Koli.
Kofar shiga harabr kotun kolin Najeriya Hoto: Supreme Court
Source: Facebook

Kotun koli ta kori karar gaba daya

A cikin wani takaitaccen hukunci, kwamitin alkalai ya amince da cewa jihar ta daina sha’awar ci gaba da wannan shari’a.

Alkalan sun nuna cewa shekaru tara lokaci ne mai tsawo da ya kamata mai daukaka kara ya riga ya shigar da sanarwarsa da kuma hujjojin daukaka karar, bisa haka kotun koli ta yi watsi da karar mai lamba SC/CR/45/2014 baki daya.

Kara karanta wannan

Abubakar Malami ya yi magana game da makamai da DSS ta gano a 'gidansa' na Kebbi

Yadda Abacha da Abiola suka mutu

A wani labarin, kun ji cewa tsohon dogarin Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha, ya bayyana cewa mutuwar mai gidansa da MKO Abiola ta faru ne ta hanya iri ɗaya.

Al-Mustapha ya ce akwai abubuwa masu zurfi da mutane ba su sani ba game da zaɓen da aka soke da kuma mutuwar MKO Abiola.

Tsohon dogarin ya nesanta kansa daga batutuwan da suka shafi littafin Ibrahim Babangida , da kuma bayyana irin yadda tsohon maigidansa da Abiola suka mutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262