Ana Wata Ga Wata: Amurka Ta Sake Waiwayo Najeriya kusan Wata 1 bayan Kawo Hari
- Amurka ta sake turo babbar tawaga Najeriya domin tattaunawa da gwamnatin tarayya kan yadda za a kare rayukan kiristoci
- Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa wannan ziyara da wani bangare na rangadin diflomasiyya da za ta gudanar a kasashe da dama
- Bayan Najeriya, tawagar Amurka za ta ziyarci kasashen Oman da Bahrain domin tattaunawa da manyan jami’an gwamnatocin kasashen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tawagar manyan jami’an gwamnatin Amurka za ta ziyarci Najeriya domin tattaunawa da gwamnatin kasar kan batun kare Kiristoci da karfafa ayyukan yaki da ta’addanci.
Ma’aikatar Wajen Amurka ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba cewa, wannan ziyarar tana daga cikin wani rangadin diflomasiyya da za su gudanar a fadin Afirka, Gabas Ta Tsakiya, da kuma Turai.

Source: UGC
A sanarwar da ma'aikatar ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta ce rangadin da tawagar za ta yi zai kwashe mako guda, daga ranar 21 zuwa 29 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan
An bada umarnin kama tsohon hadimin gwamna da mutum 4 kan zargin alaka Bello Turji
Amurka ta sake turo tawaga Najeriya
Tawagar tana karkashin jagorancin Sakatariyar Ma’aikatar Wajen Amurka, Allison Hoker, wadda kuma za ta kasance "shugabar tawagar ayyukan hadin gwiwa tsakanin Amurka da Najeriya."
Gwamnatin Amurka, ta hanyar wannan tawaga, za ta taimaka wa Najeriya wajen yaki da ta’addanci tare da bunkasa damar zuba jari a kasar.
“A Najeriya, Sakatariyar za ta jagoranci tawagar hadin gwiwa ta Amurka da Najeriya, kuma za ta tallafa wa kokarin gwamnati na kare Kiristoci, yaki da ta’addanci, da kuma fadada damar zuba jari daga Amurka,” in ji sanarwar.
Yadda Amurka ta kawo hari Najeriya
Shugaba Trump dai ya taba yin ikirari da aka bayyana a matsayin "mara tushe" na cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.
Sai dai a lokuta da dama, gwamnarin Najeriya ta musanta wannan zargi, tana mai vewa matsalar tsaron kasar ya shafi kowane addini.
A ranar 25 ga watan Disamba, Amurka ta kawo harin makami mai linzami a Najeriya da nufin yakar yan ta'addan da ake zargin su na da alaka da kungiyar ISIS.

Kara karanta wannan
Ramadan: Izala ta fitar da jerin malaman da za su yi tafsir a jihohi, kasashe a 2026
Amurka ta dauki wannan mataki ne tare da hadin gwiwar hukumomin Najeriya wadanda suka samar da bayanan sirri.
Kasashen da tawagar Amurka za ta je
Premium Times ta ce wannan ziyara ita ce ta baya-bayan nan da za ta hada manyan jami’an Najeriya da na Amurka tun bayan da Shugaba Trump ya fara nuna kiyayya ta baki ga Najeriya.
Bayan Najeriya, tawagar Amurka za ta ziyarci kasashen Oman da Bahrain domin tattaunawa da manyan jami’an gwamnatocin kasashen kan tsaron yanki, dangantakar tattalin arziki, da al’adu.

Source: Twitter
Kasar Italiya ce za ta kasance ta karshe, inda za su tattauna da jami’an kasar kan yakin Rasha da Ukraine, kasar Venezuela, da kuma kokarin samar da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya.
An nemi hadin gwiwar sojojin Najeriya da Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bukaci ƙara zurfafa haɗin gwiwar dabaru tsakanin sojojin kasar nan da na Amurka.
Laftanar Janar Waidi Shaibu ya bayyana cewa sauye-sauyen yanayin tsaro a Najeriya na buƙatar ƙarin haɗin kai da ƙasashen da ke da gogewa a fannin soja.
A cewarsa, ƙarfafa irin wannan haɗin gwiwa za ta taimaka wajen inganta kwarewar aiki, tsara dokoki da dabaru, da kuma ƙarfafa ƙarfin rundunar wajen tunkarar matsalar tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng