Duk da Barazanar Amurka, Najeriya za Ta Fara Aiki da Tsarin Musulunci

Duk da Barazanar Amurka, Najeriya za Ta Fara Aiki da Tsarin Musulunci

  • Rahotanni sun nuna cewa hukumar FRC ta bayyana shirin shigar da ka’idojin kudin Musulunci na duniya cikin tsarin rahoton kudi na Najeriya
  • FRC ta ce shirin na da nufin kara tsari, kare masu zuba jari da kuma mayar da Najeriya cibiyar harkokin kudin Musulunci a nahiyar Afirka
  • Masu ruwa da tsaki sun ce ba za a lalata tsarin da ake da shi ba, sai dai a karfafa shi da sababbin ka’idoji domin tafiyar da lamura da kyau

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar FRC ta ce ana ci gaba da shirye-shiryen shigar da ka’idojin kudin Musulunci na duniya cikin Tsarin Rahoton Kudi na Najeriya, NFRF.

Shugaban hukumar, Rabiu Olowo ne ya bayyana hakan a Abuja a ranar Laraba, 21 ga Janairun 2021 yana mai cewa shirin zai taimaka wajen karfafa tsari a fannin rahoton kudi.

Kara karanta wannan

Ana rokon Tinubu ya sauke Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan daga shugabancin NAHCON

Yadda aka gabatar da jawabi a taron FRC ta Najeriya
Dr Rabiu Olowo yayin taron FRC da aka yi a Abuja. Hoto: Financial Reporting Council of Nigeria
Source: Facebook

Hukumar ta wallafa a X cewa Dr Rabiu Olowo ya ce matakin zai kuma kare masu zuba jari tare da sanya Najeriya ta zama cibiyar harkokin kudin Musulunci a nahiyar Afirka.

Najeriya za ta bi tsarin Musulunci

Dr Olowo ya bayyana cewa wannan shiri ya biyo bayan sanarwar da hukumar FRC ta yi a bara na daukar ka’idojin kudi na AAOIFI.

A cewarsa, wadannan ka’idoji sun shafi cibiyoyin kudi na Musulunci da kuma cibiyoyin da ba sa amfani da riba da ke aiki a Najeriya.

Ya ce cibiyoyin kudin Musulunci na tafiya ne da ka’idoji na musamman da suka bambanta da tsarin kudi, musamman a bangaren haramcin riba, tallafin kudi da kuma zuba jari bisa ka’ida.

Za a yi hadin gwiwa da masana

Shugaban FRC ya jaddada cewa bambancin tsarin kudin Musulunci da kishiyarsa ne ya sa ya zama wajibi a yi aiki kafada da kafada da masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan

Ramadan: Izala ta fitar da jerin malaman da za su yi tafsir a jihohi, kasashe a 2026

Ya ce hadin gwiwar za ta taimaka wajen shigar da ka’idojin da sababbin dabarun cibiyoyin kudin Musulunci cikin tsarin rahoton kudi na kasa.

A cewarsa, tsarin zai tabbatar da cewa rahotannin kudi sun nuna hakikanin ma’amaloli na kudin Musulunci, ciki har da batutuwan shugabanci.

Tasirin aiki da ka’idojin AAOIFI

Dr Olowo ya bayyana cewa amfani da ka’idojin AAOIFI zai kara gaskiya, amana da daidaito a rahoton kudi a fannin kudin da ba ya aiki da riba.

Ya ce hakan zai taimaka wajen karfafa ladabi da gaskiya da amana a kasuwa tare da kara kwarin gwiwar masu zuba jari a Najeriya.

A cewarsa, wannan mataki zai sa rahotannin kudi su zama masu saukin fahimta da kwatantawa, a Najeriya da ma kasashen waje.

Tsarin Musulunci na karbuwa a duniya

Shugaban FRC ya kuma yi nuni da yadda harkokin kudin Musulunci ke kara samun karbuwa a duniya, ba wai a kasashen Musulmi kadai ba.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ya ambaci kasashe kamar Birtaniya da suka riga suka yarda da tsarin Sukuk da sauran lamuran kudi na Musulunci da ba sa amfani da riba.

Kara karanta wannan

Dattawan Katsina sun shiga maganar sakin 'yan bindiga 70, sun zafafa kalamai

Dr Olowo ya bayyana cewa amfani da shirin daukar ka’idojin AAOIFI ba ya nufin rushe tsarin kudi da ake da shi a Najeriya a halin yanzu.

Wasu mahalarta taron FRC a Abuja
Wasu mahalarta taron FRC kan harkokin kudin Musulunci. Hoto: Financial Reporting Council of Nigeria
Source: Facebook

An gurfanar da malamin Musulunci a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan sanda sun gurfanar da malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Isa Makwarari a gaban kotu a jihar Kano.

Kwamishinan kasa na jihar Kano, Abduljabbar Garko ya bayyana cewa suna zargin malamin da karkatar da wasu filaye a jihar.

Hon. Garko ya ce an dade ana neman malamin amma ba a same shi sai da 'yan sanda suka samu damar cafke shi a wannan karon.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng