Binciken Makamai: Malami na Tsaka Mai Wuya a Hannun Hukumar DSS, Ya Fito Ya Yi Magana
- Tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami ya bayyana cewa hukumar DSS ta tauye masa hakkokinsa tun bayan cafke shi a kofar gidan yarin Kuje
- Rahotanni sun nuna cewa an sake kama tsohon babban lauyan gwamnatin jim kadan bayan ya samu beli sakamakon wasu makamai da aka gano a gidansa
- A wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Abubakar Malami ya ce an hana shi ganin iyalai da lauyoyinsa tun da ya fada hannun DSS
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon Antoni Janar na Tarayya (AGF) kuma tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya koka kan halin da yake ciki a hannun hukumar tsaro ta DSS.
Malami, wanda ya yi aiki a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, ya zargi hukumar DSS da hana shi ganin iyalansa da kuma tawagar lauyoyinsa.

Source: Facebook
Yadda Abubakar Malami ya shiga hannun DSS
The Cable ta ruwaito cewa tun farko, Malami na fuskantar shari’a tare da dansa da matarsa kan zargin da ya shafi halatta kudade bayan EFCC ta gurfanar da shi, inda aka tsare shi a gidan yarin Kuje da ke Abuja.
A ranar 7 ga watan Janairu, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba shi beli kan kudi Naira miliyan 500.
Sai dai kuma, jim kadan bayan fitowarsa daga gidan yarin a ranar Litinin, jami’an DSS suka sake kama Malami, kamar yadda The Nation ta kawo.
An ruwaito cewa dakarun DSS sun sake kama tsohon ministan ne bisa zargin gano makamai a gidansa.
Malami ya koka kan tauye masa hakkoki
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Mohammed Doka, mai magana da yawun Abubakar Malami, ya ce rahotannin da ke cewa DSS ta gano makamai a gidan Malami "karya ne."

Kara karanta wannan
Kujerar Hajji, sabon gida da wasu kyaututtuka 3 da Gwamna Abba ya yi waijin Fatima
Mohammes Doka ya bayyana cewa ba a sanar da iyalai ko lauyoyin Malami hakan a hukumance ba.
Ya ce:
"Tsawo lokacin da Malami ya shafe a killace a hannun DSS abin damuwa ne musamman game da lafiyarsa da kuma hakkokin da kundin tsarin mulki ya ba shi".
"Tun lokacin da DSS ta kama shi a ranar Litinin, an hana Abubakar Malami, SAN, ganin iyalansa, tawagar lauyoyinsa da abokan arziki."

Source: Twitter
Sanarwar ta kara da cewa Abubakar Malami babban jigo ne a jam'iyyar ADC, kuma ya riga ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Kebbi a zaben 2027.
"Idan aka yi la'akari da wannan yanayin, ba za a iya cewa babu siyasa a tattare da wannan al'amari ba. Dole ne matakan shari'a su kasance masu cin gashin kansu ba tare da shigar da batutuwan siyasa ba," in ji shi.
An gano makamai a gidan Malami
A wani rahoton, kun ji cewa an sake bude sabon bincike kan tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami bayan samamen da hukumar EFCC ta kai gidansa a jihar Kebbi.
An ruwaito cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta ci karo da bindigu da alburusai lokacin da ta kai samame gidan Malami da ke birnin Kebbi.
Ba a bayyana adadin makamai da harsasan da aka gano ba a halin yanzu, amma rahotanni sun nuna cewa adadinsu ya kai yawan da zai jawo cikakken bincike daga DSS .
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

