Kujerar Hajji, Sabon Gida da Wasu Kyaututtuka 3 da Gwamna Abba Ya Yi Wa Mijin Fatima
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin biya wa Haruna Bashir, mutumin da aka kaahe matarsa da yaransa kudin aikin Hajji da Umrah
- Abba ya bayyana haka ne a lokacin da ya je ta'aziyya ga mutumin bisa wannan jarabawa da ya tsinci kansa a ciki a unguwar Dorayi
- Gwamnan ya kuma dauki nauyin auren da Haruna zai yi, tare da ba shi kyautar sabon gida a wata unguwa ta daban a jihar Kano
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - A yau Laraba, 21 ga watan Janairu, 2025 ne gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya tafi da kansa zuwa unguwar Dorayi domin ta'aziyyar kisan Fatima Abubakar da yaranta shida.
Gwamna Abba ya nuna matukar alhininsa kan wannan mummunan lamari da ya faru a cikin jihar Kano, ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da an yi wa mamatan adalci.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba ya dauki alkawari kan kisan Fatima da yaranta 6, Hanifa da masallata a Kano

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya tabbatar da ziyarar da Abba ya kai a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Gwamna Abba ya tallafawa mijin Fatima
Gwamna Abba ya kuma dauki alkawarin gyara rayuwar Malam Haruna Bashir, mijin Fatima Abubakar kuma mahaifin yara shida da miyagu suka shiga har gida suka kashe.
Ya bayyana cewa gwamnatin Kano za ta tallafa wa mutumin ta bangarori daban-daban, wanda ya hada da daukar nauyin aikin Hajji da Umrah, samar masa da gida, da kuma cikakken tallafin gwamnati.
Gwamnan ya kuma kara da cewa jiha za ta taimaka wa mutumin ya sake yin aure idan ya sami wadda ta dace, sannan za ta dauki nauyin duk abubuwan da ake bukata domin ya sake fara sabuwar rayuwa.
Jerin kyaututtuka 5 da Abba ya yi masa
Jim kadan bayan Abba ya sanar da wannan tallafi da taimakon da gwamnatinsa za ta yi wa Malam Haruna, Sanusi Dawakin Tofa ya jero duka kyaututtukan da gwamnan yi wa mutumin alkawari.
A wani gajeren sako da ya sake wallafafa a shafinsa, mai magana da yawun gwamnan Kano ya jero kyaututtuka biyar da Abba ya yi wa mijin Fatima, wanda suka hada da:
1. Kujerar Umra ga shi da dan uwan sa
2. Kujerun Hajji shi da dan'uwansa
3. Sabon gida a wata unguwar daban a Kano
4. Daukar nauyin sake yin aure
5. Tabbatar da daukar nauyin shari'a nan ba da dadewa ba.

Source: Facebook
Gwamna Abba Kabir ya kuma tsinewa wadanda suka aikata wannan ta'asa tare da da alkawarin sanya hannu akan hukunci da kota ka iya yanke musu, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.
Gwamna Abba ya dauki alkawari
A baya, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin sa hannu kan takardar hukuncin kisa ga duk wanda kotu ta kama da laifin kisan gillar da aka yi wa Fatima da yaranta shida.
Ya kuma sha alwashin sa hannu kan takardar hukuncin kisan wadanda suka kashe Hanifa da kuma wadanda suka banka wuta a masallacin Gezawa.
Abba ya yabawa jami'an tsaro bisa matakan da suka dauka na kama wadanda ake zargi da kisan Fatima da yaranta har guda shida.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
