Harin Bam Ya Tarwatsa Ayarin Motocin Sojoji a Borno, an Rasa Rayukan Jami’ai
- An tabbatar da kai harin bam da Boko Haram suka yi kan jerin motocin sojoji a yankin 'Timbuktu Triangle' da ke jihar Borno
- Harin ya yi sanadin mutuwar sojoji biyar tare da jikkata wasu da dama, ciki har da manyan jami’an soja biyu
- Rundunar soji ta tabbatar da cewa duk da harin, ana ci gaba da farmakin kakkabe ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - Wasu ’yan ta’addan Boko Haram sun kai harin bam kan jerin motocin sojoji a yankin 'Timbuktu Triangle' da ke jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa wani dan kunar bakin wake ya tuka mota dauke da bama-bamai ya buge motocin sojoji, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji biyar tare da jikkata wasu da dama.

Source: Facebook
Boko Haram sun farmaki sojoji a Borno
Majiyoyin tsaro sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa harin ya shafi manyan jami’an soja biyu, ciki har da Manjo da mai mukamin Laftanar.
Wani soja ya ce harin ya janyo gagarumar asara ga kayan aikin sojoji da ake amfani da su wajen farmakin kai hari da kare kai a yayin aikin kakkabe ’yan ta’adda da ake gudanarwa tsawon makonni.
Ya ce ’yan ta’addan sun yi amfani da mota da aka cika da abubuwan fashewa wajen kai harin.
Rahotanni sun nuna cewa sojojin na kan hanyarsu ta dawowa daga wani aikin kakkabe sansanonin ’yan ta’adda, inda suka tarwatsa wurare da dama tare da kashe wasu daga cikinsu, kafin harin ya afku.
Wani jami’in soja da ya nemi a sakaya sunansa ya ce duk da irin koma bayan da aka samu, rundunar ta shawo kan lamarin, sai dai an rasa sojoji biyar.

Kara karanta wannan
Abba, Barau da hukumomi 2 da suka yi alkawarin nema wa Fatima da yaranta 6 adalci
Ya kara da cewa kwamandan rundunar, Manga, na cikin koshin lafiya, kuma aikin soja na ci gaba ba tare da tsaiko ba.
An kuma bayyana cewa motoci masu sulke da na kayan aiki sun lalace sakamakon harin da ya faru a ranar Talata 20 ga watan Janairun 2026.
Rahotanni sun ce an kwashe gawarwakin sojojin da suka rasu zuwa Maiduguri, yayin da aka kai wadanda suka jikkata asibiti domin samun kulawar lafiya.
Yankin 'Timbuktu Triangle' dai ya shahara wajen kai hare-hare, inda a baya ’yan ta’adda suka yi kwanton bauna ga Brigadier-janar Musa Uba, suka kama shi tare da kashe shi.
A baya-bayan nan, rundunar Joint Task Force ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai, ta sanar da kakkabe sansanonin ’yan ta’adda da dama tare da dakile hare-haren jirage marasa matuka a yankin.
Rundunar soji ta jaddada cewa duk da kalubalen tsaro, sojoji na cikin shirin ko-ta-kwana domin kare fararen hula da kuma dawo da zaman lafiya mai dorewa a yankin Arewa maso Gabas.
Sojoji sun illata yan ta'adda a Borno
An ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya sun nuna bajinta a ci gaba da kokarin da suke na samar da tsaro a yankin Arewa maso Gabas.
Sojojin saman na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), sun yi ruwan wuta kan maboyar 'yan ta'adda a karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno.
Ruwan wutar da sojojin suka yi, ta sanya an samu nasarar hallaka 'yan ta'adda da dama tare da lalata kayayyakin aikinsu.
Asali: Legit.ng

