An Cafke Babban Malamin Musulunci, an kai Shi Kotu kan Cinye Filaye a Kano

An Cafke Babban Malamin Musulunci, an kai Shi Kotu kan Cinye Filaye a Kano

  • ’Yan sandan Kano sun gurfanar da Sheikh Ibrahim Isa Makwarari a gaban kotu bisa zargin karkatar da filayen gwamnati da na al’umma
  • Rahotanni sun nuna cewa an samu ce-ce-ku-ce a zaman kotun bayan lauyansa ya ce akwai wata shari’a makamanciyarta a kasa
  • Bayan caccaka tsinke da aka yi a zaman da ya gudana, kotu ta bayar da belin malamin tare da ɗage shari’ar zuwa wani lokaci na daban

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – ’Yan sandan jihar Kano sun gurfanar da Sheikh Ibrahim Isa Makwarari a gaban Kotun Majistri mai lamba 53 da ke zamanta a unguwar Normansland, bisa zargin hannu a karkatar da filayen Gwamnati da na al’umma.

An gurfanar da wanda ake zargin ne a ranar Talata 20, Janairu, 2026, a gaban kotun da Mai Shari’a Mustapha Sa’ad Datti ke jagoranta.

Kara karanta wannan

Makotan Fatima da aka kashe da yaranta 6 a Kano sun fusata rundunar 'yan sanda

Sheikh Ibrahim Isa Makwarari
Malamin da aka gurfanar a Kano, Sheikh Ibrahim Isa Makwarari. Hoto: Darikar Qadiriyya Radio
Source: Facebook

Kwamishinan kasa na jihar Kano, Hon. Abduljabbar Garko ya yi karin bayani game da lamarin a wani bidiyo da Premier Radio ya wallafa a Facebook.

Yadda aka gurfanar da malamin a kotu

A yayin zaman kotun, lauyan malamin ya nuna wa kotun cewa akwai wata shari’a makamanciya da ke gaban wata babbar kotu, wadda ke da alaƙa da zargin da ake yi wa wanda yake karewa.

Rahotanni sun nuna cewa mai gabatar da ƙara ya bayyana wa kotun cewa tun a ranar 18 ga watan Nuwamban 2025 aka shigar da shari’ar.

Ya ce daga bisani ’yan sanda sun mayar da takardun shari’ar zuwa ma’aikatar shari’a domin neman shawararta kan ko akwai hujjojin laifi da za a gurfanar da wanda ake zargin ko kuma a sallame shi.

Bayan sauraron bayanan ɓangarorin biyu, kotu ta yanke shawarar ɗage shari’ar zuwa ranar Laraba 21, Janairu, 2026, domin ci gaba da gurfanar da wanda ake zargin. Hakazalika, kotu ta bayar da belinsa bisa wasu sharuɗa da ta gindaya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta shige gaba don shari'a kan kisan matar aure da yaranta 6

Bayanin kwamishinan filaye na Kano

Kwamishinan filaye na jihar Kano, Abduljabbar Umar Garko, ya bayyana cewa kamawa da gurfanar da Sheikh Ibrahim Isa Makwarari a kotu ya biyo bayan dogon bincike da aka gudanar a kansa.

A cewarsa:

“Mun samu nasarar kama shi da gurfanar da shi a kotu. Ba shakka shi wannan bawan Allah ya daɗe yana saka kansa a munanan dabi’u. Ba wannan ne karon farko da muke da matsala da shi ba.”

A wani bidiyo da Arewa Update ta wallafa a Facebook, Hon. Garko ya ƙara da cewa ana zargin wanda ake tuhuma da sayar da fili guda wa mutane da dama, inda idan wata matsala ta taso, sai ya sake sayar da filin ga wani daban.

Kwamishinan ya jaddada cewa babu wanda ya fi ƙarfin doka a Kano. Ya ce duk girman mutum, ko yana da mukami a gwamnati ko kuma malami ne, doka za ta yi halinta a kansa idan aka tabbatar da laifi.

Kara karanta wannan

Mahaifin Umar ya barranta da 'dansa da ake zargi da kashe yar uwarsa da yara 7

Kwanmishinan Kano, Abdujabbar Garko
Hon. Abduljabbar Garko da Abba Kabir Yusuf. Hoto: Abduljabbar Umar
Source: Facebook

Malamin Musulunci ya rasu a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa an wayi gari a Najeriya da rasuwar babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Habibu Yahaya Kaura.

Legit Hausa ta samu bayanai cewa Sheikh Habibu Kaura ya rasu ne bayan fama da doguwar jinya a wani asibiti a birnin tarayya Abuja da sassafe.

Tuni dai malaman Musulunci a Najeriya da suka hada da Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto, Dr Jabir Sani Mai Hula da sauransu suka nuna alhinin rashinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng