Makotan Fatima da aka Kashe da Yaranta 6 a Kano Sun Fusata Rundunar 'Yan Sanda

Makotan Fatima da aka Kashe da Yaranta 6 a Kano Sun Fusata Rundunar 'Yan Sanda

  • Rundunar ’yan sandan Kano ta karyata zargin da makotan Fatima Abubakar ke yadawa a kafafen sada zumunta bayan sun gaza kai dauki har aka kashe ta da yaranta
  • Wasu hirarraki da aka yi da wasu daga cikin makotan na bayyana cewa da su aka taimaka wajen kama mutanen da ake zargin sun aikata kisan mutum bakwai a Chiranchi Dorayi
  • ’Yan sanda sun ce makota ba su kai agaji ba, kuma duk da wannan rashin taimako, sun fito bainar jama'a suna sharara karya a kan mummunan aikin da ya girgiza mutane

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta zargi makotan Fatima Abubakar da wasu ɓata-gari uku suka hallaka tare da yaranta da yaɗa shararar ƙarya a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Kisan Fatima da yaranta: Daurawa ya jero matakan da za a bi don hukunta su Umar

A ranar Asabar, 17 ga watan Janairu, 2026 ne wasu ɓata-garin mutane suka shiga gidan Fatima, suka kashe ta da yaranta shida, sannan aka jefa ɗaya daga cikinsu a rijiya.

Rundunar yan sanda ta ji takaicin kalaman makotan Fatima Abubakar
Umar Auwal, wanda ake zargin dan uwa ne ga Fatima Abubakar da yagoranci kashe ta da 'ya'yanta 6 a Kano. Hoto: Hussaina Abkr
Source: Facebook

A wata sanarwa, kakakin rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa, ya wallafa a Facebook, ya bayyana takaicinsa game da abin da ya kira “ƙarya” da makotan Fatima ke yadawa a shafukan sada zumunta.

Bayanin makotan Fatima a Kano

A wani bidiyo da Aminci Radio ta wallafa a shafinta na Facebook, wasu makotan Fatima sun bayyana cewa ba gaskiya ba ne zargin da ake yi musu na cewa ba su kai wa matar da yaranta agaji ba.

Malam Bala Abubakar, wanda ke zaune a wurin makokin matar, ya ce sun kai ɗauki, sai dai ba su isa wurin da wuri ba saboda yadda lamarin ya faru cikin kankanin lokaci.

Yan sandan Kano sun ce makotan Fatima sun shirga karya
SP Abdullahi Haruna Kiyawa, kakakin rundunar yan sandan Kano Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Ya ce:

“Har yanzu ba mu cikin hayyacinmu muke ba saboda wannan bala’i da muka gani. Duk wanda ya ce maka a unguwar nan mutane suna barci, ƙarya yake wallahi. Kawai ihu muka ji, muka ɗauki matakin gaggawa. Amma da muka zo, sun riga sun gama yin abin da za su yi. A kankanin lokaci suka aikata laifin, sun gama shiri.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta shige gaba don shari'a kan kisan matar aure da yaranta 6

Malam Bala ya ƙara da cewa:

“Ihu barawo ne na farko, ihu barawo na biyu, an zagaye unguwar nan.”

Ya ce yara ne suka fara jin ihun matar da yaranta, lamarin da ya kai ga kunnen makota, sannan aka yi ƙoƙarin kai musu ɗauki.

A cewarsa, makota sun taimaka wajen kama mutanen da ake zargi da aikata laifin tun a wurin, saboda haka ba daidai ba ne a zarge su da rashin taimakon ceton rai.

Ya jaddada cewa unguwar ta girgiza ƙwarai da abin da ya faru, kuma mutane sun shiga alhini da ba za a manta da shi cikin sauƙi ba.

Martanin rundunar ’yan sandan Kano

Wannan hira da makamantanta da suka karade kafafen sada zumunta ba su yi wa rundunar ’yan sandan Kano daɗi ba.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya zargi mutanen da nade hannaye da cewa babu wani agaji na gaske da suka kai wa matar da yaranta har aka kashe su duka.

Kara karanta wannan

Mahaifin Umar ya barranta da 'dansa da ake zargi da kashe yar uwarsa da yara 7

Ya ce:

“Abin takaici ne matuƙa. Kuna cikin unguwa, kun ƙi ku taimaka, amma kun zo kafafen sada zumunta kuna ta yaɗa ƙarya.”

Kano: Mahaifin Umar na so a hukunta dansa

A baya, mun wallafa cewa Malam Auwal, mahaifin Umar da ake zargi da jagorantar kisan wata baiwar Allah mai suna Fatima Abubakar tare da dukkannin yaranta ya yi magana kan lamarin da ya girgiza al’umma.

Umar, tare da wasu mutane uku, na hannun jami’an ’yan sandan jihar Kano bayan sun amsa laifin shiga gidan Fatima Abubakar tare da kashe ta da yaranta shida a ranar Asabar, 17 ga watan Janairu, 2026.

Mahaifin Umar ya bayyana cewa ba shi da hannu, haka kuma yana cikin takaici da dimuwa a kan yadda dansa ya kashe kanwarsa da dukkanin yaranta, sannan ya nemi hukuma ta hukunta shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng