'Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojoji Kwanton Bauna a Zamfara, an Samu Asarar Rayuka
- Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yamma sun fuskanci harin kwanton bauna daga wajen 'yan bindiga a jihar Zamfara
- Tsagerun 'yan bindigan sun yi wa dakarun sojojin kwanton bauna ne yayin da suke dawowa daga farmakin da suka kai wa 'yan ta'adda
- Lamarin mara dadi ya jawo an samu asarar rayukan sojoji tare da wani jami'in 'yan sanda guda daya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi wa dakarun sojoji kwanton bauna a jihar Zamfara.
'Yan bindigan sun hallaka akalla sojoji biyar da jami’in ‘yan sanda daya bayan da su kai musu kwanton bauna a kan hanyar Bingi–Kekun Waje–Gusau a jihar Zamfara.

Source: Twitter
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, David Adewusi, jami’in yada labarai na Operation Fansan Yamma (OPFY), David Adewusi, ya fitar a shafin X a ranar Talata, 20 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan
Sojojin sama sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'adda a Borno, an kashe tantirai da dama
'Yan bindiga sun yi wa sojoji kwanton bauna
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin, 19 ga watan Janairun 2026 bayan da dakarun rundunar Operation Fansan Yamma suka kammala wani farmaki na tsawon kwanaki uku a yankunan Birnin Magaji da Anka na jihar Zamfara.
Jami'in yada labaran ya bayyana cewa a yayin aikin, an kama mutane uku da ake zargi, tare da kashe ‘yan ta’adda hudu.
Adewusi ya ce bayan kammala farmakin, ‘yan ta’adda sun kai wa dakarun hari a Gidan Wagni yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Kekun Waje, domin amsa kiran gaggawa.
“Duk da cewa harin kwanton bauna ya zo musu ba zato ba tsammani, dakarun sun nuna jarumtaka, suka fafata da ‘yan ta’addan tare da hana su cutar da al’ummomin da ke kusa."
“Abin takaici, sojoji biyar da jami’in ‘yan sanda daya sun sadaukar da rayukansu a yayin wannan fafatawa.”
- David Adewusi
An kai wa sojoji dauki
Ya kara da cewa, bayan samun rahoton kiran gaggawa, rukunin farmaki na gaggawa na OPFY, tare da hadin gwiwar dakarun 1 Brigade Quick Reaction Force daga sansanonin da ke Kanoma da Kekun Waje, sun gaggauta isa wurin.
“Kwamandan 1 Brigade ne da kansa ya jagoranci dakarun kai taimako, wanda hakan ke nuna matakin hadin kai, tsari da jajircewa da ke cikin wannan aiki."
- David Adewusi

Source: Original
Sojoji sun raunata jagororin 'yan bindiga
Sanarwar ta kara da cewa, hadakar dakarun sun kai mummunan martani ga ‘yan ta’addan, lamarin da ya tilasta musu tserewa.
Bayanai na sirri sun nuna cewa shahararrun jagororin ‘yan bindiga Janwuya da Alhaji Bello, wanda shi ne mataimakin Kachalla Soja, sun samu munanan raunukan harbin bindiga a yayin artabun, yayin da wasu daga cikin ‘yan bindigan da suka tsere suma suka jikkata.
Sojoji sun hallaka 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya sun yi ruwan wuta kan 'yan bindiga a jihar Katsina.
Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga da dama bayan da suka jefa musu bama-baman da suka sanya suka kone kurmus.
Sojojin sun kashe su ne a yankin karamar hukumar Matazu yayin da suke dawowa daga munanan hare-hare da suka kai wa al’umma a wasu yankunan karamar hukumar Tsanyawa ta jihar Kano.
Asali: Legit.ng
