Ramadan: Izala Ta Fitar da Jerin Malaman da za Su Yi Tafsir a Jihohi, Kasashe a 2026
- Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Ƙasa ta fitar da sunayen malaman da ta tura tafsirin Ramadan na 1447/2026
- An tura malamai jihohi da dama a Najeriya da kuma wasu kasashen makwabta a Afirka ta Yamma da wasu kaashen Afrika ta Tsakiya
- Kungiyar Izala ta ce an tsara dukkan matakan ne domin isar da ilimin Al-Kur’ani mai girma ga al’ummar Musulmi a watan Ramadan
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato - Kungiyar Izala karkashin jagorancin Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ta tura malamai tafsirin Al-Kur’ani jihohi da kasashe a Ramadan 1447/2026.
Sanarwar ta fito ne daga hedkwatar kungiyar, inda ta bayyana cewa shirin yana daga cikin manyan ayyukan da JIBWIS ke gudanarwa a duk shekara domin ilmantarwa, tarbiyya da kuma yada Musulunci.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da tura malamai tafsiri ne a wani sako da Hamza Muhammad Sani ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Izala ta tura malamai tafsirin Ramadan
A cewar sanarwar, shugabancin JIBWIS ya kammala dukkan tsare-tsare tun kafin shigowar watan Ramadan, domin bai wa malamai damar isa wuraren da aka tura su tafsir cikin lokaci.
Kungiyar ta bayyana cewa an rarraba malamai zuwa jihohi da dama ciki har da Plateau, Kaduna, Bauchi, Gombe, Kano, Borno, Kebbi, Sokoto da sauransu.
Haka kuma, sanarwar ta nuna cewa shirin bai tsaya a cikin Najeriya kadai ba, domin an tura wasu malamai zuwa kasashen Nijar, Burkina Faso, Ghana, Chadi, Togo, Kamaru, Mali, Benin, Cote d’Ivoire da kuma Amurka.
Jerin malaman da aka tura tafsir
1. Ash-Sheikh Muh’d Sani yahaya JINGIR da Hafiz Aminu Yusuf Nuhu, 'Yan Taya, Plateau
2. Sheikh Yusuf Muh’d Sambo da Hafiz Abdullahi Baffa Itas, Kaduna

Kara karanta wannan
Abba, Barau da hukumomi 2 da suka yi alkawarin nema wa Fatima da yaranta 6 adalci
3. Sheikh Dalhatu Abubakar Kantana da Hafiz Abdurrahman Ahmad, Gombe
4. Sheikh Nasir Abdulmuhy da Hafiza Abdulmuni Aliyu, Nasarwa
5. Bar. Aliyu Alhassa Sangei, Unguwar Rimi, Plateau
6. Dr Hassan Abubakar Dikko, Toro, Bauchi
7. Prof. Abdurrahman Lawal Adam, Jos ta Arewa, Plateau
8. Sheikh Madu Mustafa da Dr. Abubakar Musa Bako, Maiduguri, Borno
9. Sheikh Abdurrahman Isa Jega da Hafiz Muhammad Naziru Jega, Birnin Kebbi
10. Sheikh Hamza Adam Abdulhamid, Jost ta Arewa, Plateau
11. Sheikh Salihu Sulaiman Ningi da Hafiz Yusuf Shu’aibu, Ningi, Bauchi
12. Ustaz Muhammad Umar Zango Kambama da Hafiz Isma'ila Gwadangwaji, Koko, Kebbi
13. Sheikh Abubakar Usman Mabera, Sokoto
14. Mal. Abubakar Qamarawi, Ibadan, Oyo
15. M. Murtala Abubakar Imam, Keffi-Nasarawa
16. Shittiman Borno Mal. Bashir Umar Kashere, Gashua, Yobe
17. Mal. Auwal Sa'eed Jikan Mai Waina, Bus Stop, Kaduna, Kaduna
18. Ustaz Umar Hassan Gusau, Gusau, Zamfara
19. M. Haruna Ibrahim Gashua, Kumo, Gombe
20. Hafiz Aliyu Abdulwahab, Misau, Bauchi
21. Sheikh Khadi Abdulmumin, Jalingo, Taraba
22. M. Ibrahim Yunusa Ugo, Uguaba, Enugu
23. Ustaz Musa Abdullahi, Potiskum, Yobe
24. Sheikh Adamu Girbo, Malam Sidi, Gombe
25. Dr. Aliyu Isa Makurdi, Makurdi, Benue
26. Hon. Ustaz Muh'd Muhammad Abubakar, Magama Gumai, Toro, Bauchi
27. Dr. Mas'udu Ibrahim Tulu, Maitama, FCT Abuja
28. Mal. Muh’d Kabiru Asshikawi, Kontagora, Niger
29. Mal. Mustapha Salihu Bamalli, Guzape, FCT
30. Ustaz Yusuf Kaura Maishafi da Hafiz Nawwasi Potiskum, Zuru, Kebbi
31. M. Dawd Salahuddeen da Imam Hassan Lokoja, Kogi
32. Dr. Mal. Aliyu Rashid Makarfi, Tal’udu, Kano
33. Ustaz Ibrahim Muh'd Duguri, Jalingo, Taraba
34. M. Muhammad Sani Usman Kakiyayi, Zaria-Kaduna
35. Ustaz Iliyasu Ibrahim Maigatari, Maigatari, Jigawa
36. M. Isa Ruwan Bago, Jimeta, Adamawa
37. Hafiz Abubakar Abu Sumayya, Jama’are, Bauchi
38. M. Abbas Ahmad Aliyu-Jingre, Bassa, Plateau
39. Dr. Habibu Danbatta, Dutse, Jigawa
40. Dr. Sani Ibrahim Jalingo, Jalingo, Taraba
41. M. Musa Salihu Alburhan da Hafiz Sa'adu Dalam Tilde, Tulu, Toro, Bauchi
42. Prof. Nuhu Tahir Tajuddeen, Zaria, Kaduna
43. Dr. Aliyu Ibrahim Shafi'i, Minna, Niger
44. M. Abubakar Umar Rabo, Ganye, Adamawa
45. Mal. Muhammad Sani Bichi, Bichi, Kano
46. Dr. Bashiru Mashema da Ustaz Zaidu Sa’adu, Lagos
47. M. Abdullahi Muhammad Idris, Akure, Ondo
48. M. Muhammad Dabo Dengi, Mavo-Wase, Plateau
49. M. Muhammad Bashir Abuga, Calabar
50. Hon. Ahmad Muhammad Ashir, Bukur, Jos
51. Prof. Chika Makarantar Mai Gona, Sokoto
52. Mal. Bawa Ibrahim Kafanchan, Jama’a, Kaduna
53. Mal. Ibrahim Natalatu, Bojude, Gombe
54. M. Yusuf Mustapha Takwashe da M. Abu Sa’ad, Asaba, Delta
55. Ardo Mahmud Adam-Mahanga, Riyom, Plateau
56. Mal. Yahaya Muhammad, Lafia, Nasarawa
57. Mal. Yakubu Hussaini, New Bussa, Niger
58. Mal. Idris Ardo Lere, G/Kurama, Lere, Kaduna
59. Dr. Idris Sulaiman Minna, Nasarawa
60. M. Ahmad Salihu Bukar-Y/Shendam, Plateau
61. Mal. Yusuf Sa'eedu Kirki, Dengi-Kanam, Plateau
62. Mal. Shu'aibu Almadani, Kwaya-kusar, Borno
63. Mal. Aliyu Wase, Gombi, Adamawa
64. Mal. Muhammad Idris, Kashere, Gombe

Kara karanta wannan
Zafin siyasa bai hana aiki: Abba ya fadi shirin gwamnati a kan matasa 50, 000 a Kano
65. M. Zubairu Muhammad Fari Gire, Mubi, Adamawa
66. Mal. Sunusi Dahir Mukhtar, Zaki Biam, Benue
67. Mal. Ishaq Muh’d Jangwa, Katsina
68. Mal. Muhammad Sani Gombe, Darazo, Bauchi
69. Mal. Abubakar Yusuf Yawuri, Yawuri, Kebbi
70. M. Adam Muhammad Gadar Sogai da Hafiz Zubairu Adam Ibrahim Maishafi, Bauchi
71. M. Muhammad Salihu Imam, Bayelsa
72. M. Mukhtar Aliyu Yabo, Nakasari, Sokoto
73. M. Shitu Saharanu, Tambuwal, Sokoto
74. SP. Ahmad Adam Kutubi, Wuse Zone (3)-FCT-
75. Dr. Jibrin Abdullahi, Akwanga, Nasarawa
76. M. Nasir Hussaini Bayero, Dawaki AMAC, FCT
77. Imam Jafar Hussain, Tsando, Gombe
78. Ustaz Abubakar Salihu Zaria, Damaturu, Yobe
79. Ustaz Babangida Muhammad, Azare, Bauchi
80. Mal. Haruna Y/Shendam, Mangu, Plateau
81. Mal. Aliyu Muhammad Bara, Deba, Gombe
82. Mal. Idris Sarkin Hausawa, Zungeru, Niger
83. Ustaz Abdussalami Abubakar Jega da Hafiz Mustapha Dahir Isa, Niamey, Niger
84. M. Muh'd Rabi'u Adam, Hiro, Niger
85. M. Sulaiman Mamman, Yamai, Niger
86. Sheikh Dr. Kindo Muhammad, Burkina Faso
87. Sheikh Abubakar Wadrago, Burkina Faso
88. M. Abdullahi Atibobo, Ghana
89. M. Juma'a Adam, Chad
90. Sheikh Dr. Yahaya, Chad
91. M. Abdullahi Abdullahi, Chad
92. M. Hussaini Muh'd Sankensi, Togo
93. Sheikh Abdullahi Imam, Togo
94. Sheikh Zakariyya Imam, Togo
95. Mal. Bako Abubakar, Cameroon
96. Imam Muhammad Auwal, Cameroon
97. M. Muhammad Taraware, Mali
98. M. Abubakar Kamaru, Mali
99. M. Umar Jaho, Mali
100. M. Ahmad Muhammad, C/Africa
101. Sheikh Abdussalami, Code'I'voire
102. Sheikh Dr. Dawud Kandi, Benin
103. Sheikh Mustafa, Benin.
104. Sheikh Ibrahim, Benin
105. Sheikh Ahmed Imam, New York, America

Source: Facebook
Sheikh Habibu Yahaya Kaura ya rasu
A wani labarin, mun kawo muku cewa an sanar da rasuwar babban malamin Izala, Sheikh Habibu Yahaya Kaura a birnin tarayya Abuja.
Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ne ya sanar da rasuwar malamin, inda ya ce sun rasa uba tare da fatan Allah ya gafarta wa marigayin.
Malamai da dama da suka hada da Sheikh Mansur Sokoto da Dr Jabir Sani Mai Hula sun yi maganganu game da rasuwar malamin.
Asali: Legit.ng



